← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 88

Sashe 76

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya isa, kin fad'i magana, kuma, sako yazo, saboda haka zancen ya yasheni haka."

Abin mamaki kuma sai ga Hajiya Halima ta kasa, mayar da martani sai shuru da tayi kawai tana jiran taga mai Hajiya rabi zatayi, don taga ta dauki wayarta.

Cikin tunanin t tsinkayeta tana cewa cikin wayar, "Kazo palour ko me kake yi."
Bayan d'an shuru kuma taji, tace, cikin fada nace kazo koh, babu ruwana da me kake, ko aya kake idan ba zaka zo ba tom... "
Sai ta katse kiran.
Minti baifi daya ba, sai sukaji sallama, ta bayansu, basu waiga ba, shikuma shigowarshi kai tsaye gun mahaifiyar shi ya nufa, cike da jin kunya.
_Dama mama tasan da baki tasa ya fito a haka babu wata cikakkiyar riga."?_

_Ya fito daga wanka ne, yana shirin fita, yana sa kaya ta kira shi, yasa wando, baisa riga ba sai singlet._ Abinda yake fada mata a waya kenan Cewar, _kaya yake sawa._ amma sai ta nuna fushi.

_Ashe bak'i tayi take son su gaisa.??_ Shidai yayi mamakin dalilin mama na azalzala haka, ya dan dosanu gefen ta, cike da kunya, sai lokacin ya lura da su wa ke zaune a wajen.
Ciken da rudu, ya fara magana, "Ba Basma..!!??

Mamanshi ta daga mishi hannu.
Dakata.!!
Kasanta ne."?
"Ba bas, Basma ma cehh ma mama.!
Ya fada cikin in'ina.
Uwar ta jinjina kai, sannan ta mike tsaye shima ya mike, gabadaya ya rud'e.

Uwar ta nuna shi da yatsa sannan ta nuno Basma.
"Tabbatar mata ka fasa aurenta kaima."
Cike da rud'ewa ya hau rarraba ido kamar baya gani, tsakanin mamanshi da su Basma.

Uwar ta k'ara daga murya, sannan ta nuna Hajiya Halima da yatsa, Me kikace game da 'yarki. "?

Hajiya Halima ta mike tsaye. "Basai kin nuna ni da yatsa ba, cewa nayi ni da 'yata bama son auren nan idan akayi shi za,ayi b'atacciya.!!
Ta kalli, Basma ta k'ara cewa, ko kina so."?
Basma ta girgiza kai kamar d'azu.

Hajiya rabi ta kalli danta, cikin daga murya tace, zaka aureta ko ka fasa kaima"?
Nour ya zubowa Basma idanu, itama shi take kallo, yana k'ara kallonta, tanajin wani rauni yana shigar ta a hankali.

Ahankali shima ya bude baki yace, "Nima na janye, na fasa auren ki.!!
Yana fadar haka ya dauke idonshi daga kan Basma ya juya ya kalli mahaifiyar shi, kwalla fal idanun shi.
Hajiya Halima ta bude baki, "Ahto gaskiya kunyiwa kanku....

Dakata ke!!
Hajiya rabi ta fad'a da daga sauti sai da ta razana Basma, sannan tasa Hajiya Halima dakatawar babu shiri.

Hajiya rabi ta nuna su duka tare da cewa, tunda abinda ya kawo ku ya wuce, to ku bace daga gidannn kafin na gwada muku kalar nawa ikon, don ba ahaifi yar da akanta, za, ayi min dibar albarka ba. Idan kuma kuka k'ara koda minti cikin gidan nan to tabbas zaku gane inda kuka zo.!!!

Ta juya ga d'anta tana mishi wani kallo.
Jeka karasa shirinka kaji dana.
Nasan baka da damuwa koh.'?

Cike da dakiya ya kirkiro murmushi ya jinjina kai.

Abinda ya bawa Basma madaukakin mamaki kenan.

Ina tarin naci, da dumbin son da Nour ke mata.??

Har suka koma gida jikinta a sanyaye, ta kasa nutsuwa da abinda suka aikata ita da mamanta.

"Anya kuwa batayi abinda zai zame mata nadama ba."?
Wata zuciyar tace, _wacce iriyar nadama bayan kin rabu da alakakai."??_

_________________

Agidansu Nour kuwa, bayan fitar su Basma, Nour ya fada kan kujera, ya dafe kai, kuka yake shirin yi amma kukan ma yaki zuwa, yana mamakin abinda ya faru kamar a mafarki yanzun nan.
Ya sani bazai iya bawa mahaifiyar shi kunya ba, a yadda ta hak'ik'ance zai goyi bayanta, a lokacin da ake nuna mata iyakarta akanshi.

Itama Hajiya Rabi zama tayi kusa dashi, tana son ta bashi baki. "Kayi hakuri kaji Nour, ka d'auka komai kaddara ne, kada kaga agabansu nace ka fasa aurenta. Bani da iko akan aurenku haka suma, Allah shike kaddara komai Idan ya nufa sai Anyi ko basa so. Amma hakan bazai sa na bada damar su ci mana zarafi ba har cikin gida, saboda kana son 'yarta, kaima kayi taka tsantsan kaji, ka nemi zabin ubangiji, amma ka girmama kanka, kada ka wulakanta kanka inda baza,a taba ganinka da daraja ba, bayan Allah ya girmama ka ( _amatsayinka na dan adam._)

Zanyi maka addu,a kada ka damu kaji.. "? Zamuyi magana da abbanka, tashi kaje, kayi fitarka kaji, Allah ya zaba maka abinda yafi alkhairi.

"Da kyar ya ambata Amiin mama."
Ya tashi babu k'wari ya nufi d'akinshi, fitar da tasha ruwa kenan, don ya samu rauni matuka ajiki da kuma zuciyarshi.

Da daddare Abbansu Nour, na dawowa, Hajiya Rabi tayi mishi bayanin komai, sannan ta dora da nata ra,ayin.

_"Alhaji ina ganin tun da har abin ya zama haka, to gaskiya a hak'ura, tunda har suka magantu, kuma abin yakai ga anzo har gida to ina ganin Nour ya hak'ura Allah ya bashi wacce tafita, don idan har yarinya ta furta bata so to za,a sami rashin jituwa._

Alhaji ya jinjina kai jin duk bayananta, sannan ya bude baki, baya son ya nuna mata ra,ayinshi, a lokacin don haka yace, "Tom duk naji abinda kikace kiyi addu,a Allah yayi zab'in alkhairi, zan tuntubi shi Nour din da kuma mahaifin yarinyar."

Daga nan bai sake bata damar k'ara yin magana ba.

______________

Abban Basma yayi mama kin yadda ya dawo yaga Basma bata gidan. Aikuwa ya sauke fushin kan ya ya yayar Basma da ita kanta Hajiya salman, inda ya dora musu laifi duka. Sai da ya sassauto sannan ya fara binciken inda zai samo ta, sai ya fara da Halima.

Ya kirata a waya a fusace, itama tana ganin kiran ta share. Ya kara kira karo na biyu sai taga ma gwara ta daga suyi ta ta k'are.

"Hello ya akayi ne." Ta fada a fad'ace.
Halima ki dawo da Basma, don ba muyi dake zata zo wajenki ba."
Hmm, bazan dawo da ita ba da yake jaririya ce ita da zakace na dawo da ita.!!

Nace ki dawo da itan da waye yace ki zo ki dauke ta.
Tayi dariya au ni na d'auke ta ma koh."?
"Hmm, Alhaji Yunus yarinya fa ta girma sannan ba a kauye muke ba bare kayi mata auren dole tunda tace bata so to fa bazan zuba ido ayi ba. Sannan dawowa ba zata dawo ba.
Haka kika ce koh. "?
"Eh, haka nace.!!
Cikin fusata ya kira sunanta.
"Halima.!!
Ki shiga hankaliki dani wallahi ke kin isa ki hana ni iko akan 'yata."?
To bari kiji ko kinki ko kin so aure sai na aurar da Basma, sannan koma komawarta wajenki bazai sa na fasa daura mata aure ba, sai dai in bata numfashi.."!!
Hajiya Halima ta sheke da dariyar data bashi takaici. Take ya katse kiran tunaninshi ya kira Basma, sai ya tuna cewa ya kwace wayoyinta. Yayi jigum yana tunani tabbas akwai aiki gabanshi.

Wani abu daya bashi mamaki shine kiran Abbah Nour daya gani da daddare.
Da sauri ya daga yana fatan Allah yasa lafiya.
Suka gaisa cike da girmama juna. Kafin Abban Nour ya fara magana.

Am Alhaji dama inaso ne ka bani dama ko zuwa gobe ne ina so nazo na ganka.
Fargaba ta kama Abban Basma. Ya bude baki da sauri yana tambaya "lafiya dai Alhaji."?
Cikin murmurshi yake magana, "lafiya lau, ina so ne mu tattauna wata magana ne.
Da kyar Abban Basma ya kwantar da hankali sannan ya bawa abban Nour dama daya zo gobe su tattauna din.

Yammaci nayi Abban yayi sallama, a gidan su Basma. Abban Basma ya mishi iso a falon bak'in shi.

Ya tarbe shi da ruwa da abin sha. Sun gaisa sosai. Abban Basma yayi jugum cikin fargaba, yana fatan Allah yasa zancen kawo lefe ne ya kawo shi.

Alhaji mukhtar ya muskuta, sannan ya fara jawabi. Yayin da alhaji Alhaji Yunus ya bashi duka hankalin shi.

"Am Alhaji dama wata magana ce nazo da ita saboda maslaha, kuma naga ya dace muyi magana daga ni sai kai.

Ya danyi shuru, ya lura da dan tashin hankalin dake kan fuskar Alhaji Yunus. Sai kawai ya kauda kai ya cigaba da magana.

Wato wani al,amari ne ya faru jiya da maraice. Ita mai mai da dakinka da ita yarinyar da ake nema sun zo har gida sunyi magana kan cewa basa buk'atar wannan aure.!!

Sannan an tambayi yarinyar agaban ita mai dakinka shin tana bukatar auren tace bata so, sannan ta jaddada hakan agaban shi Nuran bayan mahaifiyar shi ta kira shi."
"Innalallahi wa in inna ilaihi raji,un."
Shi Alhaji Yunus yake ta maimaitawa, ji yake kamar yayi hawaye, wannan wane irin wulak'anci ne halima tayi wa yasan iya abinda taje tayi musu a gidan mutane."? Halima ta zubar masa da k'ima.

Ganin yanayin da ya shiga na tashin hankali yasa abban kokarin kwantar mishi da hankali,

To shine nace Alhaji kada azo ayi abu da son zuciya, ya dace a tsahirta a samu amincewar tasu tunda ita yarinya dai da ita za,a zauna, kuma auren nan fata muke ayi ya d'ore. Saboda haka shima yaron zan bashi dama idan ya iya shawo kanta toh, Allah ya tabbatar da alkhairi, zamu gani zuwa wasu lukuta ko ya kace alhaji."?

Abban Basma yasa Handkerchief din sa, ya goge gumin daya tsatstsafo masa.
Rauni sosai cikin muryarshi wanda zai yake nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki.
"Don Allah Alhaji kayi hakuri don manzon Allah wallahi ban san abin nan ya faru ba...!!

Alhaji Mukhtar ya dakatar dashi yana fad'in, "ashsha.. ashsha Alhaji ya da magiya haka."?
Wallahi maganar nan saboda maslahar yaran yasa nazo maka da ita ko kadan ni ban bata raina ba akai, don bana nan ma suka zo dake da safe ne. Kayi hakuri ka dauki komai a sannu, su sha'anin mata sai a hankali. Kada ka dawo Alhaji.
Chapter 76 · 0% Book details