← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 88

Sashe 87

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Za'a fara bikin ranar Laraba a gama Asabar.
Batun had'uwa wajen amarya babu misaltuwa tayi kyau sosai tasha gyaran jiki.
Sai ana saura sati biyu sannan aka kawo lefe.

Masha Allah baby k'arya aciki anyi abune daidai karfi akwatuna set biyu golden da silver colour.

Kaya sunyi sosai Auntynsu Ukhashatu tayi kokari na had'o kaya masu inganci.
Kowa sai sa albarka yake ana yabawa.
Jamila tazo taga kaya tasa albarka tayi murna sosai itama.

Har zuwa satin biki inda ango yayiwa amarya wuyar gani haka itama saboda hada-hada.

An fara Biki cikin nishadi da nasara Hafsah taga Masoya tako ina haka Ukhashatu har wadanda batayi tunanin gani ba sai da ta gani bata bige da mamaki ba sai da taga Basma a wajen dinner ta ya kayi ta samu card admit oho ko kuma babu mamaki tunda katin yaje hannun yan makarantar su da dama.

Bikin yayi dad'i an gabatar da GAME na amarya da ango inda suka kayatar da jama'a. Biki yabar tarihi.
Daga k'arshe ranar asabar misalin k'arfe 11:00pm aka shaida daurin auren *UKHASHATU ABUBAKAR KHADI DA HAFSAH H HAMID.*

Farin ciki wajen ango baya misaltuwa ya gaza boye hakoranshi kowa albarka yake sa mishi da fatan alkhairi.

Su Fadwa an samu k'awa Amira tun farkon kayaniyar bikin suka jone saboda halinsu yazo kusan d'aya.
Amarya tasha kuka musamman sanda aka daura mata aure inda ta tabbatar yau ba ita babu kwanan gidan Abbanta.

Hajiyarsu (kakarsu) ke ta tsokanar ta wai ana so ana kuka don itama ba karamin farinciki take da auren ba.

Da yamma yan daukar amarya suka zo. Amarya tana rizgar kuka haka maman ya Nazeer ta sata tayi wanka ta shirya tasha wankan turaruka har suka fara damunta.
D'akin Abbanta aka kaita wanda Dakyar ya daure ya iya yi mata takaitacciyar nasiha da addu'oi wanda shima daga karshe rauni ya hana shi k'ara sawa. Hakan yasa Hafsah kara fashe wa da kuka..

Mama kam babu abinda ta iya ce mata. Amma dole jama'a suka sa ta ta sa mata albarka. Tasha adduoi.

An kaita gidan khady inda Hajiyar Ukhasha ta bata kyauta ka sun karb'i amarya hannu bibiyu sannan ta bada wata tsadaddiyar alkyabba su Fadwa suka d'orawa amarya akan kayanta.

Daga k'arshe an kai amarya gidan ta bisa rakiyar yan uwa abokan arziki.

Gida ya tsaru kowa sai yabawa yake amarya tasha kaya sai godia ga iyaye.

An barta ita kadai yayin da kukanta ya kara tsananta don ma gidan estate ne ba ita kadaice a ciki ba. Maman ya Nazeer ce ta hana abar kowa saboda akwai tazara kuma dare ya fara.

Amarya tayi jugum cike da tsoro shuru amma ango ba zo ba.
Shi kam yana can Abba na mishi nasiha sai daga karshe abokan shi suka taho domin raka shi. Sunyi musu takaitacciyar nasiha agurguje saboda dukka sun baro iyali.
Daga karshe ango ya tafi raka su ya dan Jima kafin ya dawo.

Ya dawo ya tarar da amarya a rakub'e saboda tsoro yayi murmurshi sannan ya nufe ta cike da wani irin shauk'i ji yake kamar bashi ba. A bude min fuskar mana amarya....

Hafsah ta tsinci kanta cikin wani yanayi mai dad'i cikin rayuwar aurenta..sosai angonta ke tattalinta da nuna mata kulawa ta yardar wa kanta tabbas Ukhasha shine dai dai da rayuwar ta kuma zabin Allah ne.
Ba zata tab'a kwatanta soyayyar shi da k'warewar shi wajen iya nakaltar komai nata da iya sata nishadi da Yusuf ba sam.. tana godewa Allah duk sanda ta budi ido ta tuna Ukhasha ne amatsayin mijinta.

Ko yaushe shi maiyi mata hidima ne ta ko wanne fanni ga barkwanci da sata nishadi..sai dai kasancewar shi dan adam itama ta fahimci abubuwa da dama game dashi.

-Yana son mace ta dinga mishi hidima.
-Sannan yana da fushi sai dai ya iya mallakar fushin shi. Ba ko yaushe ne idan yayi fushi take fahimta ba a da sai daga baya ta gane duk sanda ya tambayi abu sannan a lokacin kuma ya nuna abarshi, koda fuskarshi bata nuna ba to abadini fushi yayi.

Hakan yasa dole ta koyi abubuwan da suke saurin sauke fushin shi kuma ta zama jaruma wajen iya sarrafa shi. Shi kan shi baya iya dogon fushi da ita. Takan jin jina mishi kan komai dayi mishi godia akan komai yayi mata. Da kanshi yakan tsokane ta idan ya siyo mata koda ice-cream ne kafin ta fada sai ya mak'e murya ya tsokane ta yadda take magana.
"Thank you mu luv."!!
Sai ta harare shi tace "wa ce."?
"Mrs Ukhashatu mana.!!
Sai tayi murmurshi.

Yayan shi ya shirya musu fita kamar yadda ya shirya wa kaninshi sanda akayi bikin shi shima

Ziyara ce ta kasashe biyu Saudia da Dubai inda sauyi Umra sannan su wuce Dubai.
Jin dadi wajen Hafsah babu misaltuwa tayi godia ga Allah. Sun biya ta gidan Aunty babbar yayar su Ukhashatu a abuja saboda ta can zasu wuce sai da suka kwanan mata daya sannan suka wuce.
Ta nuna wa Hafsah soyayya matuk'a da tarairaya..

Jirginsu ya daga inda Hafsah ke cike da farinciki. Taji dadin tafiyar sosai kuma tafiyar tabar mata tarihi mara misaltuwa ta k'ara tabbatar da matsayin ta a zuciyar Ukhasha ya bar mata (memories) da dama da soyayyar shi da bazata iya kwatanta ta da komai ba. Taga kulawa da tarairaya..

Sun shafe watanni biyu a tafiyar..

_______________________
Jamila jira take Hafsah ta dawo (domin taji labarin tafiyar su) so take tayi mata albishir da mijin data samu itama kamar abin wasa a wajen bikin Hafsan sai dai yana da mata amma yayi mata sosai iyayen ta sunyi farin ciki itama.

Basma ta kammala karatu amma shuru duk cikin samarinta babu na aure..Duk da aranta har yanzu tana jin kaunar Nour domin sonshi ya zame mata jaraba amma babu damar mallakar shi tasan ya riga ya mata nisa sai yanzu take nadamar abinda suka aikata. Nadama mara amfani.
Mahaifiyarta tayi aure mutumin kiri kiri yake nuna wa Basma banbanci da kyara. Dole ta koma gidan mahaifinta shima babu yadda ya iya dole ya yarda ta zauna. Duk da zaman gidan babu dad'i aure kawai take so tayi.

Domin anyi bikin auntynta Fatima tun lokacin nata sa ranar, ashe tare Abba yayi niyyar aurar dasu amma ta bujure. Bak'in cikinta shine yadda yawanci mate dinsu sunyi aure da 'ya'yayensu tsurari ne suka rage..

Yusuf sai da ya tabbatar anyi auren Hafsah sannan ya rarrashi zuciyar shi dakyar ya shiga neman aure bisa damuwar da maman shi ta nuna sosai kan hakan. Yasa a ranshi bazai auri watststsiya ba. Haka ya binciko wata yarinya mai siffar kamilai ya kuwa mutu akan sonta. Ashe kara da kiyashi ce daukar mara sani. Bayan chajar shi da suke ita da uwarta akayi auren Sannan ya tabbatar da lallai Dara ce taci gida.
Daga lokacin zaman su ya dawo babu dad'i kullum cikin fada da cin mutuncin juna. Yana kiranta mara tarbiyya ita ma take buda baki tace ai jirgi daya ya debo mu tunda ka ganni haka Allah ne kadai yasan iri n ayar daka sheke.
Dama ya dawo da komai nashi Nigeria saboda haka sai ya fice sabgar shi da ta dade bata sashi ido ba. Kullum sukayi fada sai ya tuno da Hafsah ya sani yayi babbar asara..

__________________

Hafsah sun dawo daga tafiya lafiya sunyiwa yan uwa tsara ba tayo wa Hajiyar shi tsara ba ta musamman.

Kowa yayi murna da dawo war su inda suka dawo da murnar samun Baby tun acan dama aka tabbatar tana dauke dashi.

Lokacin Ukhashatu ya maida hankalin kan tsara musu gidansu a gabanta yake tsara zanen yanayi yana tambayarta ranki ya dade yayi nan yayi.."?

___________________

Rayuwarsu abar sha'awa ga kowa. Yadda suke tattalint juna da yadda suke taka tsantsan da juna. Hafsah tayi imanin wannan abin yana samuwa ne sakamakon sirad'in na tarkon Yusuf da ta fiye mishi da babu wannan jin dad'in a rayuwar ta. Tabbas ta gani kuma ta amincewa zuciyar ta cewa *"THE VIRGINITY OF GIRL IS HER DIGNITY"!..*

Da ta zama watsatstsiya da tuni bata da wani sauran k'ima a idon mijinta da mutane ma baki daya..wai idan ma ta samu mijin auren kenan..

Hafsah ta kuma yarda lallai yawan tarin dukiya bashi ke kawo kwanciyar hankali da jin dad'in rayuwa ba. Soyayya amincewa juna mutuntawa da tattalin juna sunfi komai taka muhimmiyar rawa. Duk da haka tasan mijin ta kuma bai rageta da komai ba, bata nemi komai ta rasa a wajen shi ba. Sai dai idan ta kwatanta da irin burikan yan matan yanzu da yadda suke hangen rayuwar wasu da dogon buri zasu kwatanta Ukhashatu cikin tsaka-tsaki (middle class) ta fannin kud'i da tara abubuwan jin dad'in rayuwa. Amma a wajenta Ukhashatu k'arshe ne babu wanda ya fishi.

Sai yanzu take k'ara ganin abubuwa da dama wanda maman ya Nazeer ta dinga nusar da ita sanda tayi zaman gidanta. A lokacin data ke k'okarin dawo da ita hayyaci.
Bazata manta ba ta tab'a fad'a mata cewa.
_"Zaki samu wanda yafi Yusuf har kiyi alfahari dashi."_

Tabbas Yusuf baifi Ukhashatu a komai ba ta fannin wayewa, kyau Nasaba, da kuma iya mu'amala.

Abubuwan da za'a iya kira da 'banbanci sune kamar rayuwar turai da Yusuf yayi wanda ita a wajenta ba wani abun gani bane tunda babu abinda zai kara mata sai ma nisanta mutum da al'adunshi idan ya zama mai sakaci ma da rashin kula sai su jinkirta yanayin addini. AMMA FA GA WASU..MISALI IRIN SU YUSUF. wadanda iyaye ke sakarwa ragamar rayuwar su tun suna yara suyi yadda suke so...amatsayin Yanci.

Kwanci tashi babu wuya Ukhashatu ya kammala musu ginin dankakaren gidansu 'nagani a yaba'

Ranar da yakai Hafsah taga gidan k'asa magana tayi acikin gidan gidane da babu kalar macen da bazata zauna ciki ba. Ya baje barisa wajen tsara ginin gidan.

Sannan a ranar dai duk yayi mata albishir da offer daya samo mata ta aiki a wata ma'aikata ta gidan Jarida sai dai ya fada mata zata fara aiki ne bayan ta ajiye mishi Baby da watanni."
Chapter 87 · 0% Book details