← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 88

Sashe 50

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Take ta danna kiran waya, tayi ringim mai tsaho, aka d'aga. "Hello, akace daga can.
Taji muryar cikin ko ina na jikinta yaushe rabonta da jin muryar shi, har kwalla ta tarar mata a idonta, Basma tayi mata laifin da baya yafuwa.!
"Hello."
Itama tace da rawar murya.
"Wanene.""?
Aka tambaya, ita kuma ta rasa abin cewa sam, tayi d'if kwakwalwarta ta kunne, baya kawai take tunowa.
"Nace wanene."?
Aka k'ara tambaya daga can.
Cikin raunin murya tace, "Nice Hafsah ce fah."
"Hmm.." akace daga can, sannan ba,a b'ata lokaci ba aka katse kiran.
Mamaki da tsoro suka saka Hafsah daskarewa ta kasa motsi.
Yau..? Ita.."? Kuma yusuf..? Haka ta faru."?
Fatanta kawai komai ma ya juye ya zama mafarki.
Fateema taji tausayinta matuk'a kuma fuskar ta ta nuna hakan, musamman lokacin da Hafsah take mishi bayanin _"Nice fah Hafsah ce.!_
Akan idonta taga Hafsah ta k'ara danna kiran, amma ba,a d'aga ba.
Fateema tasan ko ta rarrashi Hafsah rarrashinta bazaiyi tasiri ba, zata b'ata bakinta ne kawai, kuma gwara ma ta kyaleta ta zubar da hawayen ko dan ta rage rad'adin zuciya.
Bata son sauraron kukan, don haka ta mik'e tabar d`akin sai kuma taga kawai gwara taje ta fad'awa maman.
Maman a parlour take zaune da wani littafi a hannunta, Fateema tayi sallama, ta d'an rakab'e a gefe, tana kallon maman. Mama ta dago ta kalleta don taga alamun bata zauna ba. "Menene kike rab'e -rab'e"? Tana Sosa kai tace,
"Um, da dama Hafsah ce tayi kiran a waya.
"Matso nan ki fad`amin me ya faru."?
Ta ajye littafin a gefe ta bada dukkan hankalinta akan Fateema.
_"Kinga data kira, shine yace mata wa ye.. Tana cewa ita ce, yace hmm.. Sai ya kashe."_
Mama ta jinjina kai.. "Okay okay, shikenan, ba suyi wata magana ba"?
"Eh." inji Fateema.
"Ok jeki nagode."
Har ta dan fara tafiya sai kuma ta juyo cikin k'asa da murya tace, "Um mama don Allah kada kice na fad`amiki."
"Hmm." Mama taji d'an murmushi, tayi mata alama da hannu irin, _jeki kawai."_
Tun daga ranar damuwar Hafsah ta k'ara nunkunwa, har Fateema ta saba da ganinta tana kuka haka siddan. Abin ya fara damunta har take k'ara fad`awa Mama, "Mama Allah kusan kullum sai tayi kuka fa take bacci."
Jinjina kai kawai maman tayi tace mata, "Toh naji."
Aranar ne kuma mama tayi niyyar d'aukar wani mataki akai.
Da dare ta kira Hafsah d'akinta, "Baki yanke shawarar ba koh."?
Hafsah taji jim, tana tunani, _wannan fa wata dama ce, gwara ta bawa mama dama ta fad'i abinda ke ranta ko zai zama mafitar ta, don ita kanta ta sani ta damu da yawa, kuma ta gaji da zama cikin k'uncin zuciya.
"Na takura miki koh.."? To tashi ki tafi."
Tayi daurin girgiza kai. A hankali tace, _"Aa wallahi mama, na kirashi ma bai yakashe."_
Sam Hafsah ta manta ma da mama take magana, abinda ke ranta kawai take son ta fitar.
"Hmm, kingani koh."? "Abinda nake fada miki kenan Hafsah kada ki damu kanki akan mutumin da bai damu dake ba, amma bakya ji."
Abinda mama ta hau fad`a kenan, wad`anda Hafsah taji mamakinsu, azaton ta fada mama zata rufeta dashi, akan kub'utar bakin da tayi.
Mama ta kamo ta, "Tashi ki dawo kusa dani kinji."?
Hafsah ta mik'e mama ta rik'e ta harda jingina ta da jikinta, cikin murya mai nuna alhini, take magana.

_"Hafsah ba laifi bane don kinso yaron nan, tunda so baya zama laifin mutum, abu ne da yake faruwa haka kawai. Sau dayawa mutane suna tsintar kansu akan soyayyar wanda bai dace su so ba, amma babu yadda zasuyi._
"Kinga abubuwan da na fad'a miki sun tabbata koh."?
Hafsah ta jinjina kai. Don tabbas hakan ne.
"Zaki hakura dashi."?
Hafsah taji saurin d'aga kai, don ita kanta ta gaji, gwara maman ta fada mata ta gwada d`in idan zai curu.
Mama tayi murmushi, a zuciyarta tana hamdala.
_"Kiyi hak'uri Hafsah, ki d'auka hakan kaddara neh._
Kinji.
Ta d'aga kai kawai.
"Abubuwan da zaki guda biyu ne, na farko aiki ne da gangar jiki na biyun kuma aiki ne da zuciyarki.

Nafarkon shine:
Addu,a.
_"Addu,a ita ce ta farko kuma ita ce maganin komai. Ki dinga tashi da dare kina fad'awa Allah damuwarki, ki rokeshi ya yaye miki dukkan damuwa._

_Sannan na biyu shine, ki ragewa zuciyar ki yawan tunani, kinajin tunanin shi yazo miki kiyi kokari ki kauda shi da wani abin."_

_"Sannan ki daina bari zuciyarki na k'awata miki shi, ki mishi kallo da idon da kowa yake kallonshi, kada ki sawa ranki yafi kowa, zaki ji kin rage wani kaso daga sonshi."_

_"Kada ki d'auka idan kin rabu dashi bazaki taba samun wanda ya fishi ba, ki tuna mutane, daban daban ne, kuma kowa nada tashi baiwar, zaki iya haduwa da wanda ba kiyi tsammani ba a lokacin kuma zaki gane, ashe wancan ba komai bane kawai son zuciyarki ke kawata miki shi."_

_"Kisa aranki zaki iya rabuwa dashi kuma, ba zaki iya sab'awa Allah saboda shi ba."_

_"Ki bawa, kanki da rayuwarki, maimahimmanci fiye da shi, yadda zaki yardarwa kanki akwai masu buqatar ki aduniya banda shi, akwai masu son farin cikinki, ko shi baya so, akwai wad`anda suka damu dake kuma sun fishi yawa, saboda haka ba zaki wulak'anta rayuwarki akan mutum guda d'aya ba."_

_"Ki kalli alkhairan da ke tattare da sauran mutane, masu nuna suna sonki, kada Ki rufe ido akan mutum d'aya."_

_"Ki d'auka cewa, da zaki bawa wani dama, zai miki son da shi baya miki rabinsa, Hafsah meye amfanin damuwa da wanda ya nuna baya buk'atar ka."?_

_"Ki d'auki lokacinki da muhimmanci kada_
_ki k'arar dashi akan abinda bazai miki amfani ba, ko neman abinda bazai samu ba, kada Ki wayi gari lokacin kuruciyar ki ya shud'e amma baki amfani kanki, da sauran mutane da komai ba."_..

Mama tayi murmushi, _"Idan kika saka haka aranki, ina mai tabbatar miki, by time, zaki nemeshi a ziciyarki ki rasa, a hankali Soyayyar shi zata dusashe.!"_
Bance miki lokaci d'aya ba, don komai yana buk'atar lokaci, amma ki tsananta addu,a... Sannan kisa a ranki cewa zaki iya kinji.
Hafsah ta daga kai zantukan sun shige ta, sosai, indai har zasuyi mata amfani yadda mama ke nuna mata tabbas zata gwad'a.
A lokacin taji zuciyar ta ta cunkushe, da tunani daban-daban ta rasa na d'auka kawai sai ta mik'e a wajen ta kwanta sai kuma bacci.
Chapter 50 · 0% Book details