Sashe 57
Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
♥️♥️♥️♥️ *ZAZZAFAN SO* (masoyin k'warai) *Cigaban littafin Zazzafan so* *(Guba ne)* 💔💔 *By:* *Karima Tijjani Mansur* *(Hajeeyah khareemerh )* *Dedicated to Unique in your love heart group members.* 📄 *48- 49* *Yaune,* suke yinin, Fateemah, sun kacame, a wajen biki, ana ta rawa... Bikin na matuk'ar dad'i a gurinsu, sun had'u duka 'yan matan, har da matar Nazeer ma, anata rawa, da yake, yinin iya mata ne babu mazaa, ko ango bai halarci wajen ba. Adaidai wannan lokacin kuma Ukhasha nata kiran number Hafsah tana ringing amma ba,a d'aga ba. Da ya kira karo na uku, sai ya hak'ura kawai. Yayi shuru ya zuba wa _number_ ido, tunani yake kodai, ya hak'ura ne."? Sai kuma yayi wani tunani. _"A yadda take, kuma tana irin wannan aiki a media, dole baza,a rasa, masu damunta da kiraye-kiraye haka ba. Saboda haka zai jinkirta zuwa wani lokaci kawai._ Zai cigaba da addu,a idan da alkhairi akan abin, Allah ya sauk'ak'a mishi samunta. Wani tunani mara dad'i ya d'arsu aranshi. _Yanzu idan an riga an bada ita fah?_ _"a,uzubillah_ Ya fada a fili, bai ma san ya zai kwatanta halin damuwar da zai shiga ba idan haka ta faru.. Da Wannan tunanin kuma ya shiga wani tunani, na daban, wata zuciyar ta karanta mishi. _To ita yarinyar mutane da kabar ta da damuwa akanka, ya zakayi da ita.. Ko kana ganin zaka samu yadda kake so, alhanin kana da alhakin wata akanka."?_ A hankali ya furta, _"Allah ya gani bana sonta, bazan iya zama da ita ba._ _To ka sama mata mafita, tunda kana kokarin kulla taka soyayyar a wani waje._ Wata zuciyar ta fad'a mishi haka. To wacce irin mafita, menene mafitar."? Ya tambayi kanshi. Kamar an tsikare shi ya jawo wayarshi, ya danna kiranta. Cike da farin ciki ta d'auka. Tayi mishi sallama, ya amsa cikin sakin fuska. Tana mamakin sauyawar shi, cikin kwanakin nan. "Bahijja!! Ya kira sunanta. Na,am. Ta amsa ad`an sanyaye don tana tsoron abinda zai fito daga bakin shi. _Sau dayawa indai zaiyi mata magana mara dad'i yafi bata hankalin shi, da kuma jawo hankalinta._ Yaushene ma kika ce min zaki cika _twenty years.?_ Farin-ciki ya mamaye ta. _Kodai party zai had'a mata ne."? Sai kuma ta tuna irin gidansu, sannan ta tuna data gayyace shi partyn graduation, yace mata baya zuwa party._ Tana son jin abinda zai fad'a mata don haka tace, "Nan da _three months._ "Okey.." yace mata kawai. Tayi shuru tana son taji k'arin bayani. _Wato ma ko 20yrs yarinyar bata cika ba. Ya fada a zuciyarshi. Baya son ta shiga damuwa a k'ananun shekarunta. Tabbas ma yaga tsaurin ido da k'ok'arin yarinyar, da har ta iya furta mishi tana sonshi, ashekarun haihuwa fa zai iya bata goma sha uku fa. Sai kuma ya tuna _shekaru ba sune abun dubawa ba indai da so._ "Meya faru neh Dear."? Tambayeshi, jin yayi shuru babu k'arin bayani. Babu komai, kawai na tambayeki ne. Ta danyi jim, kafin tace, _"Okey"_ "Yaushe zaku fara lecture, a makaranta."? Ya tambayeta. Nan da _2weeks_ fah. Tana jin dad`i a ranta, yana janta da hira. "Ina mamanki."? "Tana nata room." Ta fada da mamakin tambayar kodai wani abu ya k'ara faruwa neh. Kafin ta samu damar magana, ya saita muryar shi, cikin nutsuwa ya fara magana yace. "In tambayeki Bahijja ."? Ta danyi shuru kafin tace, "Um." "Please ki fahimci tambayata kada ki _getting dina wrong."_ Cikin sanyin jiki tace, "Toh inaji." Kasan zuciyarta na tsoron abinda zai fito daga bakinshi. Meyasa, da maman ki ta nuna bata son mu,amularki dani baki d`auki mataki ba.?? Tayi d'if don bata da amsa. "Uhum."? Ya sake ce da ita. "Me ta k'ara yi maka ne,?_was something wrong happened again.?_ Ta tambayeshi da damuwa. "No, no no, kawai naga ta damu akan abin ne, kuma nima nayi tunani to this time ya dace ace muyi mata biyayya, mamanki ce tana da hak'k'i akanki, kuma zata fiki sanin what's right for you." Ya fad'o maganar kai tsaye. Ai kawai sai ya fara jiyo shashshek'ar kukanta. "Why all this dear, kawai kace abinda mama ta maka ne, ba zaka iya d'auka ba, but since when muke tare da kai and you knew that mama bata so kuma bakayimin wannan tuhumar ba sai yanzu." Ahankali yace, _"Calm down plz, ki daina kuka mana._ Sukayi shuru kafin yace, _ Bahijja Kinsan girman iyaye kuwa.."?_ _Kinsan girman da Allah ya basu.? Mamanki nada hak'k'i akanki, duk abinda bata sa mishi albarka ba cikin rayuwarki bazai yi miki amfani ba yadda kike so. Ina son muyi magana da ke, amma ki cire aranki don cewa abinda tayi min ne yake damuna, wallah is not, kawai naga time yayi da za,ace kin mata biyayya, ke ba yarinya bace, please mu hak'ura da wannan alak'ar, mu chanja mata suna, ki dawo k'anwata zaifi mana dad'i kuma mamanki zata fi amsar hakan pleasse!!_ Kamar ya bata sakon mutuwa, haka kalaman nashi suka shige ta fiye da koyaushe da yake fad'a mata irinsu, a muryarshi ta fahimci da gaske yake ya gama shirin tsinke zaren alak'arsu. Sai ta fashe mishi da kuka mai tsuma rai, shi kanshi sai da ya cire wayar daga kunnenshi sannan ya mayar. Zuciyar shi ce ta karanta mishi, _"Ukhashatu idan fa tausayinta zaka tsaya, sam ba zaku je inda kake son aje ba._ _Cikin dakewa yace, "Ki daina kuka, ke banda abinki mene abin kuka cikin wannan maganar, ni da ke fa bamu muke da ikon kanmu ba, kiyi tunani, akan abinda nake hango mana, alak'ar yaya da k'anwa ita tafi dacewa damu fiye da wacce muke yanzu."_ Ta saki ajiyar zuciya, "Me nayi maka laifin me nayi maka."? "Ya salam, Bahijja, me kwa kika min, me zaki yi min, me yasa kike tunanin kinyi min wani abu."? Cikin bacin rai ta tace, " Eh mana, saboda naga gaba-d`aya ka nuna ka gaji dani, baka son cigaba da kulani koh, wai baka ganin irin son.." Sai ta k'ara saka kuka, tana tausayin kanta, _wai mene haka ne, wane irin soyayya aka jarabce ta dashi."?_ Kiyi hak'uri kinji, ina sama mana maslaha ne ni da ke, bama son gaba ki zargeni." A fusace ta cafe zancen, _Idan kayi aure ba."? Saboda ni baka buk'atata cikin rayuwarka, baka sona._ Yayi shuru, yana juya zancen, kuma fa, hakane, zancenta baya son ta zarge shi, ranar da zata wayi gari an d'aura mishi aure. Amma yanayin maganar ta bashi mamaki, hakika bata cikin hayyaci da har ta iya fada' mishi magana da irin wannan sigar, da babu _respect._ "Bansan me zance miki ba Bahijja, amma kin san halin da ake ciki, ina fad'a miki ba ba tun yau ba, Abba na yayi min zab'i!! Babu shiri ta dawo da kukanta. _Kenan zancenta na kan hanya aure zaiyi._ Don girman Allah, kiyi hak'uri kiyi addu,a, Allah ya had'aki da mafi alkhairin zab'i cikin rayuwarki, ki daina kukan nan, ni ba ce miki nayi mu rabu ba fa, na sama mana mafita ne, kuma na miki alk'awari zan zame miki Yayan da xakiyi alfahri da shi kiyi hak'uri kinji.!! Abinda ya shiga fada mata kenan, don ya rasa, abin cewar komai daya tanada don ya furta mata ya fad'eshi, yasani rabuwarsu ba zata zo da sauki yadda yake so ba. "Nagode, Nagode, abinda tace mishi kenan. Ta katse waya. Yayi jim yana tunani, gwara taje tayi tunani, don bashi da wani abin k'ara mata akai, ya tabbatar idan ta nutsu zata sakko kuma yayi kudirin bazai k'ara nemanta ba, gwara ta fara koyar rayuwar da babu shi. Amma bari ya k'ara da tura mata sakon waya yana so ne ta yarda da abinda yake zuwa mata dashi ta laluma, kafin ya janye jiki, ta k'arfi idan yaga abin ya faskara. _Wallahi ban tab'a sawa raina zan wulak'anta mai so na ba.. Bahijja ban san ya zanyi ki fahimce ni ba, amma ki d'auka wannan shine maslaha agaremu, kiyi hakuri kiyi tunani akan maganata._ Iya abinda ya iya rubuta mata kenan. Ta duba sakon, tayi shuru tana tunanin abubuwan daya ce, da kuma abinda zaifi zamar mata mafita.. _______________ Tazarar kwanaki biyu ya bawa Hafsah, bai k'ara kiran number d`in ba sai ranar litinin. Haka ma, Bahijja tun ranar bata k'ara kiran shi ba, hakan ya masa dad'i, _gwara ta saba,_ amma a k'asan zuciyarshi akwai tausayinta fal. *HAFSAH* _______________ Tana kwance, tana hutawa, ta gajiyar bikin da suka sha, a yammacin ranar litinin. Danna wayarta take, tana k'ara kallon photonan da sukayi. Kira ya shigo cikin wayar da wata number, ta d'aga ta kara a kunnenta. *UKHASHA* ______________ Ba k'aramin farinciki yaji ba, ganin an d'aga kiran nashi, ga seconds har sun fara tafiya. "Assalamu alaykum." Ya fad'a cikin nutsuwar murya. Muryar ta shiga cikin jikinta sosai. "Wa alykm salam." Ta amsa da k'aramin sauti. "Barkanki da yamma, ina fata kin yini lafiya." Damuwarta shine taji da wa take magana, amma babu yadda zatayi dole ta amsa gaisuwar shi. "Lafiya lau Alhamdulillah." Tayi saurin tambaya. "Am sorry ban gane me magana ba." "Okey hakane." kai tsaye yace. "Sunana _Ukhashatu Abubakar_ Tayi shuru tana son ta tuno ko tasan me irin sunan. Bai barta da wannan ba sai ya k'ara mata da, "Ina magana da Hafsah ne koh."? Ahankali tace "Eh itace. Sai dai banajin ni Hafsan kake nema." Muryarta tayi mishi dad'i don haka ya kashingid'a, sannan yayi murmushi me sauti. "Me yasa kika ce haka."? Mamakon ta amsa, sai tace cikin k'osawa. "Kafad'a min wanene kai yadda zan gane inaga zaifi koh"? "Ayi hak'uri toh, amma na fad'a miki sunana. "Bansanka ba ai." Ta fad'a kai tsaye. Ya k'ara tattara nutsuwar shi. "Naga kin gaji dani bari na miki bayani." "Hmm.." tace mishi, kuma kamar yasan hakan ne. (Muryarshi tafi komai jan hankalin ta.) "Sunana Ukhashatu, kiyi hak'uri na kiraki bada izininki ba." Yad'an dakata, yayin da ita kuma ta bada dukkan nutsuwar ta gareshi. Bazan boye miki ba, samun number ki ba abu ne mai sauki ba, _i witnessed that._ "Kiyi hak'uri naga babu hanyar da zan iya miki magana ne idan ba ta wayarki ba." Tayi shuru don babu abin cewa. "Na rok'i abani number ki ne sai kuma nayi dace aka bani. Waye ya baka."? kiyi hak'uri zanyi miki bayani gaba. "To