← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 88

Sashe 35

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zayya no mata duk irin abubuwan da Hafsa tayi har tazo kan fitar da tayi bata sani ba.' "Ta, k'arashe zancen da cewa ni tsoro na ma, kada inje yaron ya lalata mata rayuwa..." 'Auntie tayi saurin d'ago mata hannu.' "Haba amina, wannan wacce irin magana ce mara ma,ana kike yi.?? ina tunanin ki ya ke, da zaki yiwa 'yarki wannan mummunan zaton'? "Allah dai yasa baki furta wa babanta wannan shirmen ba." "Auntie kinga fa ranar data dawo har magariba tana aikin kuka, sannan kullum cikin tunani take, idan ba wani abu ba mezai kawo haka"? "Hmm, kin bani da dariya amina, shiyasa kike kyararta kika zuba mata ido koh,? Gaskiya tunaninki yayi Kama da na yara." 'Kawai kuma don yarinya ta fita ta dawo bada saninki ba, sai ki hau zarginta koh."? "To dai ki chanja tunani, don me bazaki jata ajiki ba kiji damuwarta, ai ko bata fad'a miki ba zaki fahimci me yake damunta koh." 'Ni kin b'ata min rai ma wallahi.' "Yanzu dai, koma menene zan tafi da ita tayi koda sati biyu a wajena.' "Shikenan aunty, nagode." 'Ita kuwa Hafsah ganin babu kowa a falon kuma ga wayar mama data bari yasa tayi saurin d'aukar wayar tayi d'akinta tana godiya ga Allah.' 'Cikin azama ta hau rubuta text, 'Ban tab'a zaton zaka yi min haka ba, koda a mafarki,..idan nayi maka wani laifine, sai ka rasa ta hanyar da zaka hukunta ni, sai kaci amana ta,??.. Yusuf cutar da kayi min ba,a tab'a yi min irinta ba'.. 'Nagode sosai, bisa sakayyar da kayi min.'.." 'Hafsah H. Hamid' 'Ai kuwa minti kad'an sai ga reply, "Hmm Hafasah kenan, shine yasa kika sa Abbanku ya kira ni koh..'So ya kirani kuma yace min yana son ganina." Hm kin fad'a mishi ne koh.."? "Tana cikin karantawa sai ga su Mama ad'akin, nan tayi tsuru-tsuru, mama ta rufeta da duka da hannu, tana fad'in kinganta koh.. Kinga dai abinda takeyi.' 'Maman ya Naseer, ta rik'e hannun Mama, tana fad'in haba ki bari mana Amina, don Allah kibi komai a sannu.' 'Suka zauna, sannan Auntie ta d'auki wayar, text d'in Yusuf, ta fara karantawa, ita ma kanta ya kulle gaskiya ne akwai abinda ke faruwa.' 'Sai kuma ta kuma duba na Hafsah, sannan hankalinta ya d'an kwanta.' 'Ta ajye wayar sannan ta kalli Hafsah.' "Me yasa kika d'aukar mata waya"? "Cikin kuka take cewa babu komai." "To me kika yi da ita."? "Ta, kuma, cewa babu komai." "Hm, babu komai fa kika ce, amma kika d'auki wayar."? 'Cewar Auntie.' "Um, game nakeyi" 'Auntie tayi murmushi.' To kada ki k'ara d'aukar mata waya.' "To" "Ta dafa kafad'arta.' Tashi maza ki deb'o kayanki kinji, gida na zaki je, tun da yanzu bakya zuwa makaranta.' 'Hafsah bataji dad'in hakan ba, ta mik'e babu k'wari ta fara debo kayan daga cikin drawer.' 'Shaf ta manta da ledar nan ta Yusuf, aiko tana dakko wasu kaya, ledar ta fad'o.' 'Mama tayi saurin d'aukar ledar cikin rud'ewa ta ke cewa Auntie kin gani koh, ai mai hali baya fasa halinshi." 'Auntie ta karb'i ledar ta bud'e, sai taci karo da kwalin wayar mai tsadar gaske wato, 'IPhone' a ciki, sai wani tsadadden agogo, sai turare mai tsadar gaske, sai kuma, 'Greeting card' 'Auntie ta mayar da kulle ledar dama rubi biyu ce.' 'Hafsa ta gama shirya kayan sannan ta kulle akwatin, tasa hijabi, suka fito dukansu.' 'Auntie tace maza ki kai kayan cikin mota.' 'Ta ja akwatin tayi waje inda drivern auntie take.' 'Auntie ta kalli Mama bayan fitar Hafsah, "Ki bar komai a hannuna, ba wani abin tashin hankali bane ina zatan kyauta aka kuma bata, in sha Allah komai zai yi daidai.' 'Mama tace "Toh" Ina wayarki kira Abbanta zanyi mishi bayani da kaina.' 'Mama ta danna kiran, bayan ya d'aga "Hello, barka da rana, ya aiki." "Alhamdulillah, aiki yasani gaba." "Allah sarki to "Sannu da k'okari." "Yawwa." "Dama, Auntie Nafisa ce tazo tana son kuyi magana ne." "Okay to bata wayar." "Sun gaisa sannan ta ce, nazo ne kuma sai Amina keyi min k'orafi akan Hafsa, to shine ina so abani ita don Allah in tafi da ita tayi koda sati ne a wajena." 'Abba bashi da matsala da ita, kuma yasan ta macece jajirtacciya,kuma babba ce, don haka yace, "babu komai ai, yayi kyau wallahi, na gode sosai." "Sai dai Don Allah kada a barta ta kula duk wanda yazo wajenta, kuma kada ta dinga yawo." "To in sha Allah, na gane babu komai ai." "Yawwa, wani yaro ne yake son wargaza mata lissafi." "Auntie tace "Eh na fahimta, yaran yanzu ne babu abinda suka sani sai soyayya." "Wallahi kuwa, Allah ya kyauta ya shige mana gaba." "Ami'n inji Abba, to nagode fa, agaida alhajin." "To zaiji in sha Allah." 'Ta, kashe wayar ta mik'awa mama.' "Ki dinga yi mata addu,a, amma wannan ba wata matsala ba ce Babba, kinga shi baban nata ai ya fahimci komai." "To auntie, nagode." "To bari mu wuce." 'Auntie tace sanda Hafsah ta shigo.' 'Mama ta taka musu zuwa bakin gate.' "Mama mun tafi." 'Inji hafsah.' 'Maman ta saki fuska sosai to hafsah in kuma auntie ta rik'e ki shikenan sai ki zama bak'uwa." "Hafsah tayi murmushi, taji dad'in sakin fuskar da mama tayi." 'Suka shiga mota suna daga wa mama hannu. Driver yaja suka tafi.' 'Hafsah taji kamar tayi kuka, bata tab'a yin tafiyar data wuce kwana biyu, shima gidan Hajiyah take zuwa, amma taji auntie tace wai sati biyu zata yi..' 'Gaskiya zatayi kewar jama,ah da dama.. 'Amma haka dai, zata hak'ura.' 'Sai kuma kalaman yusuf a text to kenan Abba ya kirashi,?? To me yake nufi da ita, da yake cewa wai tafad'awa abba koh..?? 'Lallai ma Yusuf, Allah yaso ta sa number a blacklist, bayan shigowar text d'in saboda tsoron kada ya kira Mama.' 'Ta jingina jikin kujera, tana tunano ya zata kasance idan Yusuf ya guje ta... Shikuma driver sai gudu yake kan titi har suka isa unguwar Kabuga, inada gidan Auntie yake..'👏🏼👏🏼👏🏼 *TO ALHAMDULILLAHI READERS, FANS, ANAN MUKA GAMA KASHI NA D'AYA NA WANNAN LITTAFI SAI KU JIRA KASHI NA BIYU, DOMIN JIN YA RAYUWAR HAFSAH DA YUSUF ZATA KASANCE.'??* *A cikin..*👇🏼👇🏼👇🏼 ♥♥♥♥ *ZAZZAFAN SO* (Masoyin Kwarai) 💔💔 👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼 *'Jikar waziri Ahmadu dai..!!*👌🏼 *(HAJEEYAH KAREEMER)*
Chapter 35 · 0% Book details