← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 88

Sashe 33

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sunan shi" "Haha, 'Abba yayi 'yar dariya..' "Ya akayi kika manta"? "Babu komai" "Hmm, to meyasa ki ke ta kuka."? 'Tambayar ta razana ta.' "Babu komai." "Wani ya dakeki ne"? 'Ta girgiza kai.' "Hmm tom yayi kyau " 'Ya tsare gida sosai ya kuma nuna ta da yatsa' "Hafsah, Hafsah,!! Ki kiyayeni cikin sha,anin fita daga gidan nan batare da kin fad'a min ko kin fad'awa mamanki ba, haka kika ga bashir nayi? Ace k'aninki yafi ki hankali'? Wallahi kinji na rantse idan kika kuma fita ko nan da k'ofar gida ne bada sanina ba sai na yi mummunan sab'a miki.!!" "Kin manta kwanaki koh? To zan hanaki fita gaba d'aya ma." "Abba kayi hak'uri." Kada in sake jin wata k'awa tazo kun fita ke da ita ko ina kuwa zakuje, kina jina"?? 'Ta d'aga kanta.' "Ki kiyaye kafin na sab'a miki fa" "To Abba" "Ta shi ki fita saura inji labarin kink'i yin bacci." 'Ta wuce d'aki, ta kwanta' ko babu komai fad'an abba ya shige ta, da tana bin umarnin shi da bazata fita ba bare taga wannan abin bak'in cikin.' 'Ta d'akko Diary tana son ta rubuta wani abu a ciki, amma kuma ta kasa saboda cinkushewar zuciya.' Da ta d'ora biron akai sai taji hawaye ya cika idanunta." 'Ta cillar da Diary gefe guda, afili ta furta "Yusuf wai you choose to BROKE MY HEART??😭😭😭 'Ta kife kan pillow tana rizgar kuka har bacci ya d'auketa.' 'Washe garin ranar tatashi babu yabo babu fallasa, sannan kuma taji kwata kwata bata k'aunar fita ko da falo.' 'Ta daure tayi wanka ta koma gado ta k'ara kwantawa zuciyarta ce keson yi mata 'Karatun baya' 'Ta dinga tuno farkon had'uwar ta da Yusuf, halayenshi da ya dinga fito mata dasu, yadda Basma, ta fara chanja mata, da kuma zancen zuwanta birthday, sai kuma abinda ya faru ranar birthday d'in da kuma wanda idanunta suka gani jiya.' 'Ta rantse idonta, ta cije lebe, hadi da huro iska daga bakinta, ta dad'e tanajin ana cewa NZAFIN SO,' ko kuma 'SO GUBA NE.' 'Amma ita da yake tun farko rayuwarta bata ginu akan Soyyayya ba bata gane zancen sam.' Tana jin haushin Jamila idan ta dameta da zancen 'Salim' ko ta zauna kod'a mata shi.."Ai Salim ya had'u, ina sonshi d'an beauty nah.." 'Wani lokacin har tsaki take yiwa Jamila, "Aikin banza shi mutum kamar kowa amma kita faman wani rawar kai kina kod'a shi kamar wata marok'iya sai kace da 'Gold' akayi shi.. Mtsw"😠 'Idan ta tuna jamila murmushi takeyi ta ce mata, "Hmm Hafsah bazaki gane ba ne." 'Akwai ranar da wata 'yar ajinsu a islamiyya tazo tana ta rizgar kuka, har da bubbuga benci, Hafsah har dariya taji ta bata. "Wai saurayinta ne ya zagaya yana son k'awarta.' 'Ko lokacin suna tare da Yusuf, amma hakan bai hana ta yin dariya ba, musammaman data ga bilhak'k'i kuka take yi.".. "Tana ambaton an cuceta." 'Ita dai dramar soyayya na burgeta.'
Chapter 33 · 0% Book details