← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 88

Sashe 79

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaji dadin godiyar.
Don haka yace _you deserve more dear.!!_ taji dadi sosai sai dai kuma wannan kalma yana daga cikin kalaman da Yusuf ke fada mata.
Amma ji tayi kamar yau ne aka fara fada mata.

Zaki fita aiki koh."?
Ya tambaye ta.
"Eh."
Okey kada nasaki kiyi late koh."?
Tayi shuru sai agogo data kallah.
Okey ki shirya my dear sai kin dawo please ki kulamin da kanki."
"Okey u too tace mishi."
Thnk you Queen bye."
Sukayi sallama ya katse wayar yana murmurshi itama haka.

_______________________
Abban shi ya kirashi sannan ya nemi karin bayani akan zancen daga karshe ya bayyana mishi komai. Abban ya nuna jin dadin shi kafin ya zarce da kalu-balentar shi.
Yanzu idan auren nan tazo cikin gaggawa ina zaka zauna Ukhashatu."? Tun da saboda haka nake nuna maka kayi gininka amma kaki.
"Afwan Abba bansan abubuwan zasu zo min haka bane."

Babu komai ai haka al'amarin Allah yake sai ku zauna a gidajen nan na estate ko baka so."?
Ukhashatu cikin ladabi yace inaso Abba an gode Allah ya kara girma."

Amin ya Allah
inji khady.

Duk wani shiri anyi shi angama su Abba suka tsaida ranar zuwa.
A ranar Hafsah babu aiki amma sai ta wuce gidan auncle abdullah don suna dasawa da matar shi sosai tana da kirki. Hafsah bata san dalili ba amma taga mama ta nuna tana son taje can din yau, duk da ta zaci ko wani sakon mama zata bata amma bata bata komai ba banda sakon gaisuwa.

Su kansu su Zainab sunyi mamaki da suka ji wai neman auren yayarsu za,a zo.

To dai anyi komai cike da mutunta juna, su Abban Ukhashatu sunzo don har da Abban Ukhashan saboda matuk'ar son da yake Ukhashatu.

Basu tafi ba sai da suka cake kudin aure kimanin naira d'ubu d'ari.

Basu tsaida rana ba dai amma a yadda suka tattauna abin bazai wuce wata uku zuwa hudu ba saboda kada Abbah ya shiga harkar zabe.

Yau farin ciki na dabanne wajen Ukhashatu, abbanshi, hajiyarshi da kowa na gidansu, haka abban Hafsah da duk yan gidan banda Hafsah da bata san abinda akeyi ba.

Bayan shigowar abbah cikin gidan shida yan uwanshi su biyu; sunyi suka gabatar da kudin ga hajiya Amina _maman su Hafsah._
Tasa albarka sannan tayi addua. Bayan tafiyar yan uwan Abba, Abba ya gargadi su Amira kan kada su shaidawa Hafsah halin da ake ciki a waya su ta dawo shi da kanshi zai sanar mata.

Abban Ukhashatu sun tafi suna yabon karamci irin na su Alhaji Habeeb, adduar alkhairi kawai akewa juna.

Zuwa dare duk wanda bai san da zancen neman auren Ukhashatu ba a wanda da ya dace su sani to duk sunji labari sai fatan alkhairi ake kawai.

Ukhashatu jinshi yake kamar ango a ranar yayi godiya ga Allah babu adadi sannan yaji kwarin guiwar aiwatar da wasu abubuwa game da Hafsah wadanda ya dade yanaso ya aiwatar toh dama dama yake jira saboda kada aga ya zak'e ko ya wuce _makad'i da rawa._

Washe gari dai yayi niyyar fara bujuro mata da kudurin.

Ita kuwa bataji komai ba sai dai yawan faduwar gaba da ta dinga ji tana gidan auncle abdullah. Auncle yasan da zancen amma daya dawo baiyi wasu alamu da zasu nunawa Hafsah wani abu ya faru ba sai dai ya nemi data kwana tunda dare yayi mata kuma ta amince sannan ya shaidawa abbah cewa zata kwana.
Mamakinta a ranar sunyi waya da Ukhashatu har ta dinga mamakin yadda yake farin ciki sannan Kuma ya kirata da wani suna wai, _Amaryata!_

Bata kawo komai ba sai dai ta fuskanci cikin nishadi yake matuk'a kuma ranar motsi kadan taji yace, "Allah ya kai mu ranar aurenmu amaryata.!!
Ranar dai tasha ruwan kalamai da tarairaya.

Amma wani abin mamaki sai Washe gari daya kirata inda yayi mata wata magana da tasa ta fusata don aganinta bashi da hurumi akai..

Da safe ne misalin karfe 11:30pm.

Sun gama break ita da yan matar auncle da dansu guda daya Hamid ana ce mishi daddy sai yar da take goyo ita kuma sunan hajiya ne da ita wato kakar su Hafsah.

Tana kashinkid'e tana tunaninshi a lokacin. Abubuwa da dama take tunowa game dashi. Yanayinshi yadda yake nuna damuwa da ita sauk'in fushinshi, da kuma kirkin shi. Komai dai yayi yadda take so sai abinda ba'a rasa ba ma'ana a wani abin ya cika 100% wasu kuwa sai 90% ko 80% tunda dama duk d'an adam ance _tara yake bai cika goma ba._

Idan zata kasafta halayenshi da dab'inshi data fahimta da sauran mu'amala na yanayin shi da cikar d'an adam taka ta dorasu a mizanin burinta ( _akan irin mijin da take fata._) zata iya cewa Ukhashatu ya cika 89% cif cif. Tayi amanna zasu iya zama inuwa daya tunda baka taba samun mutum yadda kake so _hundred percent_ sai dai sauran tana kiyastawa da kuma fatan koda gaba azamansu tana iya tsintar cikon 15% d'in tunda bata gama tantancewa da kuma karanta komai nashi ba.
Tunda kana iya samun mutum da dabi'ar da baka mishi zato ba wacce zaka fi sonta fiye da wacca kake fata. Hafsah zata so Ukhashatu ya cike gurbin 15% d'inshi ya kara su a adadin _SOYAYYA DA KYAUTATAWA_ a gareta.

Ta lumshe ido saboda baccin safen da yake neman d'aukar ta.

Wayarta ta sata bude idon saboda k'arar da takeyi mara cika kunne sosai.
Ta dauki wayar tare da mishi sallama.
Ya amsa mata.
Sannan yace, I hope ba bacci kike na tasheki ba amarya.!!
Tayi murmurshi tare da sa hannu ta murje idanunta sannan tace "No ba bacci nake ba."
Okey sannu 'yan mata.
"Yawwa." Tace. Sannan ta tambaye shi.
Ya mum da sauran family.
"Mama na lafiya lau." Zan baki ita ku gaisa in sha Allah anjima da dare.
Tayi murmurshi sosai Okey thank you."
Suka d'anyi shuru sannan yace cikin nutsuwar murya da jan hankali.
My Hafs.!!
Na'am ita ma ta amsa tare ta tashi zaune gaba-d'aya.
Don Allah wata magana nake so muyi dake please ina so ki fahimce ni and ki bani amsa kinji."?
Ta danyi jim tana son ta hasaso wanne zance yake son yi mata haka."?
"Kinji please taji yace sannan ya dora da k'arin bayani."

Kada kice na miki shishshigi amma ina buk'atar neman karin bayani ne kan abin kiyi hakuri kinji."

Cikin k'aguwa tace "Okey fad'a min toh.
Promise ba zakiyi fushi ba.
Abin ya bata dariya to mene haka yake mata k'unbiya-k'unbiya."?
Tana dariya tace "Okey go ahead."

Ya saita murya sannan yace, am kwanaki na ganki da k'awarki ranar da nazo har kike ce min kun dade baku had'u ba please ina son sanin wane alak'ar k'awance ke tsakanin ku, kinsan before naga wata ma and itama kince min kun dade baku hadu ba for long. Please mene hadin ki dasu and meyasa kike ce min kun dade baku hadu ba."? Am sorry please tell me.!!

Hafsah tayi shuru, tana son tayi tunani kada tayi saurin fushi ko yanke hukunci saboda haka ta yanke hukunci gwara ta bashi amsa la'allah bayan jin amsar kalmomin shi da zasu biyo baya su bayyana mata dalilin tambayoyin nashi.
"Kinji."
Yace mata saboda gajiya da shurun da ita.
Ta danja numfashi kafin tace "Okey but nima inason sanin dalilin tambayoyinka akan su.
Da sauri yace in sha Allah zan fada miji please kedai ki bani amsa don Allah har sunan su inason ji."
"Hmm tace dashi sannan ta kara da cewa kodai kasan su neh."?
Noo wallahi bansan ko daya ba kawai inason in sani ne.. tunda kince kunyi shekaru bakwa had'uwa amma kuma gashi sunzo gidanku yanzu.
Hmm inji Hafsah sannan ta dora. "You mean baka yarda da abinda na fada maka bane koh."?
"Noo ba haka bane please ki fahimceni."
Tana so ta kama shi da hujja don haka ba bude baki tace. "Okey d'aya ta farkon Basma daya kuma jamila. And duk mun dade bamu hadu ba because dama makaranta ne ya hadamu da Basma and Jamila kuma na fada maka already bata nan so tazo garin nan ranar shine taxo mu gaisa."
Ta karasa tana sauke dogon numfashi na takaicin tambayoyin da kuma haushin doguwar maganar data biye mishi tayi.
Ukhashatu yayi murmurshi sannan yace, Okey nagode amma please kiyi hakuri idan tambayar ya bata miki rai.
Hmm tace mishi sannan tace "Nooo mene abin fishi."?
Yayi dan murmurshi "babu!!
Sannan ya sake bujuro da wata buk'atar cikin taushin murya.
Don Allah idan na roki wata alfarma zakiyi min."?
"Inajin ka." Tace da shi.
Please ki taimaka ki fahimce ni bada niyyar bata miki nazo miki da zancen nan ba kuma naso sai nazo mun tattauna amma na kasa"..Ya danyi shuru.
"Idan kin amince zanzo mu tsara yanda zaayi."
Cikin k'aguwa tace, "Okey menene fadamin toh."?
Ya dan gyara murya sannan ya fara duk da shima yana shakkar abinda zai fito daga bakin nashi.
"Alfarma guda biyu nake nema a wajenki na farko akan wadanan k'awayen naki please ki takaita mu'amalarki dasu badon ina zargin wani abu bane ko kuma nace kina kulasu sai dai am sorry to say zuciyata ta kasa aminta da yanayinsu bana son suna kulamin anaryata sosai."
Bai bata damar tayi magana ba ya dora zancen shi na biyu.

"Sannsn ki taimakeni don Allah badon ni ba..ki yarda ina kishinki Hafsah da zaki iya min wannan alfarmar ki ajiye aikin da kike yi idan yaso sai mu nemi wani..bana son ana nuna min ke duniya suna kallon ki please ki amince.!!!
Chapter 79 · 0% Book details