← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 88

Sashe 53

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ku bar angon ya je shi d'aya mana, tunda abin na mata ne."
Bashi da bakin magana sai yayi jim, kafin ya tuno abin fad'a, don baya son yawan tsawaita magana irin haka da Abban nasu, don ba,a nasara akanshi, sai dai idan yayi niyyar abu kawai zaiyi.

"Shiyasa zan kaisu tunda an gayyace su."
" Zaka kai ku dai, ai har da kai kaima zaka ce zaka kaisu, kawai kun bata abu ne yanzu, mata na biki kuce sai kunje.. Shi ango ai da walima aka sanshi ita yake had'awa shi."
"Tuba muke, ranka ya dad'e."
"Yaushe ne kace."?
"Yaune da yamma.
"To Allah ya kaimu amma ba,za,a kai dare ba koh."?
"In sha Allah."
Ukhasha ya fad'a. Don yasan ba tambaya bace a wajen abba umarni ne kawai, yana nufin kada akai dare, don yasan partyn da aka fita, dayin magriba ai dole akai dare.
Cewar shi ta 👇
( _amma ba za,a kai dare ba koh."?_ ) Girma ne da kuma iya magana yasa yake umarni da sigar tambaya, Don babu mamaki idan sunyi daren kaji yana tuhumar su, ~_"Bance kada akai dare ba."_?~

K'ofar d'akin da suke ya nufa. Ya tsaya a bakin k'ofa "Kuyi sauri fah, ni na fito." Da sauri suka fito, suna zolayar shi, "Yaya anyi kyau fah.!!

_______________
Suna zaune a kan kujeru, a wani wajen shak'atawa, Bashir Hafsah Zainab Ameera da Mufida.

Idon Hafsah ne ya hango mata wata kamar idon sani a wajenta, ita da wani suke tahowa, cikin takun k'asaita, kayan jikinta kamar sa b'arke saboda kama tan da sukayi, babu ko mayafi a jikinta. Suna k'ara nufo su tana k'ara wayewa da wacece, nan ta hau tab'a Basheer tana nuna masa ita da yatsa, "Basheer, ka ga wata, wallahi Jamila ce, ba bari dama na dad'e ina nementa."

Tayi zumbur zata mik'e Bashir ya rik'ota, "Haba sister ki bari mana, ki daina nuna su, me zaki mata idan kinje."?
"Ka barni Bashir, baka san na dad`e ban ganta ba, nayi shekara biyu rabon da na ganta."
Zata kuma mik'ewa ya kara rik'eta
"Plz ki bari yanzu ba fa kamar da bane, ki kyaleta kawai, babu lallai ma ta kulaki."
Nan ta hau mishi magana fad'a-fad'a kamar zatayi kuka, "Don't you know for how long nake nemanta amma kuma zaka hanani, kasan me nake ji araina.. I hate Wannan rayuwar da Jamila take, bazan iya dinga zuba ido ina gani ba..

Yasan halinta da saurin kuka, don haka, ya shiga rarrashinta, "I'm sorry aunty ba hanaki zuwa zanyi ba, amma ki jira ita tazo kinga da alama ma ta ganki, kuma tunanin da kike akanta yana da wuyar yuwuwa yanzu fa, ba,a iya chanja mutum lokaci d'aya. Bata ce mishi komai ba ta mik'e ~_"Ai idan da alkawari ba zata ga Jamila ta share ba, ko a wanne hali take ciki kuwa._~
Shima dole ya tashi, yawa sauran k'annen nashi alamar su biyo su kawai, ya musu nuni da su dakkowa Hafsah jakarta.

Jamila na hango, Hafsah, ta rabu da wanda take tare dashi tazo da gudu ta rungume ta, sun nuna jin dad`in ganin juna kafin, Jamila tace, Ai ina ganinki sometimes street haka ko wani waje, akwai distance tsakanin mu that's why bana miki magana.

Hafsah dai bata iya cewa komai ba, sai murmushi, kallon Jamila kawai, take, gaba-d`aya ta chanja, idan baka mata kyakykyawan sani ba ba zaka gane ta ba.

Jamila ta miko mata waya, lokacin su Ameera sun k'araso inda suke, ta daga musu hannu, ga mamakinsu duk sai da ta ambaci sunan su, "Ameera Zainab, Mufida, sannunku."

Ta kalli Bashir daya tsaya can gefe, bata mishi magana ba, shima kallon nata kawai yayi, ta mik'awa Hafsah wayarta samin phone dinki anan, munyi magana naga kina sauri nima ina sauri.
Hafsah tasa mata, ai kafin tau
k'ara kalma d'aya Jamila tabar wajen tana d'aga mata hannu.

Hafsah tayi ajiyar zuciya, zainab tace, "Yaya is she your friend Jamila."
Hafsah ta jinjina kai, ba zata iya magana ba.
"Chab." Ameera tace.

Mota suka shiga Basheer, yaja bai yiwa Hafsah maganar Jamila ba sam, Hafsah kam gaba d'aya yanayinta ya sauya ya koma damuwa, tsoron Allah ya k'ara shigarta, wai Jamila ce haka, babu ko mayafi, wacce a da bata iya yawo Inba da hijabi ba."? Kishin hakan ya cika zuciyarta, bai dace ta zuba ido tabar Jamila haka ba, ko ba komai ada ta amsa sunan k'awarta, ita gashi ta zama wani abu, amma Jamila fa, sam abinda take babu mai alfahri da ita.
Take ta sawa ranta zata yi iya kokarin ta wajen dawo da Jamila kan hanya, ita kanta tasan abin yana da matuk'ar wuya aiki ne ja, amma kamar jahadi ne, to kuma babban k'alubalen shine rashin sanin ta ina zata fara."?

Su Bashir nata hira ita kuwa tsit kake jinta, yana kallonta ta madubi, sai yaji ta bata mishi rai ma. _Duk wannan sauyawar da damuwar akan mutum d'aya, da babu alak'ar kusa ko ta nesa yanzu Tsakaninsu, matar da take yin abu bisa saninta, kuma da hankalin ta da ilimin ta."? Mene zaisa ta damu kanta, tunda ita maiyi d`in tana ganin daidai ne._

_________________
UKhasha tuk'i yake sosai, yayi watsi da tsokanar da su fadwa ke mishi, shakiyan ci ne kala kala, _Wai gaskiya yaya tunda Yaya Jabeer yayi aure kaima ya dace, kayi tunda dama ku biyu kuka rage._ Yayi burus dasu baice musu komai ba. Yanaji fadwa na bawa maryam labarin, _Bahijja_ da ke sune a baya. Sukayi shewa harda tafawa, ya juyo rai a had'e.
"Bana son shashanci, Allah zaku fita daga motar nan kuna min ihu a mota."

Haha.. Dariya suka mishi, ya juya kawai ya cigaba da tuk'inshi..

Wani Uturn suka zo daidai, lokacin Basheer shima ya taho dake mik'ewa zasuyi street su, shi kuma ya riga ya taho, Allah, ya kiyaye aka d'an bigi bayan motar tasu kawai. Dukkansu parking sukayi, kafin Bashir ya k'araso shi har yazo inda suke, _"Yi hakuri mai gida._ Abinda Basheer ya fara fad'a masa kenan, ya daga mishi hannu, _"Bakomai bakomai, muyi hakuri duka._ motar taku batayi komai ba."?

"Eh.. Inji Basheer "Hope kuma haka." "Babu koma, ka dinga kula kawai k'anina"!!

Karaf idanunsu suka had'u dana Hafsah. Yaji wani shock, Tabbas Itace.
Itama fad'uwar gaba taji, _kamar ta sanshi fa._

Bashir na shirin juyawa zai koma mota, _Dan Allah k'anina kaji mana._

Basheer ya dawo da mamaki.
"Me kace."?
"Um.. K'annen nan naka ka taimaka min da d'aya."
Bashir ya kalleshi da mamaki.
Me yake nufi kenan.?
Yayi k'asa da murya don yasan tambaya yake shirin yi mishi.
Kaga bamu da lokaci kana sauri ina sauri, taimaka min da number.

Bashir yayi jim, kafin yace okay.
Ya sa mishi number, yayi saving.
Ya mik'a wa Bashir hannu sukayi musabiha, "Nagode sosai abokina."
Bashir ya shiga mota, shi kuma ya k'arasa inda yayi parking, ya buda motar, gaba-d'aya yanayinshi ya sauya zuwa sanyi, akan idonshi suka wuce, da alama su ba wajen bikin zasu ba.

Yayi amanna Allah ne, ya dube shi ya k'ara had'a su. Su Fadwa sunyi mamakin sauyawar shi lokaci d'aya.

Basheer kuwa ya tafi yana mamaki, mutumin nada kyan mu,amala, shifa aka bugawa amma shine ya fito...

Mufeeda ta ji bazata iya shuru ba tace, Yaya naga kamar kunyi exchange numbers da wancan."
"Eh.."
Kawai yace mata, don bai son fad'ar dalili don baisan wa ya gani cikinsu ba, aranshi yaji yana fatan _Allah yasa Hafsah ce._

Da suka zo wucewa ma sai da ya d'aga wa Basheer hannu, sannan yaja tashi motar...

_Addu,a Kawai yake axuciyarshi Allah ya taimake shi akanta ta yarda dashi..._

📝
*HAJEEYA KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄 *46*
Chapter 53 · 0% Book details