Sashe 38
Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
k'ara girma." Ami'n, baffa ya fad'a yana mik'a mishi hannu alamar suyi 'musabaha' (Abisa al,adar kawun idan zasu yi bankwana da koda jinkansa ne.') 'Ukasha ya mik'a hannu sukayi musabiha, sannan ya mik'e.' "To na barka lafiya baffa." "Masha Allah, a gaida mutanen gidan, Allah yai muku albarka." "Ami'n baffa ya fito yana, ajiyar zuciya, don yaga alamun sassauci a b'angaren K'anin mahaifin nasashi.' 'Ya nufi gate, ya tarar da driver ya d'an kwanta cikin motar yana jiran shi.' 'Yana ganinshi yayi saurin fitowa zai bud'e mishi gidan baya.' Ya dakatar da shi, "A,a ka gaba zan zauna ina son zamuyi hira ne.' 'Driver yayi murmushin jin dad'in hakan, duk da suna gaisuwar mutunci amma yayi mamakin cewa hira da Ukasha yace zaiyi da shi, saboda yasan shi ba ma,abocin yawan magana ba ne da yawa, amma sam ba,za,a ce yana da wulak'anci ba saboda halin gidansu gaba d'aya na karamci ne, domin sun gaji girma da karamci.' 'Ya bud'e mishi gaban, sannan ya zagayo, shima ya zauna ya kunna motar sannan suka hau bisa titi.' 'Sai da suka fara tafiya sannan ya kalle driver yace, "Malam najib, ina son tambayarka ne, amma don Allah ka Fad'amin gaskiya." "To in sha Allahu, mai gida zan fad'a maka iya abinda na sani." "Yawwa to, am nasan dai ak'alla zan baka shekaru kamar hud'u, amma ina son sanin wani abu ne tun da kai kana da aure, kuma, yanzu 'ya'yanka biyu kace koh."? 'Ya gyad'a kai, "Hakane mai gida, yanzu na uku ake shirin haifowa." "Yai murmushi, Masha Allah." 'Sannan ya saita muryarshi, "Aganinka me yasa su baffa suka takura min da sai nayi aure."? 'Najib driver yayi dariya sannan yace, Ai mai gida, bama sai an tambaya ba ka isa munzali tun yaushe, kuma, tunda ba wani abu ake jira na shiri ba (Kud'i) ai ya dace dai ace zuwa yanzu an mallaki iyali. Sannan hankalinsu zaifi kwanciya idan har kana da auren" "Wane irin kwanciyar hankali kuma"? "Najib yai 'yar dariya, sannan yace a zuciyarshi, "Bari na bi dashi ta yadda zai fi fahimta." 'Don ya fahimci, ba wai ukasha ya damu da auren bane, idan ya fahimta ma shi zancen ma baso yake ana yi mishi shi ba.' 'Sai ya kada baki yace, "Mai gida, sai kawai ayi hak'uri tun da manya sun nuna suna so sai a yi k'okari ko don biyayya.' 'Sannan shi aure yana sa a dinga ganin k'imar mutum ta musammaman.' 'Ya kalleshi, "To yanzu idan na fahimta wata tawaya ce kenan saboda bani da aure koh."? "A,a mai gida, kawai shi aure yana cika darajar mutum ne." "Yai murmushi, sannan ya gimtse, sannan yace, "Bana son wulak'anci ne irin na mata." "Alhaji ai ba kalar ku ake wukak'antawa ba gaskiya.' "Hmm, haka kace, amma kada in maka shishshigi da sai ince, tsakaninka da Allah matar ka bata maka wulak'anci."? "Kasan ni shine abinda na tsana a gurin mace." 'Ya fad'a yana yatsina fuska.' "Eh to, wallahi mai gida batayi gata da sanin yakamata, ga tsafta, sai dai kawai kasan mata ba,a rabasu da jan aji wani lokacin." "Yai murmushi sannan ya jingina jikin kujerar motar, 'Jin daga an tab'o matar shi ya fara zuba.' "Ahankali yace Allah sarki, tunda haka ne, in sha Allah nima zanyi k'okari ko dan farin cikin su Abba.' 'Driver ya ce "Toh Allah ya zab'a ta gari, mai gida." "Ami'n" 'Dai dai lokacin sunzo wajen wani store mai kyau, yayi mishi alamar da yayi parking a wajen.' 'Sai da suka tsaya, sannan ya kalle shi, "Muje kad'an sama mata kayan gayu, madam d'in taka tunda kace 'yar gayu ce, sai ka had'a harda na jaririn koh? " 'Driver ya hau fara,a "Godiya nake alhaji." "Tare suka shiga, kantin.' 'Kaya ake siyar wa na madaidaitan kud'i, amma sai kyau." B'angaren atamfofi ya zab'ar mata uku masu kyau, amma ya mishi alamar daya k'ara, ya dad'a guda biyu saboda kada ya zak'e da yawa, babu abinda bai sashi ya d'aukar mata ba tun daga kan mayafai takalma, sark'oki da turare, da sauransu.' 'Sai kuma kayan Baby, sai takalman yara da yace ya d'aukarwa ya'yan nashi.' 'Shidai Najib har kasa godiya yayi, yasan kawai Allah ne yayi mishi katari, ayau d'in, don yana shirin fitowa ya nufi gida, Ukashan ya kirashi, kira yake kawai, "Allah ya k'ara arziki, yasa a gama lafiya, Allah ya k'arawa alhaji nisan kwana." "Ami'n yake cewa shi dai, 'Ya mik'a katinshi aka zara wajen dubu abba'in da wani abin.' abinka da kud'in yanzu ba wuya kiji sun taru akan k'aramar siyayya bare kuma siyayya irin wannan.' 'Sai da suka fito yace mishi, to adinga taya mu da addu,a muma, Allah ya bamu nagari." "Ami'n Ami'n, mai gida addu,a dama kullum muna saka ku a cikinta." "Sun isa gida, ya sauke shi, sannan ya deb'e kayan shi ya nufi gida cike da jin dad'in yadda matarshi zatayi farin ciki da kayan, saboda yana yabonta sosai.' "Ukasha kuwa, yana shiga cikin gidan yaji wata masifaffiyar yunwa, nan ya tuna rabonshi da abinci tun safe, lokaci guda kuma ya tuno da wannan Yarinyar ta d'azu a wajen biki, take yaji wata mummunar fad'uwar gaba, daya tuna bai ma san yaushe tabar wajen ba." "A shagwaba irin tashi ne, ya nufi d'akin k'anwarshi yana buga mata k'ofa, saboda sanyi ne duk sunyi bacci, shiyasa ma bai nufi d'akin hajiyar tashi ba. "Ita kam Fadwa, yasan ba bacci take ba, fadwa please ki fito mana.' "Ta ajye wayar ta gefe, sannan ta mik'e ta zare key sanan ta fito, "Kinyi bacci ne? "No, ta girgiza kai." Ok plz ki had'amin abinda zan iya ci yanzu yunwa nakeji kinji." "Ta gyad'a kai kawai, saboda tasan halin yayan nata da rigima bama tasan me zata dafa mishi ba, kuma may be idan ta tambayeshi yace ya fasa, ko ya zaci ya takura mata ne.' "Ta nufi kitchen, ta duba taga da miya sai kawai ta, d'ora d'an ruwa ta dafa mishi taliya, sannan ta zuba ruwan tea madaidaici tasa mishi kayan k'amshi, ta juye a plask, amma saboda ta tsokane shi sai ta d'auki iya abincin kawai, ta nufi d'akin shi dashi.' 'Ta tarar ya idar da sallah, ta ajye mishi tana cewa bross, gashi toh." 'Ya d'aga mata hannu alamar godiya, sannan bayan ya shafa addu,ar ya kalleta, "To ina coffee d'in kuma."? "Tayi murmushi, kamar yace ta mishi da coffee, sai kawai tace, "Ai bakace min da coffee ba." "Yazanyi in iya cin abinci babu coffee kin sani, amma shine zaki k'i had'a min"? "To bari in samo maka." "No ki barshi ai kinsan ina so, baki had'o min dashi ba, so kije ki huta kawai thank you, kinji." 'Tayi murmushi, wai shi dole sai ya nuna mata baiyi fushi ba kenan, bayan tasan wannan zai iya zama sanadin k'in cin abincin nashi ma gaba d'aya.' 'Zata yabeshi bashi da matsala a komai, amma a b'angaren nan, sai matarshi ta fahimce shi, idan ba haka ba zasu dinga samun matsala, saboda, shi mutum ne dayake son kawai ki fahimci abubuwan da yake so, da wanda baya so, idan ya nuna miki al,adar shice yin abu to ki rik'e ba sai kullum ya maimaita miki ba.' saboda bashi da son yawan maimaita abu.' 'Shiyasa take mishi fatan ya samu mace, mai lura sosai, saboda banda wannan bashi da wata matsala shi dai.' "Am yaya na fa had'a maka d'akko maka kawai zanyi.' 'Ya jawo hannunta sannan ya rankwasheta, "Kin maidani abokin wasanki koh,? saboda muna level da'ya ni da ke koh"? yana nufin,👇🏼 (Duk basu da aure) "Ougsh,! Yaya da zafi." Ya sake ta, "Maza hurry up ki d'akko min yunwa nakeji"." "Ok bros, tayi saurin kawo mishi had'e da cup da d'an plate ak'asan cup d'in.' "Thank you, sai da safe, kuma, gobe ki fad'a ma su Maryam zaku je dinner d'in bikin nan, coz yana min k'orafin baku je yau yau ba.' "Okey yaya saura kai, dama ku biyu kuka rage" Ta fad'a tana Mik'ewa zata gudu.' 'Ya jefa mata key d'in shi, ta fita tana mishi dariya.' 'Ahankali yake dan shan tea d'in, sai yaji gaba d'aya ya manta da damuwarshi ta d'azu, sai kuma wata sabuwa tunanin yarinyar nan dake damun zuciyar shi, abin ya fara damunshi dak'yar ya iya cin abincin kad'an, duk kuma fargarbar yadda zasu k'ara had'uwa yake.'.. 'Abin ya dinga bashi mamaki, sai yake tunanin kodai yarfa sun da tayi ne, yake jin haushin hakan"? 'To ai kuma shi baiji ko da d'igon haushin ta ba cikin ranshi, hasalima wani abu yake ji na mussamman game da ita, ji yake kamar ya mik'e ya tafi nemanta.' 'Ya dafe kanshi yana tunanin wannan wane sabon abu ne ke shirin samunshi..?? 👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼