← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 88

Sashe 64

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan suka cigaba da hirar su, sosai Yusuf ya saki jiki da ita, domin yana da saurin sabo da sakin jiki Indai ga mata ne.

Ya bata labarin yadda alak'ar su da Basma ta fara.
Cikin 'yan kwanaki suka k'ulla wata alak'a mai k'arfi da Haala, kuma ya tabbatar mata cewa zai zo Nigeria aranar asabar, kuma a ranar zai shigo kano komin dare.

_____________
Basma tasha tuntub'ar ta akan zancen, amma kullum Haala fad'a mata take babu matsala duk ranar daya dira kasar itama kawai ta dira gidansu kuma zata sanar mata da zarar yazo... Gefe guda abbanta yana ta mata tuni, ya fada mata. Nace iyayen Nurah su shirya don idan banga idon Yusuf ko iyayenshi ba ranar asabar toh Lahdi in sha Allah zasu zo su. Kada kice na miki badai-dai ba shiyasa nake baki dama. Ita dai komai ta mayar dashi ga hannun Haala tunda kullum cikin kwantar mata da hankali Haala take, amma abinda ke bata mamaki shine sau biyu Haala tazo gidansu, duk maganganun da suke yi a waya ne gashi gobe wa,adin abba zai cika.!!

📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*

[17/03, 2:37 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔

*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*

📄 *53*

*Yau* jin ta take gaba-d`aya kamar ba ita ba, komai tana yinshi ne cikin sanyi. Ba wai damuwa ce ta mata yawa ba, sai dai kawai fargabar bak'on da zatayi. Ta nemi dalilin damuwar itama ta rasa.
Ita ba bakin maza ne batayi ba, bare ace rashin sabo ne, takanyi bak'i idan ta kama saboda yanayin aikinta.

Sannan gefe guda tana son sanarwa mama batun zuwan bak'on shima taji ta kasa hakan. Hatta Basheer, ko Zainab ji tayi tana jin nauyin sanar musu bare kuma abba. Sai ta fara tuhumar kanta. _"Zuwan nashi zuwa ne fa na ziyara kawai, ba alak'ar soyayya ce tsakaninsu ba, idan ma zata bashi matsayi zata iya kiranshi da abokinta kawai.._
_To mene ya kawo jin nauyin da fargabar."?_

Wani b'angaren na zuciyarta yace, _"Saboda baki sanshi ba baki taba ganin shi ba.!!"_
Sai kawai ta yardarwa kanta wannan dalilin ne yasa.

Har kusan k'arfe uku da rabi tana d'aki a kwance. Mufida na ta kai kawo cikin d'akin, sai da ta tambaye ta ma, _"Aunty ko baki da lafiya ne."?_
Ta girgiza kai kawai.
Jin ana kiran sallar La,asar ne yasa dole ta tashi. Tuna cewa, _yace mata da yamma zai zo fah."?_

Sai da tayi wanka sannan tayi sallah lokacin zainab itama ta lek'o d'akin. Ta kirata.
"Zainab zo kiji."
Zainab ta shigo d'akin gaba-d`aya ta zauna kusa da ita, "gani meke faruwa."?
Ta girgiza kai, _"babu komai,_ sannan ta waro ido, don tambayar tasa ta tsargu. _"Me kika gani.?_ Ta tambaya.

Zainab ta girgiza kai.
"Babu komai gani nayi kin kirani."
"Okey Abba yana nan."?
Hafsah ta tambaya.
"Ya fita tun dazu."
"Basheer fa."?
Zainab tayi mata kallon mamaki sannan tace. "Ya sa kayan kwallo ya fita."
"Okey.."
"Bak'o zanyi neh!!

Ta fad'a a hankali tana kawar da kai.

Zainab ta saki murmushi, dama ta lura da yawan wayar da yayar tata keyi kwanakin nan.
Ta waro mata ido, "Really aunty."?
"Aa to mene kike mamaki don nace zanyi bak'o"?
Zainab ta kuma yin murmushi, "Babu komai, da yamman nan zaizo."?

"Eh, ni duk na kasa komai ma.!!
Ta fada tana k'arasa shafa mai a hannunta.
Zainab ta boye dariyarta. Sannan tace, "Meya sa toh aunty."?
Tana sane tayi mata tambayar.
"I don't really know, kawai bana son ya raina ni, so kuma na kasa komai."

"Kin tanadi kayan da zaki sa."? Inji zainab.
Duba Ki zab'o min.
Zainab ta mik'e ta shiga dubawa, har kayan cikin akwatu, itama tana son ta fito da yayar tata.

Daga k'arshe dai ta nemi mata, wata pink d`in atampha riga da skirt dinki stone work yayi kyau sai shek'i suke, ta ciro mayafi, da sark'a d'an-kunne zobe, agogo duka ta ajye mata.
"Kisa wannan aunty zaki yi kyau."
Ta kalli kayan ta tab'e baki, kawai ni yazo zai tashe ni tsaye wallahi.!!
Zainab tayi murmushi ta gimtse. Hafsah ta mik'e don saka kayan. Zainab Tayi saurin dakatar da ita da tambaya, "Aa yaya ba zaki shafa ko powder bane."?

"Ke kyale ni fa, ba wai kwalliya zanyi ba yana zuwa kuma zai tafi."

Zainab ta zaunar da ita bisa gado. "Please aunty Ki bari na shafa miki powder."
Bata mata musu ba, saidai ta had'e rai.

Zainab ta mata saasauk'ar kwalliyar powder, sai lining na kan ido, da mascara sai can janbaki. Nan da nan farar fuskarta ta d`auki haske da sheki tayi kyau matuk'a.
Tana mik'ewa da nufin saka kaya, kirashi ya shigo. Taji gabanta ya fad'i, kamar ta share sai kuma ta d'aga.

"Ranki ya dad'e na iso cikin unguwar fah."!!
Ta waro ido, ta kalli zainab.
Number nawa ne ma gidan. Baki fad`amin ba"?

Batayi magana ba sai ta turawa Zainab wayar.
Zainab ta rik'e, tasa a kunne, dai-dai lokacin yana cewa, "Kiyi hak'uri nasan na takura miki amma don Allah ki fad`amin."

"Hello." Zainab tace, sai yaji ba muryata ba. Cikin muryar tausayi yace, "Don Allah ina take me wayar, please kada kuyi min haka."

Cikin muryar shi zainab ta fahimci nutsuwa a tattare dashi, sai ya bata dariya da tausayi lokaci guda.

"Kana ina yanzu."
Ina unguwar da ta fad`amin.
Ina kenan."?
"Sallari tace koh."?
"Eh nan ne."
"House no. 35." Inji Zainab.
Thank you, in sha Allah gani nan."

"Amma please ina take."? Ya tambaya da damuwa.
"Bata kusa ne."
Kamar zai k'ara magana, sai kuma yace, "Okey thank you."

Zainab ta kalli, Hafsah, lokacin har ta gama sa kaya. A d`auki d'an kwali zata d'aura mata.
"Yaya ya kusa isowa."
Batace komai ba.
Zainab ta mata d'aurin, yayi kyau sosai.
"Kinyi kyau Yaya."
Ta fad'a tare da mik'a mata mudubi.

Hafsah ta kalli, madubin tayi kyau sosai. Tayi murmushi.
Zainab ta tambaye ta, "Yaya kin fadawa mama."?
Ta girgiza kai, Aa ai ba dad'ewa zaiyi ba kuma friend dina ne fah kawai.
"Hmm, Zainab tayi murmushi.
Sai kawai ta fice.

"Mama, aunty Hafsah wai bak'o zatayi."
"Waye zaizo."?
Nima ban sani ba, inaga wanda suke waya dashi ne.

Mama tayi murmushi, "Ai shikenan tunda bata gayamin ba."

Zainab tayi dariya itama.

"Idan kinga bata bashi ruwa ke ki kai mishi kinji." Inji mama.
"Toh, zainab tace ta juya ta nufi d'akin da Hafsah take.

Tana zaune jugum, wayarta na gefenta, wayar na ta fara k'ara, amma ko kallonta batayi ba, kafin Zainab tayi wani yunk'uri har wayar ta tsinke.

Ta kalli Hafsah daidai lokacin kuma, wani kiran na k'ara shigowa.
Yaya menene wai, kiranki ake fah."
Ta yatsina fuska. "Ki kyale ni kawai idan zaki d'aga ki d'aga amma fa kyar idan zan fita ma."

Zainab tayi mata wani kallon mamaki, tana so tayi magana amma bata son wayar ta k'ara katsewa ba,a d'aga ba, don haka da sauri ta mik'a hannu ta d'akko wayar, ta d'aga kiran.

"Hello."
Tace dashi.
Cikin murya mai cike da damuwa yace, _"Don Allah kibawa yayarki hakuri wallahi idan zuwana zai zamar mata damuwa, na fasa, zan juya kawai."_

Da sauri zainab tace, "Aa fah, tana wani abu ne. Kana ina ne."?
"Ina kofar gidan da kika fad`amin house no 35."
Okey please ka dan jira. Zainab ta fad'a.
"Okey thank you, amma please ki fad`amin gaskiya meyasa Hafsah taki amsa wayata, kinji, don Allah."

Hafsah ta gyara zama, tana jinsu, tunda wayar kamar hands-free take. Ita kanta batasan dalilin abinda takeyi ba, kawai ta tsinci kanta da rashin son hada id'o dashi.

Allah babu komai fah.
"Okey thank you."

Zainab ta ajjye wayar ta kalli Hafsah. "Don Allah Yaya ki daina kinga ke fa kika ce mishi yazo."

Hafsah tayi shuru, ta zubawa zainab ido kawai.

Zainab taja mayafinta zata fita.

"A kujerun waje zaki ce ya zauna."
Hafsah tayi mata magana.
Ta gyada kai ta fita kawai.

Tana bude gate ta hango bayan shi, yana tsaye daga gefen dama na gidan, ya juyawa hagu baya. Babu mota a wajen d`in mota bare ace da ita yazo.

Zainab ta dan matsa har zuwa kusa dashi sosai, sannan tayi mishi sallama.
Assalamu alaykum."
Ya juyo da murmushi a fuskar shi. "Wa alykum salam
Zainab zuciyarta tace, _Masha Allah, amma wannan aunty Hafsah take wa yanga. Mutum ne mai kwarjini da cika ido, ga kyau mai d'aukar hankali._

"Kaine bakon Yaya Hafsah koh."?

Ya d'aga mata kai.
"Okey, ka k'araso toh."
Tace dashi.
Yayi mata murmushi tayi gaba ya bita a baya, har suka iso farfajiyar wajen can gefe da kujeru a wajen da d'an table.

Zainab ta mishi nuni da kujerun sannan tace, "Ka zauna ga kujera nan, tana zuwa itama."
"Okey nagode, sannu kinji." Ya fad'a a shigen zuci.

Zainab ta k'ara kallon shi sannan ta shige gida.

Yaya Yaya, gaskiya mutumin ya hadu kinganshi kuwa, wallah Masha Allah, gashi da kwarjini da...
"Hmm, Hafsah ta katse ta."
"Don Allah Yaya ki tashi kije kinji."
Ta kalli Zainab, tana son fita, amma nauyi takeji, amma babu yadda zatayi.

Zainab ta d'auki jan jambakin data sa mata dazu zata k'ara mata, ta kauce.

No ki bari zainab haka ma ya isa.
Ta muk'e ta k'arasa jikin mudubi ta kalli kanta, tabbas tayi kyau.

Zainab ta duba ta dakko mata takalmi me sauk'in tudu, ta sanya.

"Zoki raka ni Zainab." Hafsah tace.
Noo Yaya, kije ke kad'ai, please."
"Aa nace kizo fa."
Please Yaya Allah kikaje ke kad'ai sai kinfi kwarjini a wajen shi.
Hmm, inji Hafsah, a zuciyarta tana cewa, _"an gaya miki so nake na burge shi."_

"Yayah.!!
Zainab ta kirata da k'aguwa.
Ta kalli Zainab ta mata alama da ido, _"mene."?_
"Kina wasting time Don Allah ki tafi kinga babu dad'i fah."

Dole ta bude k'ofa ta fita, gabanta nata fad'uwa.

Yana zaune, hankalinshi gaba-d`aya nakan, flowers (fulawowin) da sukayi wa farfajiyar gidan ado, don ya gaji da kai kallonshi hanyar fitowa daga cikin gidan.
Chapter 64 · 0% Book details