← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 88

Sashe 46

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Acan* wajen qarshen layinsu suka hango ta tana qoqarin tsare napep.
"Ki bita da sauri mana."
Mama ta fad'a da fad'a-fad'a.
"Gudu gudu, sauri sauri Fateema keyi tana, kwalawa Hafsah kira.
Ai kuwa ta jiyo kamar ana kiranta sai ta juyo.
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un.
Shine abinda Hafsah ta shiga furtawa ganin mama na nufo ta, yau ta kad'e, ina zata kai kunyar mama."?
Allah yaso Nazeer baya nan da yaya zatayi, da kunyar shi."??
Bata bi takan me napep d`in ba ta juyo, suka had'u da Fateema, ta riqe hannun Hafsah jikinta duk yayi sanyi.
Ina zaki je Hafsah."?
Bata da bakin magana sai jikin ta dake yin rawa, tsabar tsoro m, lallai tayi ganganci da rashin tunani.
Suna qarasowa daf da Mama, takaici yaja maman ta daga hannu ta wanke ta da mari.
"Yau na tabbatar da cewa baki da mutunci yarinyar nan, shiyasa Amiina take cewa, kina neman fin qarfinta.!!"
Ta talle qeyar ta, ta tusa su gaba ita da fateema wuce muje gida ki fad'a min gidan uban wa zaki tafi."
Dukkansu sauri suke kamar zasu tashi sama, sai gasu cikin abinda baifi minti d'aya ba har sun iso gidan.
Kiii, mama taja Hafsah sai d'akinta.
"Nema kike ki wulaqanta ni koh, shiyasa zaki fita bada izini na ba koh."?
"Kuka kawai Hafsah keyi kukan nadama, da Kukan rashi.
Ki rufe min baki ko in tattaka ki anan, kuma idan baki fad`amin inda kikayi niyyar zuwa ba, sai naci mutuncinki a gidan nan.
"Idan kuma don in maida ki gida, kikai min haka ina mai tabbatar miki babu inda zaki, idan nace kin dawo nan babu wanda zan hana ni hakan..."
Takaici ya tuqe mama ta dafe kunci tayi shuru.
Tabbas yarinyar ta bata mamaki, ya akayi ta zama haka ne, yarinyar da aka santa da nutsuwa da ladabi da biyayya, amma gaba-d`aya ta chanja.
Kaii idan ka biyewa yaran yanzu sai ka b'ige da hakan jini ko ciwon zuciya.
Shirun Maman, ya tsorata Hafsah, tabbas an kai ta bango, shiyasa ta rasa abin cewa.
Tsanar Basma ta nunku a zuciyar Hafsah ninkin ba ninkin.
_Ba don ita ba babu abinda zai dinga kawo mata sabani da iyayenta haka._
Tayi mata Allah ya isa tafi dubu zuciyarta. Take hawaye suka fara zarya a kuncinta.
Mama ta riqe haba da takaici, kafin ta miqe zumbur, ta kaiwa Hafsah wani mugun bugu da takaici, Allah yaso ta kauce.
"Ni banyi kuka ba sai ke."? Saboda kin raina ni, zaki dinga kuka.? Me nayi miki.."? Tsabar sharri koh, dama haka kike ban sani ba, dama haka kike yiwa Aminan..?
Gaskiya kin cuci kanki kam, baki yiwa kanki adalci ba..
Cikin kuka ta fara bada hak'uri "Don Allah mama kiyi haquri, don Allah.."
Wallahi bazan qara fita ba, kiyi hakuri na daina don Allah kiyi hak'uri.
"Hum, Haquri ai ke ya kama 'yannan, wacce irin rayuwa kike son ki fara,? Duk qoqarin da ake yi akanki bakya gani koh."?
"Wallahi bazan qara ba don Allah Mama kiyi hak'uri."
Ta rage sautin muryar ta, "To ina kika fita zaki je."?
Cikin shashsheqar kuka tace, gidansu qawata."
"Gidan su kawar ki."? Mama ta maimaita da sigar tambaya.
"To me zaki je yi."
Dif wuta ta d'aukewa Hafsah, sai jan majina da take yi.
"Ba tambayar ki nayi ba."
Shuru, ina ne gidan."?
"Gadon k'aya ne.!!
Hmm, ai kin koyi qarya kam, to ki sani ko zaki kwana kina rantsuwa na daina yadda da abinda zaki fad'a kuma dole ne ki fada min inda kika fita zaki je a yau d`innan, idan ba haka ba zan d`auki munanan matakai akanki, ciki harda sanarwa da Abbanki, abinda kikai."
Da sauri, Hafsah ta waro idanuwa, ita dai ta shiga uku, Yusuf da Basma na neman saka ta a bala'in da babu ranar fita daga cikin sa.
Cikin wasu zafafan hawaye ta durqusa bisa guiwowinta, abin gwanin tausayi, ta had'e hannayenta, tana rokon ta, "Don mama kiyi haquri kada ki fad'awa Abba, wallahi na rantse miki bazan sake ba, wallah bazan kuma yin irin haka ba."
Tausayi ta bawa Mama, don haka tace cikin had'e gira, idan haka ne toh ki fad`amin inda kika yi niyyar tafiya."
Wasu sabbin hawayen suka fara bin kuncinta banda nada, _"Indai zata labartawa mama inada tayi niyyar zuwa, yana nufin fa, sai ta fad'a mata tsakaninta da bamsa da yusuf, kuma dole hakan yakai ga sanin mama akan abinda idon Hafsan ya gane mata a gidan su Yusuf."_
Bazata iya ba.. Sam bazata iya fad'awa mama wannan zancen ba a matsayinta na yayar mahaifiyarta.
"Kinga koh.. Inba rashin gaskiya ba, me yake sakaki kuka idan aka kamaki da laifi irin wannan."
Maganar mama kenan wacce ta katsewa Hafsah tunani.
"Gi..gidan su qawata zanje wa walima."
"Walima kuma yaushe aka gayyace ki ban sani ba."?
Mama tayi mata zancen bawai don ta yarda da abinda ta fad'a d`in ba.
"Um.. tun ina gida ta kawo min katin.."
"Hmm.. Koh."? Inji mama tana tab'e baki.
Hafsah ta ja baki ta tsuke, tasan zancen bai karb'u ba sam.
"To ina ne wajen."?
"Gadon k'aya."
Hmm, saboda ban isa ba, ke kike iko da kanki shiyasa kika fice a sace koh."?
Bata da amsa illa shuru.

_"K`al!!_ mama tayi kwafa, ban yarda da wananna qaryar ba.
Ta nuna ta da yatsa, Tabbas sai kin fad`amin dalilin fitarki, kafin na d`auki mataki akanki. Sannan zaman gidan nan yanzu kika fara shi.
Maman ta dakata saboda kiran sallar magriba da aka fara yi, tana tuno yadda kusan kullum sai Amina (Maman Hafsah) ta kirata akan Hafsah, ta lura har yanzu hankalinta ya gaza kwanciya.
"Don Allah yaya ki taimaka ki saita yarinyar nan, wallah mahaifinta ma cikin damuwa yake, don ma kece shiyasa ya kwantar da hankali amma da babu yadda za,a ya barta taje wani waje a halin da ake ciki."
Ire-iren kalaman da take mata kenan kullum idan ta kirata.
"Kije kiyi sallah, sannan ki dawo nan bamu gama magana ba.
Ai kamar an sauke wa Hafsah wani abu mai nauyi daga kanta haka taji, ta gaji da wannan titsiyan na maman ya Nazeer, amma ko ma menene ita ta jawa kanta.
Tana shiga d'akin ta fad'a gado, minti kadan sai ga fateema daga toilet, tayo alwala. Ta d'an tsaya ta qareway Hafsah kallo kafin ta d`auki hijabi tasa ta tayar da sallah.
Hafsah kuwa kunyar Fateemah takeji, bata so tayiwa mahaifiyarta laifi irin wannan ba.
Sai da ta idar sannan ta hawo kan gadon, har lokacin Hafsah na kife, Akan cikin ta tayi rub-da-ciki, ta kwanta akan hannayenta ta rufe idanuwanta dasu, da alama kuka take.
Zama Fateema tayi sosai, akan gadon tana fuskantar Hafsah kafin ta fara magana, babu ruwanta da rashin d`agowar Hafsan don tana da yak'inin tana jinta.
"Hafsah, Allah ya gani badon wai cewa Mama mahaifiyata bace, kuma badon kinzo gidanmu bane zan fad'a miki haka, amma ke 'yar uwata ce, dole na fad'a miki gaskiya.. Tayi shuru, sannan ta cigaba.
_"Ban so kika yiwa Mama irin wannan laifin ba a yadda take daukar ki mai hankali.. Hafsah Ke ba yarinya bace, kuma ba ke kadai kike rayuwa ba, kina da 'yan uwa.. Meyasa idan kin shiga damuwa bazaki iya fad'a ba idan ba zaki iya fad'awa mama ba sai ki fad`amin in baki shawara, amma mene ne amfanin abinda kikayi."?
"Kin d'aukar min waya, kinyi kira, kuma kinki fad`amin wacce kika kira, sannan kina kuka na tambayeki dalili kinki fad`a, gashi yanzu kin yiwa mama laifi.. Ya kike so muyi miki.. Ko mune muke takura miki.."?
Fateema ta qarashe zancen da murya mai bayyana tsakanin damuwa.
Duk zancen da take, Hafsah bata d'ago ba, amma kuma tabbas zancen Fateema ya shige ta. Idan ba gaskiya zata k'i ba, to kuwa tabbas tasan gaskiyar kenan aka fad`ami mata.
Ta tsagaita da kukanta tana tuhumar kanta..
_Tun farkon da aka fara abin nan babu shawarar wanda ta nema, babu wanda ta sanarwa idan ba aysha ba, itama ta bata shawarar da tayi watsi da Yusuf d`in da Basmar duka, amma tak`i jin zancen ta, sai ita da kanta take yanke wa kanta hukunci._

Jin tayi shuru, kuma babu alamun zatayi magana yasa Fateema, ta kuma cewa, _"Na fad'a miki ne a matsayinki na 'yar uwata amma idan kinga magana ta ta b'ata miki rai toh Allah ya baki hak'uri."_ Tana gama fad'ar ta miqe zata tashi tabar kan gadon, a nufinta ma ta bar dakin gaba-d`aya, amma sai taji Hafsah ta riqo ta gam.
Ta miqe ta zauna itama, fuskarta jajir, cikin dashewar murya ta fara magana.
"Nagode, Fateema, nagode, kiyi haquri, da abinda na yiwa mamanki, na sani nayi mata badaidai ba, don Allah ki bata hak'uri... Hawaye suka fara bin kuncinta. Ta cigaba da magana, Fateema, abinda akayi min ne bazai fad'u ba a baki, bazan iya sake labarta shi ba, don, idan zan fad'a ji nake kamar a yanzu abin yake faruwa... Fateema anci amanata, ancuce ni, an yaudare ni, an raina min hankali.. Na amince anci amana ta, anyi min snatchin mafi muni..!!.Kuka yaci K'arfinta ta kifa, kanta akan cinyar fateema, yayin da Fateema tayi shuru, itama zuciyarta tayi rauni, kome akaiwa Hafsah to tabbas bashi da dad`in ji, tun da tayi haka.
Dukan bayanta ta shiga yi tana bata hak'uri, tana rarrashinta akan ta fad'a mata abinda akayi mata, in sha Allah zata bata mafita.
Da kyar, ta samu ta shawo kan Hafsah, har ta fara magana kamar haka: _"Fateemah wacce kika ga na kira qawata ce, tun a makarantar boko, da ita nake shawara akan komai, ita take bani shawara akan saurayi na, na yarda da ita sosai......_

_Nan Hafsah ta bawa fateema labarin komai tun daga farkon had'uwar ta da Yusuf, da irin shawararin da Basma ta dinga bata, da yadda Basman ta fara shigewa yusuf har zuwa birthday d`in Basma, da abinda Aysha D'aheer ta nuna mata a waya, zuwansu gidan su, yusuf, abinda suka gani da idonsu, har zuwa jiya da Hafsah ta kira basma a waya, kawo fitarta ta yau.._
Rashin sanin, abin cewa, da d'aurewar kai, yasa, fateema zubar hawaye, gaskiya abin ya tab'a zuciyarta..
Bubuga bayan Hafsah kawai take yi alamun rarrashi...
Chapter 46 · 0% Book details