← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 88

Sashe 34

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ashe marmari ce daga nesa.'😳 'To yau gashi abu ita ma ya sameta kuma ta rasa mafita.'. "A tunaninta ko dai tayi wa Yusuf wani abu ne shiyasa ya rama.'?? 'Me yasa yanzu sai ka yarda da mutum, yake cin amanarka?.. W'ani Babban abin takaici shine gashi dai k'iri- k'iri tana jin zafin Yusuf, amma kuma gefe na zuciyarta na k'ara wassafo mata shi, da kuma karanta mata kada ta rabu dashi, tun da shima bai nuna mata ya rabu da ita ba.." 'Ita kanta tasan idan ta rabu da Yusuf, to tabbas tayi wa rayuwarta illa, tasan zuciyarta ma bata da jarumtar jure hakan.'.. Dole ne ta rungumi abinda yai mata, ta yi d'amarar kwato shi itama da k'arfinta, don idan ta barwa 'Basma' shi to tabbas ta tafka babbar asara, kuma Basma tayi nasara akanta kenan..'? Banda kuma dumb'in soyayyar shi dake dank'are cikin zuciyarshi, wacce bazata iya sadaukarwar da ita ba ga wata'.. 'Ta sani aiki ne a gabanta ja, amma bata san ta ina zata fara shi ba.' Dole ne dai tabi umarnin Abba idan tana son zaman lafiyarta, to idan kuma babu fita ta ina zata dinga had'uwa da Yusuf'? 'Tasha alwashin idan taga basma sai ta yi mata abinda bazata manta ba, sai ta d'and'ana mata b'akin ciki ita ma...' Sallama ta jiyo a falo kamar ta Aysha, amma kuma kusan minti uku bata shigo d'akin ba kamar yadda ta saba.' 'Sai kuma taji an turo k'ofar. Mama ce tsaye kanta, "Sai ki fito ai." 'Abinda tace mata kenan, ta juya.' 'Ta mik'e ta fito, taga Aisha zaune, ta d'an saki fara,a, tazo kusa da ita ta zauna.' 'Ta lura da hararar da mama ke aika mata da ita.' 'Tayi yake sannan tace "Aysha Sannu da zuwa" "Yawwa" "Ya mamanku"? "Lafiya lau wllhi." 'Duka sukayi shiru saboda ganin idon Mama.' Ita Aysha nason tayiwa Hafsah zancen jiya kuma tana son kwantar mata da hankali, shi yasa tayo azamar tahowa lokacin baifi 11:00am, ba. Don tun jiya hankalinta ya kasa kwanta wa.' 'Hafsah ta lura da akwai magana don haka ta mik'e muje d'aki, "To" inji Aysha, taji kuma d'adin hakan.' 'Dama tunda tazo bayan sun gaisa da Maman, zata wuce d'akin Hafsan, mama tace ta dakata Hafsan, tafito.' 'Aysha na mik'ewa hankalin Mama ya yo kansu' fuskarta a d'aure ta kalli Hafsah, "Ina kuma zaku je"? "Um bed room zamu shiga." "Ba inda Zakuje, ku zauna anan." 'Har yanzu bata saki fuskarta ba.' 'Hafsa taji kunyar hakan, tare da jin takaicin Mama, "Meyasa take mata hakane yanzu."? "Mama mai fara,a ga k'awayenta"? 'Amma yanzu duk ta sauya'? 'Dole ta dawo ta zauna ita da Aysha sukayi shiru.' sai can ne ma Ayshan k e sako mata hirar makaranta jefi jefi.' 'K'arar wayar Mama yasa ta shi da sauri ta nufi d'akinta, ta basu iska.' 'Tana zuwa tashi Aysha ta bud'e baki.' "Don Allah Hafsah kada ki dinga saka damuwa don Allah wallahi bansan abinda zamu tarar ba da bazan kaiki ba, badai je gidansu Basma ne na tarar zata fita, kuma dana karb'i wayar ta sai naga yusuf ya mata text d'in address d'inshi.' ta dakko wayar ta tana nuna mata.' 'Ta cigaba da cewa, "Don Allah,ki cire Yusuf aranki don wallahi ba saurayin da za,a zauna da shi, bane." 'Hafsah ta zaro ido, zatayi magana kenan, Mama ta fito daga d'aki, tilas tayi shiru da bakinta.' 'Aysha bata jima ba ta mik'e, "To mama na tafi, hafsah sai anjima." "Ki gaida gida." 'Mama tace mata.' 'Aysha ta mik'e don raka ta.' "Mama ta murtike fuska, Saura ki fita daga cikin gidan nan." 'Suna fita daga falon Hafsah ta fara bawa Aysha ha'kuri.' "Don Allah Aysha kiyi ha'kuri da abinda mama tayi miki, wallahi tun jiya bayan dawo take fushi." 'Aysha tayi murmushi,' "Babu komai wallahi." 'Amma don Allah ki rage damuwa wallahi har kin fad'a, daga jiya, ki daina saka abin aranki, kada mama tayi zargin wani abu." "K'walla ta cika idanunta, Aysha dole na damu, Yusuf fa.." Kuka ya hanata magana.' "Kiyi ha'kuri dai. "Ni dai shawarata ki cire shi daga ranki, don Allah, shine kawai maslaha." "Hmm Aysha bazaki gane ba kawai." "Allah ya kyauta, ki koma kada mama ta ga kin dad'e." "To nagode Aysha ki gaida mamanku." 'Aysha ta d'aga mata hannu sannan ta fice daga gate d'in gidan.' 'Hafsah ta tsaya ta goge fuskarta sannan ta dawo cikin gida, ta tarar maman na zaune inda ta barta.' 'Zata wuce d'akinta kenan, Mama ta kirata.' "Ke zonan" 'Ta dawo ta zauna a kujera.' "Mama gani" "Wannan Yarinyar daga ina take"? 'Hafsah taji banbarakwai.' "Um, k'awata ce ita fa mukayi photo ranar graduation." "Bana son jaye jaye" 'Hafsah ta gyad'a kai kawai, tana Mamakin Mama.' 'Kuma, bana son zaman cikin bed room d'in nan da kike, ko uban wani ne yake korar ki daga falon'? 'Ta girgiza kai.' "To kada in sake ganin kin kwanta." 'Dole ta nemi guri a falon ta kwanta, saboda idan tana, 'Menstruation' ciwon jiki take fama, ga kuma kasalar son kwanciya.' 'Mama da ta ga ta kwanta taji saurin cewa, "Tashi maza kije ki gyara daki'n abban ku, kuma, ki wanke toilet d'inshi." 'Badon ranta yaso ba haka ta mik'e ta nufi d'akin Abban, tana murje ido, to da wanne zataji da fushin mama ko kuma abinda ya dami zuciyarta.' 'To haka ne yake ta faruwa kullum har wajen sati d'aya, Hafsah da son yawan yin tunani, mama kuma da son matsa mata, ga kuma tambayoyi da take damunta dasu, "Kya ma fad'i inda kika je" 'Ita dai, Mama batun fitar nan, ya tsaya mata aranta.' 'Hafsah ta kasa gano dalili.' 'Ko sanda ta fita ita da yusuf daga gun party, bata d'auki zafi haka ba.' 'Hafsah ji take ita kad'aice mai matsala a duniya.' 'Abinda Yusuf yayi mata ya ki barin zuciyarta ga uwa uba kuma kewarshi data dameta, tun ranar bai nemi inda take ba gashi bata da wata hanyar contacting d'in shi.' 'Tsoro ya cika zuciyarta.' shikenan basma ta k'wace mata yusuf d'inta da take so.' 'Matuk'ar zata tuno shi to tabbas sai tayi hawaye.' 'Ta yi rama, kallon daya zaka yi mata kasan tana cikin damuwa, duk maganar da mama ke mata kan zaman bed room taki ta daina.' 'Abin ya dami kowa cikin gidan, k'annenta sun lura ta rage walwala.' Bashir kullum sai ya tambayeta me yake damunta, amma amsar guda d'aya ce babu komai.' 'Abinda ya tashi, hankalinta shine, bashir yace mata, "Yaya Hafsah jiya antaso mu daga school naga wannan yusuf d'in shida k'awar nan taki a mota danja ya tsaida mu." 'Gabanta ya fad'i ta shiga damuwa sosai.' 'Kenan yusuf ya ajyeta.. Ya daina yayinta..? bazai rabu da basma ba,??.. 'Ta fita muhimmanci a wajanshi kenan...'?? 'Ta kasa hak'uri har sai da ta zubar da hawayen tausayin kanta bayan fitar bashir. Ita dai son Yusuf ya zame mata 'GUBA' 'Abba, a dole ya kira Yusuf, a waya.' "Hello." inji Yusuf.' "Assalamu alaykum." 'Inji Abba.' "Wa alaykum salam" "Ina magana da yusuf ne"? "Eh nine." "Yawwa, ka gane mai magana." "A,a." ('Don Yusuf sam baiyi serving number ba') "Okay Abban Hafsah ne.' Yusuf yaji fad'uwar gaba, kada dai yarinyar ta fad'a wa ubanta abinda ke faruwa." 'Ya daure dai yace.' "Daddy ina wuni" "Lafiya lau. 'Abba ya fad'a cikin fara,a.' "Am dama so nake in tambayeka ka." 'Yusuf ya d'auke wuta saboda fargaba' "Hafsah ta fad'a mak a ina son ganin ka"? 'Yusuf yai wata wawuyar ajiyar zuciya' "Huuam, No, bata fad'a min ba daddy." Abba yai murmushi lallai ma shida aka fad'a mishi a gabanshi.'? 'A lokacin ya gane inda yusuf ya dosa.' "Abba yace ok shikenan.' "Idan babu damuwa gobe ko jibi kazo, ina son ganinka." 'Ya yi shiru, sai da abba yace "Kaji"? Sannan yace okay Daddy." "Abba yace nagode sai anjima." 'Abba ya ajye wayar yayi shiru yana nazari, yasan da k'yar idan yaron zai zo.' 'Hakan ya tabbatar mishi irin yaran nan ne da ba aure suka shirya yi ba, sai dai su hure wa yarinya kunne.' 'Saboda haka ko yazo d'in ma zai san matakin da zai d'auka kawai.' 'Mama ma a neman tata maslahar, da suna waya da yayarta take ce mata, "Wallahi yaya da akwai matsala ne" "Lafiya dai ko"? "Hafsa ce dai." Yayar tayi dariya, "Hmm amina kenan, kin iya dagula al,amra kila ma ba wani babban abu bane." "Hmm, Yaya Yarinyar so take tafi k'arfina wallahi." Ke amina wannan wacce shashashar magana ce, ki haifi 'yar ki dinga kiran tafi k'arfinki."?? "Ki dinga saita bakinki don Allah." "Hmm yaya.." 'Kada ki fad'a min komai ki bari gobe zan shigo.' "To shikenan, yaya na gode." 'Yayar ta kashe wayar tana dariya.' 'Washe garin wajen k'arfe goma sha biyu, Hafsa na zaune a falo, ta kasa samin nutuwar zuciyarta kiyasta wa take yau kome zai faru sai ta tura wa yusuf koda text ne.' 'Tana cikin tunanin ne 'Aunty Nafisa.' ('Maman ya Nazeer') Tayi sallama hafsah ta amsa mata kuma ta d'an saki fuskarta. 'Tayi mata Sannu da zuwa.' "Mama na jiyo sallamar ta ta fito da sauri, Aunty sannu da zuwa." "Yawwa Ameena." "Ina wuni" inji mama "Lafiya lau." "Yasu Naseer da Fatima"? "Duk lafiya lau suke, nazeer shirin Service ('NYSC') ma yake" "Allah sarki Allah ya taimaka to." "Amin, ya yaran gidan." "Suna nan k'alau sun tafi makaranta ne." "To ya Abban su Hafsah"? "Lafiyar shi lau wallahi." "To Masha Allah." 'Hafsah ma ta gaisheta' "Bari in kawo miki lemo." 'Mama ta mik'e.' "A,a ki zauna mana ga Hafsah." "Ta Kalli Hafsah 'yan mata an yi candy koh."? "Maza ki kawo min ruwa ne kinji, ki daina barin mama tana aiki ke kina zaune." Hafsah tace, "To" 'Maman Naseer ta kalli Mama, "Muje ciki koh"? 'Suka mik'e duka suka yi daki'n mama.' 'Hafsah ta d'oro ruwa da lemo da cup a plate ta bisu da su.' 'Ta ajye sannan ta fito, ta dawo falo.' "To Sannu kinji"? 'Inji maman ya Nazeer.' .'Ta tsiyaya ruwa tasha, sannan ta kalli mama sosai cikin nutsuwa tace.' "Me yake faruwa ne ke da 'yar taki."? 'Mama ta gyara zama cikin damuwa take karanto mata.' "Kinga dai abinda tayi ranar bikin abdallah, to kafin nan sai da taje gidan Hajiya kakarsu... Nan ta
Chapter 34 · 0% Book details