← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 88

Sashe 54

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Allah-Allah* yake ya dawo gida, ya kira number da ya karb'a, number da ko sunan mai ita bai tambaya ba.
Biki yayi dad'i sosai. Ango da amarya kowa na cikin farin ciki, anci an sha, sannan an sha rawa, gobe shine kai amarya.
Ko a wajen bikin ma kiran bahijja wajen uku, amma bai ji bama saboda k'arar kida bare ya d'aga.
Sanda suka dawo gida kuma, wajeny misalin tara na dare, shi kanshi shakkar shiga gidan yake saboda Abba bare kuma k'annen nashi. Babu yadda ya iya biki ne na aminin shi, ya kamashi ne sosai abin, banda haka shima ba son hayaniyar biki yake ba, kuma muddin baiga k'annen shi gurin bikin ba bazaiji dad'i ba, shiyasa yaje da su na yau.
Yana parking suka fito, shima ya fito, bai wuce ko ina ba sai d'akin abban dake gefe.
Da sallama ya shiga, amma ba,a amsa ba, sai akayi gyaran murya alamar ya shigo.
Ya sami guri ya zauna, yana jiran abban ya gama jan charbin da yake. Carbin k'ato ne irin mai dubun nan, Allah ya so ya kusa gamawa, yana kammalawa ya kalleshi.
Ai kafin Abban yayi magana Ukhasha yayi. "Afwan akaramakallah, bamu dawo da wuri ba, abinne ba,a fara da wuri ba.."
Ya d'aga mishi hannu kawai.
"Mun gode, Allah ya k'ara girma." Zai mik`e Abban ya dakatar dashi da hannu. Ya dawo ya zauna.
Yayi gyaran murya kafin yace, "Kaje kiran da Baffan yayi maka koh."?
"Wata fad'uwar gaba ta ziyarce shi, _Abba yasan da maganar kenan, indai haka ne toh dole ya k'ara k'aimi don idan har Abba ya fara sa baki a maganar abin bazai mishi kyau ba._
"Eh naje Abba."
"To madallah, sai ayi k'ok'ari tunda ansan aje na wasu.
Ukhasha ya sunkuyar da kanshi kawai, a zuciyarshi yana cewa, _Ai ni na riga na samu.!!_
"Za,a iya tafiya, Allah ya bamu alkhairi."
"Amin, Abba sai da safe."
Ya fita, shima kanshi sauri yake yaje ya gwada number nan.
Yana ta k'okarin kira amma kiran Bahijja dake ta shigowa ya hana sau biyu yana _rejecting_ ya gaji ya d'aga rai a b'ace yace, "Wai ke meye hakane, ki kyale ni da-Allah, haba.!!
Ya katse kiran, sannan ya hau kiran number, _is switched off ake ta ce mishi_ amma ya k'i yarda sai kira yake yana kumawa,
har ya gaji ya daina, gaba-d`aya yaji ranshi babu dad'i to ko dai alhakin yarinyar can ne da yayi wa tsawa, tunda yasan irin son da take mishi bai dace ya mata haka ba. Nan take ya yanke shawarar ya kirata ya bata hak'uri ko shima Allah zai taimake shi, don ya tabbatar indai bai samu number ba ayau to tabbas ba zai iya barci ba, yarinyar ta rikita shi lokaci d'aya, musamman yau daya k'ara ganinta, ai ji yayi jininshi na tafasa, gaskiya ba k'aramin al amari ne ya same shi ba.

Ya lalubi, number Bahijja, ya kira, ringin kad'an tayi ta d'aga tare da sakin ajiyar zuciya. Shuru yayi itama tayi shuru, shi har ga Allah tausayinta ke tsarga mishi a zuciya. "Me yasa bakiyi bacci ba.?
Kawai ya fara da haka. Cikin shashshek'ar kuka ta fara magana, ba kaine kace kada na k'ara kiraka ba."?
"Ya isa toh, kiyi hak'uri kece kika batamin rai, ina gaban abbana kina ta kira.
Murna ta cika zuciyarta, yau ita ce, ukhasha ke bata hak'uri."? Wacce irin rana ce yau data zo mata da sa,a haka."?
Yana ji a kunnenshi tana sauke ajiyar zuciya, ta ma rasa me zata ce.. "I'm sorry.." Yaji tace, kana jin muryarta kasan tana cikin farin-ciki, shi kuma zuwa yanzu ya k'agu ya kashe wayar.
"Ok, kiyi bacci kinji."
Yace mata haka, amma ita sam bata son su katse wayar, yadda take jin farinciki yau, sai ta b'ige da mishi shagwab'a. _Um..um._
"Kinga koh, meyasa haka toh ina miki magana sai ki k'iji, ni inason nayi bacci ne toh."
Sai kuma ta shiga hankalinta. OKey Dear ka hak'ura da abinda mamana ta maka."?
Cikin k'osawa yace mata yes."
"Thank you."
"Okay gud night."
Yace mata, tare da kashe wayar.
Ita kuwa farincikin daya sa mata Allah ne kad'ai yasan yawanshi. Tayi wani juyi akan gado cike da murna. Sai murmushi take, _Yau Itace ya nuna damuwa da ita haka.. Duk da ba yau kad'ai yake cewa ta daina kiranshi ba, amma tasan duk ranar da yayi mata irin haka, baya k'ara saurarar ta. amma yau shine har da biyo kiranta..? Gaskiya taji dad`i da alamun nasara sosai a tattare da ita.

Mamanta ce ta shigo, ta tsaya akanta, bayan ta k'are mata kallo, ta lura da wayar dake hannun ta tace, waya kike da wannan mara mutuncin yaron koh."?
Ta ke ta had'e rai, "mama please ki bari, stop abusing him, ni banga me ya miki ba fah!!
Uwar Tayi kwafa, "Hmm, idan an zage shi sai me, banzar yarinya kawai, idan bakiyi wasa ba, sai na k'wace wayar taki ma.
Yar ta juya mata baya tana k'un-k'u ni.
_Bahijja, yarinya ce wacce bazata wuce shekaru 19, ba, asalin yaren mahaifiyar ta Ibra ce, mahaifinta kuma, bahaushe ne, mahaifiyar ta basa tare da mahaifinta, sun rabu tun tana yarinya, kuma ta hana shi ita. yarinyar na da kirki sab'anin mahaifiyarta, bata dad'e da kammala karatun ta na secondary ba.

A tsarin Ukhasha da ra,ayinshi, sam babu irin yarinyar a rayuwarshi, yanayinta, shekarunta, yanayin tarbiyyar gidansu duk baimishi ba sam, abinda yasa ma mu,amular su tayi tsaho haka, saboda yana tausayin yarinyar, gashi shekarunta sunyi k'ank'anta ace tana fuskantar abu irin haka, ban da wannan da tuni ya yanke mu,amalarsu ko ta Yaya ne..
Kawai shi ya yarda kaddara ce ta had'a su.

_Wato wata rana ne, garin anyi ruwa irin na asubahin_ _nan, shi kanshi badon dole ba, da bazai fito ba a lokacin, amma haka ya fito aiki. Kuma ranar sai ya chanja hanya akan hanyar da yake bi, saboda yayi sauri yaje inda zashi don ya so ya makara. Akan hanyar ne ya gamu da yarinyar cikin uniform, tana tsaye bakin titi, ta rasa mota. Da kanta ta tsaida shi, ganinta da uniform yasa ya tsaya._
_Sai da ta shiga, sannan tayi mishi magana "Ina kwana.."? Don Allah can gaba zaka ajye ni, na rasa mota ne."_
"Okay, yace, mata bayan ya amsa gaisuwarta.
Hankalinshi nakan tuk'i, ya manta wayar shi akan kujerar da zata zauna ya bari, sai dai ya lura kamar ta d`auke wani abu sanda zata zauna.
Lokacin da aka k'araso makarantar su, tace masa ya tsaya anan zata sauka.
Ta mik'a mishi wayar, kawai yasa hannu ya karb'a.

Tana ta godiya.
Shine ma ya tambayeta sunanta,
"Babu komai, ya sunanki ne, tace _Bahijja_ "kaifa.? Yace "Ukhashatu."
Tayi murmushi ta juya tafi.

To tun a washegarin ranar, shi dai bai san ya akayi ba, kira yake ta shigowa wayar shi, da wata number, tun bai d'agawa har ya d'aga take ce mishi, Bahijja ce."
Tambayar farko daya mata shine, "Ina kika samu number ta."?
Tayi dariya kawai, tak`i bashi amsa, sai cewa tayi, "Godiya na kira nayi maka."
"Kada ki damu."
Yace mata.
"Zamu iya dinga gaisawa a waya."?
Shi kuma ganin ta yarinya, kawai sai yace, "Eh k'anwata amma sai kin fad'amin inda kika samo number.
A wayarka na gani.
"Hmm.."ki daina d'aukar wa mutum waya."
Tace "Toh.
"Kayi saving number."
Zanyi, sa anjimanki."
Tun daga ranar take kiranshi, watarana ya d'aga watarana ya share, shi bai kawo komai a ranshi ba, ganinshi yarinta ce , kawai. Bai ankara ba har sun shafe wata uku.
Lokacin tace mishi ta gama makaranta.
Yayi mata murna. Sannan tace, "Ko zai zo partynta."?
"Bana zuwa party.!!
Yace mata.
Tayi shuru bata yi magana ba. Sai bayan da ya manta, kawai sai gata a gidansu, abinda ya tada mishi hankali kenan, ya akayi tasan gidansu. Ta kirashi a waya, ka ganni k'ofar gidanku za,a barni na shigo."?
Yayi dariya sannan ya gimtse, "Idan kika ce wajena kika zo za,a barki mana.
Shi duk cikin wasa yake maganar.
Minti kad'an ya jiyo ta window d`in d'akinshi suna magana da Fadwa a harabar gidan.
Tambayar ta take, "Don Allah ina zata ga ukhasha."
Ita kuwa Fadwa cikin mamaki take ta jero mata tambayoyi, wanne ukhasha."? Anan gidan, ke wacece, bama gurin Zainab kika zo ba."? Dake taga ba zata wuce sa,ar zainab d`in ba.
Babu shiri yana jin muryarta yayi sauri ya fito, lallai yarinyar bata da hankali da gaske take kenan.
Ya rasa da fuskar da zai tare ta, sai kawai ya had'e rai, "Ke dama da gaske kike."? Ita kuwa murmushi take na jindad'in ganinshi.
_"Eh, ai nasan gidan ku dama."_
Bashi da lokacin b'atawa wajen tambayarta ~_"Tayaya.?_~
Chapter 54 · 0% Book details