← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 88

Sashe 32

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

k'ara rushewa da kuka, har da dukan 'pillow' saboda alhinin raina mata tunani da akayi.' 'Gaskiya sun raina tunaninta, takaicinta ajinta da aka zubar mata ranar birthday d'in Basma.' 'Ta tabbatar rabin 'yan class d'insu sun je, kuma an kira Yusuf da saurayinta, amma saboda su tabbatarwa da mutane sun rainata, kuma ita ba komai bace a wajen yusuf.'. Yasa suka yi hakan.. ' 'Tayi kuka har kanta ya fara ciwo, idanunta, sukayi jajir kamar an watsa mata barkono.' 'Har kiran sallar magariba bata fito ba, tana ta aikin kuka, amma babu shashsheka sai hawaye dake fitowa daga cikin idanunta, wand'a kana gani kasan tana cikin k'uncin zuciya, da taikaici.' 'Tana jiyo tafiyar hajiyah, amma ko lek'awa parlour bata yi ba.' 'Ta dai tashi tayi sallah sannan ta koma ta kwanta.' 'Mama kuma fushi take da ita, don haka ko lek'o ta batayi ba. 'Can kuma bangaren, mama tunani tayi kamar bata kyauta ba data hana abban hafsah dukan Hafsar, bai dace ta dinga katse mishi hanzarin ba, akan dukkan matakin daya ga ya dace ya d'auka akan Hafsar tun da ita ta gaza.' 'Ta saba tun da can bata dukan Hafsah, bare kuma yanzu da ta zama budurwa sosai.' 'Ba kuma, don hafsan tafi k'arfinta bane, sai don shi dukan bashi da amfani.'. 'Amma to ya ta iya, wani lokacin dole sai an had'a da dukan, musammaman yanzu da Hafsah ke neman 'bujirewa, ta kama wani layi na daban.' A tunin maman, 'Wanda zancen Abba da mutane yayi tasiri akanta har ta ke zargin wani mummunan abu ayau ga Hafsan wato fad'ar da ake na,👉🏻 'BA,A SHEDAR YARAN YANZU'.. B'angaren zuciyar mama na wassafo mata wani abu, wani b'angaren na k'okarin korewa.'.. 'Haka ta tilasta wa zuciyarta sai ta binciko gaskiyar zarginta. Hafsah ta gudu gidan Hajiyah tayi zance kuma ta tabbatar a d'akin uncle abdallah tayi zancen.' sanan ta fita da saurayi bada sanin kowa ba ranar biki, yau kuma ta fice yawonta (idan ma ita kad'ai d'in ta fita) batare da sanin kowa ba. 'Wanda dukka wad'annan halayen ba nata bane ada ba zata iya koda kwatanta yinsu ba, to Yanzu to 'Me TAKE SON ZAMA.'? 'Wai don ma mama bata ji halin da uncle abdallah ya gansu ba ranar.' 'Da akwai matsala inji Mama.' 'Iya k'arfin tunanin mama kenan..'😇👏🏼👌🏼#Hajeeyah Kareemerh.' 'Shiko Abba sai bayan anyi sallar magariba, sannan ya shigo gida.' 'D'akin shi ya wuce maman ta kai mishi abinci can, bai nuna mata komai ba ya saki jiki da ita har sukayi hira.' 'Bai sako mata zancen Hafsah ba sam, kuma tasan halinshi so yake ya barta tayi nata k'okarin, don haka tayi azamar chanja hirar tasu ta sako ta abinda yafi damunta ayanzu wato 'lamarin Hafsah.' "Am Abban Hafsah baka tambayeni ya mukayi da Hafsah taka ba."? 'Cikin rashin bawa zancenta muhimmanci yayi d'an murmushi mai sauti.' "Hmm to ai wannan ke da ita ne. "Me yayi wa Abba zafi,? 'Bake tayiwa laifi ba, kin barta jiran gida ta fice nata sabgar,? to ni me ye nawa kuma ciki."?? 'Nan da nan fuskar Mama ta sauya taji zafin kalamanshi fiye da tunani. 'Da bazata tanka ba sai kuma taga asarar hakan, don haka ta had'iye fushinta, tace,' "Idan tamin laifi ai kaima ai tayi maka, kuma ko ba haka ba ma ai kafi kowa iko da ita." "Hmm, ta yaya? Bayan gaki, kefa kika haifeta." "Haba Abban Hafsah don Allah ka daina fad'ar haka." "Hmm da Hakane Amina, ai da baki nuna min wai kada in tab'a miki 'ya ba koh'? 'Subhaanallah, wallahi ba haka bane, wallahi bada wani manufa bada manufa nayi hakan ba.' "Hmm to ai shikenan nima bacewa nayi wani abu ba. 'Ki mata abinda ya dace kawai." 'Yana fad'a ya mik'e don fita masallaci sallar isha'i.' 'Hankalin mama ya tashi, tayi da na sanin hakan data mishi, data bari ya d'auki mataki akanta, ita gani tayi dukan bai da anfani, kuma ta tsorata da dukan da yayi wa Hafsan kwanaki.' 'Shi abinda kake tunanin zaiyi fushi akai to, ba,a kanshi yake fushin ba.' 'Yanzu ya zatayi idan ya zare hannun shi daga kan Hafsah'??😳 😀 'Mama kenan'!👍🏻 'To shima abba, a b'angaren shi, ba wai cire, hannun nashi zai yi ba.' 'To idan yayi haka mekenan yayi, ai kanshi yayiwa.' 'Dole ne ya sa ido akanta ko dan hak'k'insu akanshi yake, bare kuma yafi sonta akan dukan 'ya'yanshi.' 'Kawai ya kyale mama ne, don kuma da gaske abinda ta mishi ya b'ata ranshi sosai.' 'Amma shima da akwai nashi tunanin akan matakin daya dace kan Hafsah.' 'Koda aka idar da sallah bai nemi hanyar gida ba, ya jima yana addu,a kan Allah ya taimake shi akan tarbiyyar Hafsah, 'Don yasan addu,ar ita ce komai bawai wani k'okarinshi ko fad'anshi ba..' 'Yasani tarbiyya da akwai wuya amma, kuma yasan yayi iya kokarinshi, sai kuma yanzu da wani keson wargaza mishi komai.' 'Shi dake tuninshi daban da na mama, yayi amanna tabbas 'Soyyaya' ce ke dawainiya da Hafsah har bata tsoron fushinsu yanzu, ya lura tanayin duk abinda zai zamar mata maslaha ne ga soyayyar ta ko menene kuwa zai biyo baya.' 'Shi abba ba takaicinsa bane soyayyar data fad'a, a,a abinda yake b'ata mishi rai shine kalar yaron data nacewa.' 'Ya tabbatar ba na nunawa bane in banda haka meyasa ya kirashi, yak'i zuwa.'? 'Amma yanzu ya zamar mishi wajibi ya nemi yaron koda a waya ne, don maslahar shi.' 'Saboda haka yasa a ranshi gobe zai kira shi..' 'Da wannan tunanin ya kamo hanyar gida.' 'A gidan kuma, yaran ne suka dami mama bayan ta fito daga d'akin Abba, 'Wai ina yaya.'? 'Nace muku tana d'aki meye zaku dameni.'? "Mama bata da lafiya ne..?" 'Inji Mufida. "Ban sani ba, kije ki duba mana." 'Cewar mama cikin fushi.' 'Mufida ta mik'e ta nufi d'akin Hafsar.' 'Tana kwance sai juyi take.' Bayan ciwon kan daya addabeta yanxu kuma ciwon mara take fama.' 'Ga kuma uwa uba ciwon da aka haddasa mata cikin zuciyarta.' "Yaya, Yaya, wai baki da lafiya ne? 'Ta d'ago jajayen idanunta, ahankali ta bud'e baki murya a dashe saboda kuka tace, "Eh Mufida, bani da lafiya." "Kaii, amma baki fad'awa mama ba.? Bari inje to in fad'a mata. 'Tana yunk'urin ce mata a,a, amma ina, ai tuni ta fice.' 'Daidai sanda ta dawo falo lokacin Abba ya shigo yaji tana cewa.' "Mama Mama yaya bata da lafiya kuka take tayi ma." 'Mama ta d'an rud'e ta tabbatar kenan tun la,asar Hafsah keyin kukan nan, idan kuwa haka ne, to da akwai babbar matsala tabbas akwai abin da ya faru da Hafsan ayau d'innan kuma ta tabbatar mummunan abu ne, sai zarginta ya k'ara samun wuri.' 'Bata nuna damuwarta afili ba, ta dai mik'e ta nufi d'akin.' 'Abba ya jinjina kai sannan ya bita.' 'A kwance ta sameta sai juyi takeyi.' 'Maman tazauna, a gefen gado, ta tab'a k'afarta, abinda yasa Hafsah ta d'ago da idanunta, ahankali tace bani da lafiya.' "To meya yake damunki"? 'Sai da tayi jinkiri, sannan tace, "Ciwon kai, kuma marata ciwo take." 'Mama tayi azamar k'ara yi mata tambaya, kana ji kasan a rud'e take matuk'a, kuma tana cikin tsoron faruwar wani abu.' "Ke.. ke Haf..sah dazu ina kika je ehe.? 'Wani abu da Mama bata sani, ba shine da zarar tayi wa Hafsah tambayar 'inda taje, tana k'ara tuno mata da abinda ya faru ne.' sai taji bazata iya fad'a musu ba, kuma bazata iya rik'e kukanka ba.' 'Ta, rantse idonta don wani irin suka da taji zuciyarta nayi.' 'Wai shin Gaske ne yau taje gidan tayi Yusuf, har taga wannan mummunan al,amari.'? 'Tsawar mama ta firgitata da tace, bazaki fad'i gidan uban da kika je ba koh, cikin raunin murya tace, mama dubiya muka je.." "K'arya kike.. Zaki fad'amin gurin wanda kika je idan na tattaka ki anan." 'Dam gaban Hafsah ya fad'i, har rawa jikinta ya fara yi, ka da dai mama tasan inda sukaje.' 'Muryar Abba taji da yake tsaye abakin k'ofa, yana cewa "Meye haka Amina, wacce magana kike yi ne ehe"? "Yarinya bata da lafiya kina wani tuhumar ta da wani zancenki."? 'Ya juya kan Hafsah "Ke tashi maza, zaki iya tashi koh"? "Ta gyad'a kai." To tashi ki shiga toilet kiyi wanka, kisa ruwan 'Heater' dayawa kinji? Idan kin shirya kizo ki sameni.' 'Ahankali ta d'aga mishi kai.' Gaskiya taji dad'in abinda Abba yayi yanzu.' 'Ahankali ta mik'e tana bin bango saboda dad'ewa da tayi a kwance har jiri takeji.' 'Mama ta daka mata tsawa, "Zakiyi tafiya daidai, ki daina bin bango ko sai na ci ubanki!"? 'Babu shiri ta dawo kan doka da oda, inda ita kuma mama ta k'ura mata ido.'😅😄😄 🤔 To wai me Maman ke nufi ne.'???😒 'Ruwa mai zafi ta had'a, tayi wanka dashi, tanayi tana hawaye, wanda sun ma k'afe sai rad'ad'i cikin zuciyarta.' 'Ga takaicin abinda mama take mata, sai taga wannan karon tafi Abba ma d'aukar zafi.' 'To meye dalili?? 'Wata zuciyar tace, "Hafsah kina jawo mata magana ne da yawa..! 'Da tayi wankan taji dad'in jikinta sosai, kuma taji, zuciyarta ta rage k'una, sai ajiyar zuciya da take ta faman yi.' 'Ta tarar da Abba a falonshi, yana zaune kan kujera. Zata zauna a k'asa yace ta tashi, ta zauna a kujera itama, sanan tace Abba gani.' 'Memakon ya amsa mata sai yace mata, "Kin ci abinci"? "Ta girgiza kai." Ya nuna mata tray da mama ta shiryo mishi abincin daya ci d'azu, gashi nan ki zuba kishi kinji.' 'Ta, gyad'a kai' 'Madaidaici ta zuba sannan, ta fara ci ahankali, abba na kallon 'television' jefi jefi yana kallonta. "Kici fa abincin nan sosai." "To" 'Ta fad'a.' Taci fiye da rabin abinci ta sha ruwa, sai ya nuna mata apple da aka yanka akan wani k'aramin 'plate' ta, d'auki guda d'aya ta fara ci." 'Gaskiya taji dad'in jikinta, cikin abinda suka addabeta har da yunwa.' "Kin fad'a wa maman naki inda kika je."? Tambayar da Abba yai mata kenan babu wasa a fuskanshi.' 'Ta d'aga mishi kai, "Eh" 'To fad'amin' "Dubiya muka je ni da k'awata" "Ina kenan." "A asibiti aka kwantar da ita." "To ya sunan asibitin a ina yake"? 'Tayi d'if, to fa anzo wajen' Sai da yace "Uhum"? 'Sannan ta samu tace, um bansan.. Au na manta
Chapter 32 · 0% Book details