← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 88

Sashe 37

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Katafaren* d'akin, taron 'Meena event center,' ya k'awatu sosai, an cika ana jiran shigowar ango da amarya da ango. 'Tana zaune a nasu table d'in.. Ita da sauran k'awayenta.. Babu jima wa ango da amarya suka shigo tare da rakiyar k'awaye da abokai..' 'Alokacin ne kuma biki ya kankama, aka fara lik'i da rawa." 'Tunda tazo wajen bataci komai ba.. tayi kyau cikin ankon bikin na atamfa da peace d'in head.' 'A can b'angaren abokan ango kuma.. rawa suke casa, kasancewar Mc, ya basu fagen.' 'Kana ganinsu kaga wayayyu maza ajin farko, sam basu da hayaniya, rawar ma ba wani yinta suke bilhak'k'i, ba. Sai kudad'e 'yan dubu dubu, da suke ta yin ruwan su.' 'Ahankali angon ya jawo wani daga cikin su, ya dafa kafad'ar shi, yai mishi rad'a a kunne, "Mene haka ne please ka saki ranka don Allah kada wannan abin ya b'ata maka rai.' 'Ya lumshe idonshi a hankali ya bud'e.' "Ok, but kasan dole ne fa abin ya dameni, matar nan fa taci mutunci na.' "Na sani amma ka share please kada ka damu kaji? Kaje ka zauna ka sami nutsuwa." "Ok. "Baya ya wuce yana duba 'sit' d'in da babu mutane sosai, amma ko ina da jama,a, gashi tsarin duk na mata da maza aka cakud'a a kowanne table ' 'Yaja siririn tsaki lokacin da ya isa daf da table d'in da Hafsa take, bai wani lura da su wanene akan table d'in ba, amma yasan dai matane su uku kawai.' "Tunda ya zauna ya dafe kanshi da hannunshi.' 'Sauran 'yan matan ne su biyu suka mik'e, don jin cewa, an buk'aci k'awayen amarya na school da su fito suma.' 'Itama Hafsa mik'ewa tayi ta bisu tana cewa, "Anisa, bari nima na biku, nayi lik'i. 'Sai da suka fara tafiya sannan ya d'ago kanshi.' 'Ya sauke ajiyar zuciya, yana kiran sunan Allah a zuciyarshi, a hankali ya fara jin nutsuwa na saukar mishi.' 'Sai lokacin ya tuna rabonshi da abinci tun safe, gashi yanzu har k'arfe shida saura kwata.' 'Hafsah tayi wa amarya lik'i tare da yi mata fatan alkhairi, sannan ta nemi da su Nabila su taho su koma wajen zamansu. 'Amma sukace mata ai su sai sun ca she.' 'Dama bikin wata 'yar ajinsu ne da suka yi degree tare da ita.' "No nidai gaskiya i can't dance cikin wad'annan gayyar mazan kawai ni na tafi, ku sameni acan.' "Alright" 'Inji Nabila tana tsokanarta ke kin fiya kunya wallahi.' 'Bata kula su ba ta wuce ta dawo wajen zamansu.' 'Tun da take takowa yake kallonta ita kuma sai taji kamar ta sauya waje saboda su kad'ai kenan zasu zauna a table d'in.' 'Zata wuce shi kenan taji yace a hankali, "Nop, ki zo wajenki ki zauna babu matsala." "A hankali batare da ta kalleshi ba ta zauna a kujera dama da shi amma tabar tazarar kujera d'aya a tsakaninsu.' "I hope ban tsare miki guri ba." 'Ya fad'a cikin taushin muryar da taji sanyin ta har cikin ranta.' "Ta girgiza mishi kai ahankali kawai." 'Su kayi shiru na d'an wani lokaci yayin da shi yake aikin kallonta.' "Ita kuma duk bata jin d'adin zaman wajen so take kawai ta tashi." 'Gashi karo na wajen uku kenan tana jin ringing d'in wayar shi amma a yadda ta lura ko kalla bai yi ba bare ya d'aga.' 'Wasu maza ta gani wajen su biyar cikin abokan ango sun nufo su.' 'Suna k'arasowa da'ya ya zagaya bayanshi ya dafa shi, sannan ya fara yi mishi magana.' "Please ukasha ka share abin nan don Allah, meye zaka sawa ranka damuwa.? Please feel free mana." 'Shiru shi dai baiyi magana ba.' "Daya daga cikin su ne yace " ka bari a gama harkar bikin nan, zata gane kuranta, amma ya zaka zauna wata mace tasa ka maka damuwa.." 'D'ayan ne yai dariya har da tafa hannaye, "Ku kuna abinku, yayi muku banza ba kuga shi hankalinshi ba ya wajenku ba, no wonder ma haushinku yakeji, yana tad'in shi kunzo kun dame shi.' "Ko ba haka ba ne UK"? 'Ya fad'a tare da dukar mishi baya.' "Murmushi yayi shi dai kawai." 'Ita dai Hafsah Allah Allah take dukan su su tashi subar mata wajen saboda gaba d'ayan su sun dameta, gata ita kad'aice mace duk mazaa sun zo sun baibaye ta.' 'Wanda tun da suka zo baiyi magana ba, shine ya kalleta yace, "Kinga please k'anwata ki dan miqo mishi wannan abincin ko zai ci." 'Tab, inji Hafsah acikin zuciyarta, a wanne dalilin zasu sata wani aiki kan wani mai ji da kanshi sai wani cika yake kamar ita ta mishi abinda akai mishi.' 'Ta kalli wanda yai mata maganar, sannan ta mik'e tare da cewa "Excuse me please" 'Ta rab'a ta gefensu ta, bar musu wajen.' 'Dukkansu suka bi bayanta da kallo har da shi d'in ma.' "Wanda yai mata maganar shi ya fara yin magana.' "Tab, lallai Yarinyar nan 'yar zafin kai ce, wato ba zatayi magana ba ma shine ta mik'e ta bar mana wajen kenan.?" "Muna da aurenmu, bare taja mana aji wannan UK ta, yarfa ai." 'D'ayan yace Allah yaso bani ta yarfa ba.' 'Da bazan iya ha'kuri ba wallahi.' 'Sai yanzu wanda suka taru danshi d'in yai magana, bayan yayi ajiyar zuciya, "To kada ka hak'ura d'in." 'Su rasa ma abinda za suyi mishi sukayi, sai kawai suka shek'e mishi da dariya.' 'Wanda ya mata magana, ya fara jawo hannunshi, "Wallahi sai ka taso kuwa mun tafi, duk hada hadar nan sai anyi dakai." "Mubarak ka barshi yasha ko da ruwa ne mana." 'Take ya girgiza kai shima, "No bazan iya sha ba.' 'Ya mik'e ya bisu, a hankali take fad'o mishi a cikin ranshi, sai ya dinga jin damuwar shi gaba d'aya ta gushe, sai ma damuwar, tafiyar da tayi, ke damun ranshi.' 'Babu laifi ya saki ranshi aka sha hidima sosai da shi, sai dai kuma tun da Hafsah tabar wajensu, har aka tashi bai k'ara ganinta ba, lamarin daya d'an tashi hankalinshi kenan.' 'Misalin k'arfe takwas kenan na na dare aka tashi daga gurin bikin, kai tsaye shi gida ya nufa, bai tsaya wani hada hadar d'iban mutane ba saboda kiran da Baffa yai mishi tun yamma, yace ko k'arfe nawa ne idan ya gama yazo yana nemanshi.' 'D'aya daga cikin drivers (Direbobi) na gidan ya kira a waya, yace yazo ya kaishi gadon k'aya.' 'Yasan ba zai nutsu yayi tuk'i ba, saboda fargarbar abinda baffan zai fad'a mishi.' 'Driver yana fito wa ya nufi motar ya bud'e mishi ya fito, sannan ya gaishe shi.. 'Ya koma gidan baya, yayin da drivern ya zauna a mazaunin driver ya bawa motar wuta.' 'Mintuna kad'an ya kaisu unguwar, inda sukayi parking a dai dai, k'ofar wani madaidaicin gida, driver ya fito ya bud'e mishi k'ofar sannan ya fito, ya fara takawa zuwa cikin gidan.' 'Kai tsaye sit room d'in gidan ya nufa don ya ganshi a bud'e.' 'Yai sallama aka amsa, sannan baffan yai mishi izini daya shigo.' 'Shida Hajiya ne a sit room d'in.' 'Cikin nutsuwa ya durk'usa ya gaida su, suka amsa tare da tambayar shi ya mutanen gidan.' 'Hajiyar ce ta mik'e ta nufi cikin gidan da dama ta sit room d'in zaka iya shigowa ko kuma ta k'ofar dake gefe.' 'Baffa ya kira sunanshi, "Ukashatu" Cikin ladabi ya amsa, "Na,am baffa"? Kasan dalilin kiran nan naka? 'Ya girgiza kai, "A,a baffa." 'Yad'anyi murmushi sannan, yace, to zancen mu ne dai dai da aka saba shi." 'Ukasha ya gyara zama, har wani zufa yaji ya keto mishi, baya son ayi mishi zancen nan, bayan kuma gashi yau gaba d'aya ma ranshi a b'ace yake.' 'Cikin tunanin shi yaji yo, Baffan na mishi magana babu alamun wasa a tattare da shi.' "Ya ake ciki to, kasan dai tun tini lokacin da muka baka ya cika koh"? "Ya gyad'a kai, nasani baffa." "To ya banji bayani ba har sai da na kirawo ka"? 'Ya muskuta, sannan ya fara magana , "Ai baffa ba,a samu ba ne.' . "Nan take baffan ya rufe shi da fad'a, "Wato ka maida mu abokan wasan ka koh?.. Ka d'auki zancen da wasa koh?? "Shikenan to yayi kyau abinda kayi, amma ka san bazamu zuba maka ido ba koh"? 'Tun da ya fara mishi fad'an ya sunkuyar da kanshi k'asa, sai da ya dire zancen shi sannan ya kwantar da murya yana bada hak'uri.' 'Ayi ha'kuri baffa, Allah ya huci zuciyarka, bani da burin in b'ata muku rai wallahi ayi hak'uri dai." 'Shima baffan sakkowa yayi, saboda wani tunani da yazo cikin zuciyarshi.' "Wato ya dace su mishi uzuri, basu san dalilinshi nayin hakan ba, ga kuma larura irin ta jinnu da dai sauransu.' 'Don haka yace, Ukashatu, ba muna matsa maka bane amma kasani aure shine cikar mutum, kuma, muna ganin ka kai munzalin da ya dace ace kaima kana da iyalinka, duba kaga shekarunka yanxu a k'alla sun kai talatin da shida, fa, to me kake jira, tunda kana da rufin asirinka, ka k'aninka ya gaji da jiranka har yana da 'yarshi? Ya k'ara sassauta murya, sannan yace, 'Kodai baka da lafiya ne, baka fad'a mana ba"? 'Abinda ya ba ukasha dariya kenan har yayi dariya mai sauti, sannan yayi saurin toshe bakin shi, tuna wa da yayi baffan ba abokin wasan shi ba ne.' 'Baffan ma murmusawa yayi, sannan yace cikin sigar yi mishi, wayo ko dan idan yana da larurar ma ya sanar da shi.' "Ka daina jin kunya, ko 'shi' yana nufin ('Abban ukashan') idan ka b'oye mishi ai ni bazaka b'oye min ba, kuma larura ai daga Allah take, wannan ba abu bane da zaka b'oyemana, sai ka fada mana koda a waya ne sai a nema maka magani koh"? "Amma asani na, da yadda sa,anninka na nan gidan ma suke fad'a ba,a tab'a jin kayi lissafin aure cikin sha,anin ka ba sam." 'Ya d'an gyara murya sannan yace, "Baffa in sha Allahu na kusa kawo muku ita, a dinga yi mana addu,a dai Allah ya taya mu zab'i na gari." "Ami'n, ami'n, inji kawu daya saki murmushin jin dad'in furucin, sannan ya d'ora da cewa, "Kuma kaima ka dage da addu,a saboda da akwai shed'anun aljanu masu cutar da d'an adam." "Hakane Baffa na gode sosai, Allah ya
Chapter 37 · 0% Book details