← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 88

Sashe 77

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abban Basma ya kara gyara zama..
Dole na roki afuwarka Alhaji. Domin wannan cin mutunci ne, ya za,ayi azo har gida saboda rashin hankali haba ai abin babu mutunci. Don Allah kayi hakuri wallahi bani da masaniyar hakan. Kuma ita matar ba ma tare da ita shiyasa take kokarin hana auren. Amma kayi hakuri don Allah a bawa mutanan gidan hakuri suma don Allah."!!

Cike da kunya alhaji mukhtar yake magana domin bai so yasa abban Basma cikin wannan halin ba.
Babu shiri ya mike da shirin tafiya. Kayi hakuri kaima don Allah sannan kabi komai a sannu. Wallahi babu komai a wajena wannan abin ba komai bane illa neman samun maslaha, kuma mu cigaba da addua Allah yasa alkhairi dama harkar aure dole ana samun kalubale. Amma wannan abin ba komai bane balle kuma kasan sha,anin mata sai su. Ayi hakuri dai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Ya mik'a mishi hannu jikin abban Basma a sanyaye sukayi musabiha.

Ya mike da kyar ya raka Alhaji Mukhtar cike da kunyar shi. Don abin da Halima tayi yaja mishi kunyar manyan mutane irin su Alhaji mukhtar. Kuma yasan ta gama zubar mishi da k'ima.

Tafiyar abban Nour kenan Alhaji Yunus ya shigo gida.
Yanayin sa ya tada hankalin Hajiya Salma ta bishi dakin shi da sauri..

Ta tarar ya yaye babbar rigar shi, ya cillar a tsakar dakin yana shirin juyawa zai fita. Alhaji lafiya ta tambaye shi.
Sai da ya juya zai fice sannan yayi mata magana a fusace yana huci.

Billahil-aziim sai Halima ta gane wanene ni.!! Ya cigaba da tafiya bai kara magana ba.
Hajiya Salma ta bishi da sauri kiranshi ta tsorata da yanayin nashi amma ina tuni ya fice. Ta biyo shi har Harabar gidan tana kira amma ya fice ko mota bai dauka ba.

Ta dawo gida cike da rudu tana tambaye tambayen da babu amsarsu. Fatima meya faru da Abban ku. Ina tunanin gidan halima zaije fa. Ina tsohon abinda zai faru ko me tayi masa oho."
"Kinga dakko hijabin ki muje wallahi ban aminta da fitar Alhaji zuwa gidan ta ba. Fatima ta taso babu shiri. Itama hankalinta duk ya tashi.

________________
Mamaki da razani ne suka tarar tararwa Hajiya Halima ganin Alhaji Yunus a gidan ta kuma babu neman izini daga sallama ya shigo cikin falon.
Ta mike tsaye a dan tsorace, ya nunata da yatsa. Sannan ya rigata fara maganar da take shirin yi cikin fushi.
"Halima kinyi abinda kikayi kinji dadi kuma yayi kyau bazan ce kinfi karfi naba, don idan nayi niyyar daukar matakin zakiyi mamaki amma zan nuna iko a inda nafi ikon sosai, don wallahi baki isa kin iko akan yata ba kuma aure babu fashi.!!
Kan tayi wani yunkuri ya wuce ta ya nufi bedroom dinta.
Aikuwa sukaci karo da Basman daya shigo nema don tajiyo muryarshi tana shirin fitowa taga me zaiwa mahaifiyar tata.

Ai kuwa ya kife ta da mari kafin ya jata fii ya zubar da ita a kasa.
Cikin tsananin fushi yake maganar.

Kinje kinyi abinda kukayi ke da uwarki yayi muku kyau wallahi idan hakan ya zama silar fasuwar auren ki Basma hakkina sai ya biki don nayi iya kokari na kuma bazan sake saka hannu akan al'amarinki ba. Don na sauke hakki na a kanki.

Meye haka me kake ji dashi ne zaka shigo min gida kana min hayaniya kuma don wulak'anci har uwar daka me kake nufi.

Ya juyo a fusace komai ma ina nufi.. Don baki isa kin hanani iko akan yata ba.
"To wallahi ka fita kafin na tara maka jama'a."
Ya daga muryarshi ya fuskanto ta shima.
Ki tara mini jama,ar Halima sai me aini kin gama zubda min da k'ima kuma sai Allah ya saka min abinda kikemin ina yiwa yata tarbiyya kina rusawa."

Hankalin Basma ya tashi har taji ta dan fara nadamar abinda tayi. Don bata san abin zai zama haka ba. Yau abban ta har cikin uwar daka saboda ita."? Shida da wuya ma ya shigo cikin gidan tun da can ma idan yazo ganinta."?

"Hmm, kada ka manta ba kai kayi min nakudar ta ba ehe kuma wallahi ka kara tabata sai sharia ta rabamu don baka isa ba ka nuna mini iko."

Bai tsaya komai ba saboda xuciya.. ya rufe Basma da duka tana ihu. Yana fad'in idan na karya ta sai naga naki matakin..wallahi Halima nayi nadamar haihuwa tare dake da kika haifa min abinda zai bujure min.

Basma cike da nadama take bashi hakuri tana kuma yayin da hajiya Halima ta kasa kwa kwatarta duk kurinta.. Don abban mahuci yasaka da ya gani a gefe sai da ya kakkarye sannan ya kyele ta. Lokacin Hajiya Halima ta fita waje neman dauki inda ta hadu da hajiya Salma suka ranks rankaya babu tsayawa ce-ce-ku-ce.

Huci yake yana ta sababi. _"Saboda baki dauke ni mahaifi ba kinfi son ki ta garari kina wayo a gari kina son ki lalace ko." Kina biye mata tana doraki kan hanyar banza. Wai har ke kinsan ki je gidan mutane kuyi musu cin mutunci don kawai dansu na sonki.? Cewa nayi miki Alhaji mukhtar sa,a nane ko itah matar tashi sa'ar uwarki ce."? Idan daraja da mutunci ne kin isa ku nuna musu."? Saboda ki nuna baki da tarbiyya yar mace ce ke koh"?_

_To Allah ya gani bada yawuna kuka je ba kuma mutunci na da kuka zubar na barku da Allah kuma illa kanki kikayi wa..._

Hajiya Salma ta dakatar dashi. Don Allah Alhaji kayi hakuri kada ka aibatata. Kayi hakuri kazo mu tafi tun farko bai dace kazo bama. Basma yarka ce ka dinga mata adduar shiriya ba fada ko aibatata ba.

Ya goge gumi ya juyo ya kallesu. Mataki daya zan dauka ko ta bini ko kuma idan bata bini gida yau ba to na rantse bazata kara taka min cikin gidana ba.

Aikuwa bazata bika ba. In yaso ka cireta cikin yayan naka sai me."?
Cewar Hajiya Halima kenan cikin fushi.

Zai tanka mata, matar shi ta tsaida shi. Sannan ta bige da rokon sa kan ya fito sun zo da mota. Don ita damuwar ta shine ya fito daga cikin gidan.

"Don Allah Alhaji kayi hakuri kajira mu a waje yanzu zamu fito da ita din."
Dakyar ya juya zai tafi yana hararar Hajiya Halima.

Itama hararar ta jefa masa kafin tace, "kasani baka daki banza ba don wallahi sai na dauki matakin sharia kan ci muni mutunci da kayi har gida.!!
Cikin kaushin murya shima ya maida mata martani.

Ki kaini kotun koli!! Kuma indai baki barta ta biyo ni ba kada ta kara kirana ubanta."
Fatima ce ta hau mishi magiya.
Don Allah Abba ka fito kayi hakuri.

Ya juya ya fita a dakin.
Ya bar Halima tana ihun sababi.

Hajiya Salma ta sunkuya tana wa Basma nasiha duk da har yanzu bata san abinda tayi ba.

Hajiya Halima ta janye ta tana magana cikin gadara. "Malama zoki bar gidan nan munafuka asirin da kikayi yayi saura ki jira nawa martanin.."
Hajiya Salma tayi murmurshi, "Hmm Halima kenan ke kika san asiri da kike ambatarsa amma kiyi wa kanki fada yarki macece.!!

Bata jira cewar ta ba itama ta juya saboda bata son tashin hankali. Tana cewa Basma, Kibi mahaifinki dai Basma don da uba ake ado sannan aure shine darajar mace.!!

Tanajiyo Halima tana zaginta amma sai tayi murmurshi kawai don bata da lokacin ta.

"Bayan fitar su Halima ta koma gun yarta tana rarrashi tare da kara hure mata kunne tana kara nuna mata ubanta ya tsane ta ne kawai don an rabasu da ita."

Basma taji nadamar abinda tayi amma tana tsoron bin mahaifinta. Don ta daku a wajen shi.

Amma dukan da yayi mata yayi tasiri matuka wajen shigar da ita hayyaci har ta fahimci tayi kuskure sannan kalaman shi sun tsorata ta.

Su hajiya Salma kuwa, sunje gida cike da hikima take shawo kan mijinta har ya dan sakko sannan ta nuna mishi illar zuwa gidan Halima sannan ta taushe shi kan ya dinga yiwa 'yartashi addua.

Sai daga baya ya sakko har ya sanar da ita a binda Halima ta aikata.
Hajiya Salma ta dade da mamakin abin daga karshe ta nuna mishi kada ya damu.

___________________________

Hajiya Rukayya ta zaunar da Nour sosai take tausar shi..ta karanta mishi abubuwan da take guje mishi akan auren macen da bata yi dashi da kuma illar auren mace mara tarbiyya da kuma yar mace. Ta bashi misalai da dalilai kala-kala sannan ta shiga nusar she shi abinda take gudu.

_Nour ni mahaifiyar ka ce, ko kana son ka auri mace n da zata rabani da kai.."? Ya kalleta ta jinjina kai. Tabbas bakasan son mace yana rufe idanu ba har a dinga hango laifin uwa imma ta hanyar kissa ko kuma ta asiri."? Mata da yawa sun rabamu maza da iyayen su. Ko kana son a dinga wulak'anta min kai ko yaushe ka zama baka da kwanciyar hankali."? Wallahi na tabbatar idan ka auri yarinyar nan sai kaji dama baka aure ta ba tunda har abin ya fara da haka._ "Ka tuna fa yadda babu kunyar ido na ko naka amma ta bude baki tace bata sonka haba nour ai so ba hauka bane.. nidai ina rokonka kuma ina baka hakuri don Allah ka cireta a zuciyarka badon bana sonta ba ko don na hana sunna, sai dai don a zauna lafiya kuma in sha Allah, zaka sami wacce ta fita kaji. Allah yayi maka albarka ya baka mace ta gari.

Amin mama inji Nour.

Don bata barshi ba sai da ya yaji ya cire kaso mafi yawa na son Basma daga zuciyar sa. Don yana matuk'ar son mahaifiyar shi idan ya tuno d'awainiyar da ta sha dashi yana k'arami. Don yasha jinya typhoid data sarke shi yana d'an shekara sha uku. Sai da yayi shekara daya yana fama. Babu wanda ya zaci zaiyi rai ma.
Ya saki jiki sosai kuma ya tabbatar wa da mahaifiyar tashi cewa ya bar abin.

Don haka lokacin Abban ya tuntubeshi da zancen yana fada mishi sunyi magana da mahaifin yarinyar yayi hakuri ya cigaba da shirye-shirye kada wannan abin ya dame shi.

Nour ya gyara zama yana zayyanowa mahaifin shi jawabi.
Chapter 77 · 0% Book details