Sashe 65
Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahankali take tafiya, ta k'ara saka yanga akan alhinin yangar da take tata ce ta halitta, saboda bata son k'arasawa inda zata je.
Tana hangoshi tana k'ara rage sauri. Ga k'aruwar fargaba kuma.
Yana kallon fulawowin har yanzu, gaba d'aya ya bada hankalinshi can, don ya fitar da ran fitowarta kusa.
Hakan da yayi ya mata dad'i bata son ya jiyo sautin takunta, bare ya juyo.
Sai da ta kusa zuwa inda yake sannan ya juyo.
Tunda ya gano me tahowar ya kafa mata idanu, har ta k'araso inda zata zauna, ita kuwa da kyar take iya cira k'afarta. Tayi k'asa da idonta ga barin kallon shi, dama bata yarda sun had'a ido ba. A hankali ta d'an bude baki ta mishi sallama, sannan ta d'an ja kujera a hankali ta zauna.
Sai da ta daidaita a kujerar sannan ya bud'a baki shima ya amsa mata, yana k'ara kai idanunshi fuskarta, "Wa alaikumus-salam."
Sukayi shuru tun bayan sallamar daya amsa.
Sai kuma taga ya dace ta mishi sannu da zuwa, tunda bak'onta ne.
Cikin rashin daga sauti kamar koyaushe tace, "Sannu da zuwa ya hanya."?
Sai yanzu ya ji dad'i sosai har ranshi, don da har ya fara wani tunani. Ya fad'ad'a murmushi sosai.
"Yawwa, sannu kema, hope na sameki lafiya.
Ta fad'a a hankalin dai.
"Lafiya lau Alhamdulillah."
Suka k'ara yin shuru, shi cikin nazarin irin had'uwar ta, datsaruwarta komai nata yayi mishi yadda yake so, yafi ganin kyanta ma yau fiye da koyaushe da ya tab'a ganinta. Ita kuma cikin k'aguwa da kallon da yake mata, da tunanin irin haduwar shi shima da kwarjinin da yake da shi, don jinta take kamar gaban wani sarki take, gaba d'aya ta takura.
"Hafsah, yau gani koh, Allah yayi yau kinga ukhashatu.!!
Ya fad'a da murmushi. Itama ta dan murmusa, bata da abin yi ko cewa idan ba murmushin ba.
Yayi yar ajiyar zuciya a hankali.
Alhamdulillah.!!
Taji yace, sannan bayan wani d'an shuru ya furta.
"Ki yarda Allah ne ya had'ani dake, kuma shiya san alkhairan da zai kulla tare damu, shiyasa na nace miki duk da ke naga kamar takura ne agunki koh."
Ya k'arashe maganar yana k'ara zuba mata idanunshi, ta taga sunyi mata wani _harr_ a nata idanun, kamar wani giftawar haske.
Tayi saurin kawar da idonta gefe tana murmushin zancen shi.
"Da gaske ne kenan ni me naci ne a wajen ki koh."?
Ya fada shigen rad'a.
Dole ta bude baki don kare kanta.
"Ni bani na fada ba dai.!!
Ta fada tana yar dariya.
Shima dariyar yayi, hmm ai ni nasani, inada naci akan abinda nake so gwara na fada da bakina.
Gabanta ya fadi da kalmar daya fad'a, _inada naci akan abinda nake so.!_
Sonta yake kenan."?
Ta tambayi kanta, tare da d`agowa ta kalli idanunshi don tabbatar da abinda yace.
Ya jinjina mata kai shikuma, "yes.!!
Ya fad'a.
_Ta kasa tantance me "yes d`in tashi ke tabbatar wa. Kasancewar shi mai Nacin ko kuma kalmar kan abinda yake son, dayace.? wanda maganar kai tsaye tasan akanta ake yi._?
Suka tsaya shuru shida ita, kowa cikin nazari.
Takun tafiya sukaji daya sa su dukansu juyawa.
Zainab ce rik'e da tray na ruwa da lemo sai _cups._
Ta musu sallama sannan ta ajye.
Bata bata lokaci ba ta juya, wanda hakan bai bawa ukhashatu damar yi mata godiyar da yayi niyya ba. Sai kawai ya juya ga Hafsah. "Thank you.!!
Yace mata.
Ta mishi alama da ido. Tana neman karin bayani akan godiyar.
Yayi mata nuni da tray d`in yana murmushi, sannan yace, "ko ba ni aka kawo wa ba."
Murmushi tayi ita, tace, "hum.."
Kawai.
"Zan iya sha don inajin k'ishirwa.?
Ya tambaya.
Ta d'aga gira kawai.
Ta mishi kyau sosai hakan yasashi b'ata lokaci ya kalleta, sannan ya d`auki ruwan ya zuba a kofi, ya d'aga zai sha.
Ta zuba mishi ido ita kuma, sai taga ya fasa.
Batayi magana ko wani motsi ba taga ya d`auki bottle d`in zai kuma zuba wani ruwan.
"Oh sorry ban tambayeki ba ruwa zaki sha ko lemo. Ni dai nafi ga ruwan."
Batace komai ba, sai mamaki daya bata, _wannan mutum akwai salo!!_
Tace a ranta.
Uhum."?
Ya kuma tambayar ta.
Ta bishi da kallo kawai, sai kawai ya zuba mata ruwan, a cup ya ajye agabanta.
"Gashi."
Yace mata sannan ya tsare ta da ido.
Ala dole tace, thanks.
Tana ganin yanayin murmushin da yayi mai bayyana tsantsar farin ciki.
Sannan a hankali ya daga nashi ruwan ya fara sha.
Bata da bukatar shan ruwa a lokacin, kuma ko da, da buk'atar hakan ba,zata sha agabanshi ba.
Sai da ya shanye, ya k'ara zuba wani ya sha, rabi sannan ya ajye, "Thank you."
Yace mata, wanda kafin ya fad'i hakan sai da ta lura da motsawar bikinshi ya furta, _"Alhamdulillah!._
Sukayi shuru, bai k'ara ce mata tasha ruwan ko wani abu ba. Sai kallon agogon hannunshi da yayi.
Itace ta tuna da wata tambaya da tace zata mishi, don tana san tabbatar wa.
Tana fara magana, ya zubo mata idanu, wanda hakan yasa ta dan rikice sai da kyar takai k'arashen jimlar.
Um.. Kace ka taba ganina a wurare, so ina da inane."?
Ya saki murmushi, sai lokacin ta lura da dimple d`in da yake dashi ya jinjina mata kai.
"Of course naganki sau biyu kafin na ganki a television."
Tana so ta k'ara tambayar shi, "To ina ne."?
Amma bata son ta k'ara tambaya.
"Na ganki a gidan biki, sannan na ganki a titi.!!abinda yace kenan yana wata iriyar siririyar dariya.
Sai ta tafi tunani, Gidan biki kuma.. Titi kuma."?
Da kyar ta samu ta tuno irin gidan bikin da yake nufi, da taimakon k'ara kallonshi da tayi take ta gano shi.
_Mutumin da taji abokan shi sun kirashi da UK ranar bikin Aysha er ajinsu sannan tabbas sunyi magana da Basheer randa suka had'u a titi._
Wato dole yace gidan biki da kuma titi.
Da sauri ta bude baki tace, waye ya baka number ta toh."
A hankali kuma cikin nutsuwa yayi saurin bata amsa, "Allah.. Allah ne ya bani.!!
"Hmm, koh."?
Ya jinjina mata kai.
Sannan don kada ya bata damar sake mishi magana ya fara wata magana takaitacciya, amma wacce ta rikita komai nata.
"Tun ranar naji kinyi min, naji inason kulla alak'a dake, sai dana rasa hanyar samun contact dinki na gano sonki nake.!!
Ya dago kai sannan ya dora, kiyi hak'uri nasan ba lallai kin shirya karb'ata ko kuma na chanchanci ki soni ba, amma inason ki bani dama mu dinga ko da gaisawa ne don Allah."
Magiyar da yayi ya k'ara sa mata tausayin da yanayin maganar shi ya sakata.
So.."? Yau kuma"? Yanzu, ake furta mata shi."?
Ji take kamar babu wanda ya taba ce mata hakan a duniya.
Taji zaman
wajen ya gundure ta, kamar ta tashi bar gurin, amma babu dama.
Gashi shi kuma tun bayan da yayi maganar yayi shuru ya koma kalar tausayi yaki ya k'ara furta mata koda kalma d'aya sai kallon ta da yake ta faman yi...
H hameeed!! Sukaji an kwallo mata wani kira, wanda hakan ya sasu waige waige shi da ita.
Wata budurwa ce take tahowa daga wajen gate, sanye take cikin riga da skirt na atampha sai wani siririn mayafi wanda iyakarshi kafad'ar ta.
Da wani irin sauri take tahowa. Da alama ba cikin hayyacinta sosai take ba.
Tana k'ara isowa kusa dasu Hafsah na k'ara fahimtar wacece. Don haka da saurin ta mik'e saboda mamaki.
Da gudu ta k'araso, ta rungume Hafsah gam, kafin Hafsan tayi wani yunk'uri, cikin kuka take magana..
"H. Hamid, Yusuf.. Yusuf!!
Mamaki ya cika ukhashatu, ya lura ita ma Hafsah a razane take, sannan yana lura da yadda take ta kokarin kwace jikinta.
Da k'yar ta iya kwacewa, suka tsaya kallon juna.
"Ukhasha ya mik'e, ya kalli Hafsah, naga kinyi bak'uwa, koh, bari na barku ku gaisa. Thank you.!!
Ya juya, ya kama hanyar fita. Basma ta bishi da kallo.
Hafsah taji kamar ta kurma ihu, wannan wacce irin masifa ce, Basma a gidansu, a irin daidai wannan lokacin da take da bako irin wannan, kuma yake furta mata abubuwa masu muhimmanci."??
Ta bishi da ido har ya isa gate tana gani, sukayi musabiha da mai gadi, yana fita ta juya itama da gudu ta wuce cikin gida, bata tsaya ko k'ara kallon Basma ba.
Aka bar Basman a tsaye tana tunanin abinyi...
📝
*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH*
[17/03, 2:40 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*
📄 *54*
*Ganin* zata b'ata lokaci, yasa tabi bayan hafsah da gudu itama.
Acikin gidan kuma Zainab da Mufida na zaune a parlour suka ga Hafsah ta shigo kamar anjeho ta tana hak'i.
A razane Zainab ta mik'e tana dube-dube, zatonta wani abin ukhasha yai wa Hafsan, tana bud'e baki da nufin tambayar hafsah ~meya faru ta shigo haka."?~ sai ga wata ma ta shigo da sauri, Zainab ta ware ido ta kalleta sosai sannan ta fara gano wacece.
Itama mamaki ne ya sa ta tsaya shuru, babu abin cewa, kafin ita wacce ta shigo d`in ta nufi Hafsah ta rirrik'e ta, H. Hameed baki ganeni ba ne... Basma Yunus ce, kiyi hak'uri abinda nayi miki wallahi sharrin shaid'an ne nima yau na tabbatar Yusuf ba d'an goyo bane, nima yayi min abinda mukayi miki.. Yusuf ya yaudare ni yaci amanatah..
Ta fada da iyakacin k'arfinta cikin kuka, wanda sautinta ya tsorata su, sannan har ya isa ga kunnen mama da ke can d'akinta.
Hafsah tasa k'arfi ta ture Basma lokacin da take wasu maganganunta.. Don Hafsan ta gaji da abun, gani take mene had`i kuma yanzu.."? Bata da wata alak'a tsakanin ta da su dukansu d`in.
_Hafsah ki zo, mu yaki Yusuf ki manta da abinda ya faru, don Allah, mu kwatarwa kanmu yanci mu hada kai kinji.. Mu ganar da shi kuskuren sa, nayi alkawari indai kika yadda to zan bar miki Yusuf bayan mun koyar da shi darasi dama ni Abbana aure zaiyi min, zan kyale miki shi wallahi da gaske nake.!!"_