← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 88

Sashe 52

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban abinda yafi b'ata mishi rai shine, mahaifinshi da aka ambata. Meye dalili..? Shi baice yarinyar dameshi ba da irin bak'in nacinta sai shi wai za,a ce ya asirce ta.? Allah ya sawwak'e, ai ko asiri yake bazai yiwa wannan 'yar ta ta ba, yarinyar da bai tab'a ji kalarta ko wani abu ya nata ya burge shi ba sam.
_Wai lalata.!_ shi ake cewa zaiyi lalata da wata yarinya..? Akan me zata yi masa wannan sharrin.. Ta taba ganinshi k'ofar gidanta."? Kawai tsabar sharri irin na mata, don 'yarta ta nace mishi tana son ta rabata dashi sai ta fake dayi masa sharri, ai kuwa idan haka ne dole ya d`auki mataki akai, duk nacin yarinyar sai ta daina kulashi ko bata so, sai dai in ta mutu, tun da abin ya na neman yazo da sharri..

Gyangyad'i yake tayi saboda gajiya, sai ya mik'e kawai ya kwanta, bai bi takan wayar ba ma, ranshi a b'ace, _amma yarinyar akwai k'arfin hali da naci.._
Shi banda bazai iya ba, ai shine yake da abin cewa, badon ba halin shi bane cin fuska, da babu abinda zai hana shi mayar mata da munanan kalamanta kan 'yarta.
_"Ai yarta ce mayya, ita ce ke bibiyarshi, ga mugun naci sam bata da zuciya._
Amma da ke bazai iya ba wayar kawai ya katse ya kyaleta.

Har ya fara bacci ya tuna gwara ya kashe wayar, idan ba haka ba, zata iya cigaba da damunshi da kira don zata aikata. Gefe kad'an na zuciyashi, yana tausaya mata, bai tab'a ganin inda ake irin abinda yarinyar ke mishi ba, wani _"Makahon so"_ take mishi. Yayi imanin idan yace ta kyale mahaifiyarta tsaf zata barta!!
Ya nemi tsarin Allah daga fad'awa irin wannan son.

Yadda ya d'auka shine, su mutanen yanzu, ka so su tsa ka-tsaki shine maslaha, don yana da tarihi na soyayya kala-kala musamman a cikin abokansa, wad`anda suka _ZAFAFA_, k'arshe suka k'are a asibiti.

Yana mamakin kansa, bai tab'a jin ya kwana da wata arai ya tashi da ita, ya ku ma kwana ba, sai dai wani lokacin ya kan b'ata lokaci akan tunanin _Bahijja_ shima ba wai begenta ba, a,a kullum cikin tunanin yadda za,ayi su rabu salin alin yake, ba tare da ta zargeshi da b'ata mata lokaci ko kuma k'inta ba. Amma duk wasu hanyoyi ya gwada basuyi amfani ba, ya sha fad'a mata, tayi hakuri tayi aure, shi a gida za,a bashi mata amma tak'i sai dai ta ji shi kawai, har fada' mishi take, _"Taji, ta amince ya auri uku ya cikashe ta hud'u da ita wallahi zata yarda.!!_

*HAFSAH*
______________
Misalin k'arfe sha d'aya da rabi na, safe, sun gama karyawa, dake kuma _weekend_ ne babu makaranta, kowa ya kama abinda zai fishshe shi. Gidan tsaf yake an share babu datti, sai k'amshi kawai ke tashi.

A parlour Hafsah ce zaune bisa kujera three seater, ta dora _Laptop computer_ akan hannun kujerar. Sanye take da riga da skirt na atampha, wanda suka d'an kamata, babu d'an kwali akanta. Gashinta wanda dama can bai cika ci ka ba, sai dai tsaho ta tufke shi da ribbon, farar fatar ta sai shek'i take, babu alamun kwalliya a fuskar ta, idan ka kalleta zaka ga babu abinda ya sauya daga ita idan har ka santa ashekarun baya, komai cikin nutsuwa take yi kuma a hankali babu gaggawa. Kana kallonta zaga ga alamun hutu da wayewa atattare da ita, ba mamaki kuma ka k'i yarda cewa Bashir k'aninta ne, saboda yanayin jikinta bata da girma sam, sai dai matsakaicin tsaho.

Da Sallama Abba ya shigo palourn daga d'akin mam. Hafsah ta amsa tare da rankwafawa tana gaida shi, _Abba Barka da safiya."_
Ya kalleta sosai, "Sannu Yaya, bakya son saka d'an kwali koh..?"
Ta danyi murmushi tana shafa gashinta da ke ta shek'i, ta kalli gefe da gefe kamar zata ga dankwalin a wajen.

Har yanzu yana kallonta. "Baki bi su zainab d`in kitson ba ke."?

Cikin nutsuwa tace, "Eh abba ba ba sai nayi kitson ba, ai nayi _saloon."_
(Duk shirye shiryen bikin Fateema suke k'anwar Ya Nazeer )
Yayi kyau, "Ki saka d'an kwali toh."
Ta mik'e zata wuce d'akin.
"Nima zan fita wani meeting ne."
"To Abba a dawo lafiya."
"Allah yasa Yaya."

Zai fita kenan Bashir ya shigo, ya zube har k'asa "Barka da asuba."
Abba yayi dariya "Asuba ko rana."?
"Ko dan ku baku son tashi da wuri koh."?

Ya fara tafiya Bashir na binshi a baya.
"Ya kuke fama da baccin nan a makarantar kuwa."?
Basheer ya sosa kai, "Ai Abba hakura ake."
"To da kyau ai."
Cikin ladabi yace "Abba fita zaa yi ne."?
"Eh zanje wani meeting ne, kasan an kusa yin _primary election_.
"To bari na raka ka Abba."
Abba yayi murmushin jin dad'i "Yawwa, _amma dai ka sa hula koh."?_

Ya kalli jikinshi riga ce _long sleeves_ da dogon wandon _Jeans._

Yayi murmushi, sannan da sauri ya wuce cikin gida, duk da d'akinshi kafin a shiga ciki ne, yana shigowa palourn, Hafsah na fitowa daga d'akinta, tana d`aura d'ankwali.
"Gud morning sister of mine.!
"Morning _Junior_ "
( _Haka ta dawo kiranshi._)
Tana tahowa shi kuma ya tsaya, bata gama k'arasowa ba yace, "Anjima da yamma zamuje park idan na dawo, yanzu zamu fita da Abbah ne."
"Okey tace mishi."
"Ina mama, kice mata mun fita da Abba."
Ya fad'a cikin sauri, sannan ya juya. D'akinshi ya bud'e ya d'akko hular ya kifa akanshi, yana murmushi, yasan da Hafsah zata gani babu abinda zai hana tayi ta mishi dariya.
Murmushinshi ya k'ara fad'ad'a yana son yayarshi yana son farin-cikinta.

"Haha, kufa yaran yanzu kwalliyar ku da ban ce!"
Cewar Abba sanda Bashir ya k'araso inda yake.
Ya bud'ewa Abba d'aya gefen, sannan shima ya shiga mazaunin _driver._
Don ance ka sako hula, sai ka sako ita kad'ai..? "Ai ana nufin ka sako kayan da ake sawa hula."
Ya k'arashe maganar yana dariya.
Bashir ya sosa, k'eya, "Ai kada na bata lokaci ne shiyasa."
"Hakan ma yayi, ai naga haka kuke yi yanzu, _asa kayan bature, a d'ora hular bahaushe!!."_
"Kuna kwaikwayon rappers kuke ce musu ne ko hip -pop"
"Bashir yayi dariya, kawai."
"To yayi, _bridged_ muka nufa, nan za,ayi taron.
Abba ya fad'a sanda Bashir ya tada mota.
Mai gad'i ya bude musu gate, suka fita, suna tafiya suna hira irin ta d'a da mahaifi.

__________________

Shiri suke, sosai duk sun baza kayan kwalliya a d'akin, mai yi musu kwalliyar fuskarta ko powder babu, Fadwa kenan, take wa su Maryam da Zainab kwalliya, kasancewar ta iya kwalliyar zamani. ( _makeup artist ce ita_)
Shirin zuwa partyn Abokin Yayansu Ukhasha suke wato Jabeer (JB). Shima Ukhasha yana d'akinshi yana shiryawa.
Zainab ce da ake shafawa powder tace, "Yaya Fadwa muyi sauri fa kinga, kada Yaya yayi ta jiranmu..Kinsan halinshi zai iya tafiya ya barmu."
Bata tsaya da abinda take yi ba tace, "Kedai ki tsaya kiyi kyau kawai, yanzu k'arfe nawa ne ma kwata-kwata"?

Sai da ta gama mata tsaf tayi mata d'auri, dama ta gamawa maryam. Ta d`auki mudubi kenan zata fara da fuskar ta, wayarta tayi k'ara, maryam tayi saurin kai hannu ta d'auka, Fadwa ta miko hannu, maryam tayi gefe da wayar tana cewa, "Don Allah kiyi sauri Yaya ne fa bari na d'aga."
Hello..
"Ina ta jiranku fah."
"Mun kusa gamawa Yaya."
"Hmm, kada ku batan lokaci don Allah, me ita Dadwan keyi sarkin k'ak'ale-k'ak'ale."
"Yaya ta gama, d'aura dan kwali take."
"Please Kice tayi sauri kunga sai kirana suke."
"Tom."
Ya katse wayar don jin kira ya shigo a zaton shi ango ne.

Sai kuma yaga Bahijja, kamar bazai d'aga ba sai kuma ya tuna wani abu.
Bai bata damar magana ba yace, "Kinga zan fita ne, idan na dawo zamuyi magana."
Ya katse kiran, sannan ya k'arasa d'aura takalmin shi, ya mik'e ya nufi mudubi dake manne jikin bango, k'asan shi anyi wata 'yar kanta mai kyau, kayan shafe shafe ne na maza, da sauransu akai. Babu wasu tarkace dama a d'akin, drawer ce me biyu wacce ta cika da kaya, sai akwatuna, suma kayan ne dai aciki, sai abin d'ora takalma, sai madaidaicin gadonshi, gefe da gefen shi da _bed side drawer_ ya dora mata littafai aciki da wajenta.

Ya kalli kanshi sosai a madubin, sannan yasa hannu ya gyara zaman hularshi yayi kyau matuk'a cikin _Brown shadda_ da sukayi ankonta, bai da kiba sam, sannan ba dogo ne irin sosai ba, yana layin tsakiya dai, fatar shi ba fara bace tas, amma tana da haske sosai, yana da saje a fuskar shi, haka dukkan jikinshi akwai gashi, amma basu cika cika ko tsayi sosai ba.
Akwai shi da kwarjini idan ka kalleshi, bashi da yawan magana barkatai musamman inda bai da sanayya ko sabo da mutanen gurin, amma yana
da hira harda zolaya indai ka mishi farin sani. Bai bata lokaci sosai wajen tsayawa kallon kanshi ba, ya fesa turaruka masu sanyin k'amshi, sannan ya fito, daga d'akin kawai.

Lokacin suma k'annen nashi sun gama shiryawa, sunyi kyau sosai, cikin shigar _blue black lace_, mayafansu mayalwata, baza,a ce sun fito da tsaraici ba. Sai kuma suka b'ige da zaman d'aukar photo.

_Wani abu game da Khady Abubakar shine, baya hana 'ya'yanshi mata zuwa biki, ko wani taro, indai har ya yarda da tsaftar mutanen, sai dai dole zasuyi shiga ta mutunci, wacce dama kullum cikinta suke, sannan ba,za,a barsu su tafi su kad'ai ba, sai dole ke da 'yar uwarki ko yayanki ko k'aninki. Sannan basa sakewa su haura k'arfe takwas na dare.

_Aganishi ka hana yarinya mace zuwa taron biki, kamar shiga hak'k'i ne da kuma bada k'ofar shigowar b'araka, don a yadda yaran yanzu suke muhimmanta biki, to idan ka hanasu dole su nemi hanya ko da bada saninka ba, har gwara ma a fita da saninka, kuma matuk'ar ka tarbiyyantar dasu yadda ya dace, babu abinda zasu yi na zubar da mutunci ko makamancin haka._

Yanzu haka ma sai da ukhasha ya nemi izini a wajenshi, sannan da k'yar ya yarda.

"Ku idan zakuyi biki kuyi iya ku mazaa, mana, amma kun hada har da mata."?

Ya sosa k'eya, "Akaramakallahu, ai na matan ne, gayytar mu sukayi.
Chapter 52 · 0% Book details