← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 88

Sashe 81

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ta kuma tuhumar kanta kan rashin tsayawa tayi mishi jawabi yadda ya dace ma'ana ta fada mishi gaskiya gashi ta jawo akan k'awance da babu shi a yanxu (musamman ga Basma.) ta shiga matsala.

Har bayan magriba bata samu matsaya mai sunan mafita ba.
Sai kuma tana kwance taji kira a wayarta. Gabanta ya fadi da taga shine.
A sanyaye ta daga.
Tana dagawar ya mata sallama tare da cewa, ina kofar gidanku don Allah ki fito kinji."

Tayi jimm ko motsawa batayi ba.
Ya zatayi ta iya kallon shi a yau dai."? Bayan haka tana fargabar abinda zai fada mata ta idan sun hadun.

Sai ta tuna bai kashe wayarba kuma jiran cewar ta yake yi.
A hankali tace "Okey"
Tana tararrabin yadda zata fita tunda ta tabbatar kin fitarta hakan zai tabbatar mishi cewa tana kan bakar ta ne.!!...

📝
HAJEEYAH KHAREMERH

*Wannan shine page na biyun karshe.*👏🏻👏🏻

♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔

*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄 *Last*

*Ta sauke* wayar jiki a sanyaye haka ta mik'e ta sanya mayafi akan kayanta ta fito falo, gaba-d'aya tunani ya cunkushe mata zuciya _me zataje tace mishi."?_
Sai da ta leka d'akin mama sannan tace mata a kunyace tana yan soshe-soshe "Mama wai shine yazo."
Mama ta gane sai ta bita da kallo. "Haba Yaya kisa kwalli mana."
Hafsah tayi d'an murmushi ta juya ciki. Ta d'auki kwallin ta saka kuwa ta d'an fesa turare, ta shafa powder.
Data fito kuwa a palour taga mama, Mama ta mata magana daf da zata gifta ta.
"Saura kiki bashi ko da ruwa ne."
Hafsah ta toshe bakinta tana dariya amma Mama bata gani ba.

Yana Harabar gidan daga gefe ta hangoshi tana fitowa.. shima tana fitowa ya hangota aikuwa tana ganin ya ganta duk ta k'ara rikicewa taji k'afarta tayi nauyi da kyar take dagata saboda kwarjinin daya mata.

Tana k'ara doso shi tana gano yanayin fuskar shi, sam bazata ce akwai alamu na farinciki ko akasinsa a tattare dashi ba sai kyau da ya kara had'i da wani kwarjini cikin shigar shi ta voil na maza me kyan gaske sai agogon shi silver colour da hula.

Ya gyara tsayuwarshi sanda ta iso daf dashi, ya dan saci kallonta ya kawar da kai.
Ta hard'e hannu a kinji don samun kwarin guiwar tsayawa yayin da shi kuma nashi hannun guda daya ke cikin aljihun shi.

Ahankali ta sanya k'warin guiwa a muryarta ta mishi sallama.

Sai ya amsa a take babu wani jira amma daga amsawar bai k'ara ce mata komai ba.

Ta kalli gefe inda kujeru suke amma kuma bai zauna ba.

Cikin sanyin murya tace, "Baka zauna a kujera ba."
Ya girgiza kai "Noo nan ma is Okey."
Ta gyara tsayuwa ita dai ba gwanar tsawaita tsaiwa bace sannan tafi buk'atar su zauna d'in zasu fi fahimtar juna kuma ita kanta sai ta fi sakewa."

Tana wannan tunanin taji yace "Zuwa nayi na baki hak'uri ai... ya d'an dakata..
"Bansan xanyi laifi ba idan nayi miki wannan zantukan amma yanxu na fahimci na wuce gona da iri kiyi hak'uri."

Kafin tayi yunk'uri sai kawai taga yana k'okarin juyawa.
Baki na rawa ta bude zata kirashi sai dai ita kanta bata san sunan da zata kirashi ba.
Sai kawai taji bakinta yace,
"Allah ka tsaya!!
Haka ta iya cewa kawai, shima sai ya tsaya din kuwa.
Ta d'an kara takowa ta matso ya gama karanta raunin da take ciki.
"Ka zauna don Allah kaji..
Ya danyi jim, sai kuma
baiyi magana ba ya nufi kujerun itama ta bishi suka zauna kusan tare.

Wannan karon shiya fara magana. "To me kuma kike so Hafsah ko baki hak'ura bane."?
Murya a dashe ta sauke numfashi sannan tace, "I'm sorry please wallahi ni bansan..."
Sai kuma tayi shuru.
"Baki san me ba."?
Sai ta kama bakinta don zancen bashi da k'arashe. Ce mishi zatayi batasan an bashi ita ba ko me."?
"Kiyi magana mana."
Tayi shuru don bata da abin cewa.
Shuru ya mamaye gurin sai shi ya zuba mata ido.
"Bai zaci zata iya mishi abinda ta mishi ba, kuma yanxu yaji tana bashi hakuri to me hakan ke nufi."?

Ya katse shurun da dan yin gyaran murya.

"Me yasa kikayi shuru uhum.."? Bai jira cewarta ba shima ya shiga fad'ar abinda ke ranshi.

"Ni ina tunanin kamar mun zama daya ne, zan iya fad'a miki ra'ayi na a kanki."
Ya zubo mata idanu.. "Ba dole nayi niyyar miki ba Shawara na baki.. nima fa ina da k'anne mata Hafsah wallahi bazan aureki na cutar dake ba ki fad'a min duk wasu burikan ki in sha Allah zanyi kokari wajen ganin cikarsu..amma fa har ga Allah zan kara fad'a miki banason aikin gidan TV."

Kanta na kasa bata d'ago ba tace.. "Kayi hakuri.."
Ya kalleta da mamaki.
"Meyasa kike bani hak'uri ne."? Ai ra'ayinki kika nuna ba fa laifi kikai ba."

Ya tausasa murya don ya lura neman kuka take amma yana mamakinta.. _kamar ba itace ta mishi fada a waya ba to mene dalilin rauninta a yanzu.?_

A hankali ta kara bude baki zatayi magana sai kuma ta fasa.
Cikin sanyi shima yace "To kiyi hakuri kema na aibata miki k'awaye.!!
Ta rasa abin cewa sai tayi murmurshin jin kunya tana kawar dakai.

Suka k'ara yin shuru..ita tana matuk'ar son ta cire mishi shakku akanta amma kuma ta kasa ta yadda zatayi ta mishi bayani.

A yadda ta karance shi har yanzu abinda tayi mishi yana ranshi kuma tabbas ya saka ayar tambaya akanta.

So take ta kalleshi don ta k'ara fahimtar shi don haka ta dago da idonta sosai a sanyaye suka had'a ido ta kauda ido gefe.
Daidai da mik'ewarshi.. "Zan tafi," yace da ita.
Tayi shuru babu magana bata son ya tafi bata fahimtar dashi wani abu ba amma kuma ta kasa.

Sai ta lura da wani abu da yake mik'o mata, ita kuma tana can tunani.
Tayi sauri tasa hannu biyu ta amsa babu musu duk da tana shakkun karb'a.
"Ki gaida su mama."
Yace da ita tare da fara takun shi don barin gurin.

Sukaci karo da Bashir a tsakiyar gidan daidai lokacin shigowar shi kenan.
Bashir ya fad'ad'a murmurshi suka yi musabiha. Ukhashatu ne ya fara magana.. ya akayi mutumina baka tafin ba ne."?

Wallahi gobe nake shirin d'agawa.
Suka fara takowa zuwa inda Hafsah take, bisa dole tabar wajen.

Suka zauna suna fuskantar juna.. Ukhashatu yace "zamuyi missing dinka fa aboki."
Basheer yayi murmurshi, "Sosai fa especially mutuniyar taka.!!
Ukhashatu ya zubo mishi ido da wani kalar murmurshi akan fuskarshi wanda ke bayyana zallar shauk'i.

"Hmm to zamu hanaka tafiya."
Sukayi daria a tare..

Sunyi hira mai tsaho wacce yawancinta ta zancen makarantar da Bashir yake yi ne. Ukhasha yake kwatanta mishi wani abokinshi wanda yake matsayin HOD a makarantar Bashir bai gane shi ba don haka suka rufe zancen da cewa..zan mishi nuni da kai ince qanina ne yana da kirki mutumin.
Bashir ya amsa da "Toh nagode Yaya.
Ukhashatu ya duba agogonshi. "Bari na wuce kaji."
Bashir ya mik'e suna takawa har qofar gida in da yabar motarshi.. _HONDA ACCORD._ motar da Hafsah bata ma san ya na da ita ba.

Sukayi musabiha bayan Ukhashatu ya shiga mota. "To qanina Allah ya kiyaye hanya kaji."
"Amiin, inji Bashir.
Ya motsa da niyyar juyawa Ukhashatu ya kirashi. "Bashir na manta Ungo wannan."
Bashir zaton shi sak'on Hafsah ne don haka ya mik'a hannu. Ukhashatu ya mik'o mishi kudin. Bashir yayi jimm, "karbi mana." Inji Ukhashatu.
Bashir ya amsa yana kallonshi da neman k'arin bayani.
"Ka kara guzuri dashi nagode ka gaida su Abba.

Bashir yayi jimm jiki a sanyaye yana buda baki zai ce mishi "angode" ya ga har ya fara tada motar duk da haka sai da ya fada "angode."
Ukhasha ya d'aga mishi hannu kafin ya ja motar ya wuce..
__________________
A palour ta fada kan kujera sanda ta koma cikin gida. Mufeedah ce da amira a palourn babu Zainab suna ganinta suka maida hankalinsu kanta da alama tana cikin damuwa.

Kamar ta rusa ihu haka take ji.. ya akayi tayi sakaci har ya tafi bata wanke kanta ba a wajen shi."?

Ta bata mintuna a daskare hankalinta na can ga tunani, sai da mufida ta kirata.
Yaya baki tab'a nuna min ya Ukhashatu ba aunty Ameera ce kawai ta sanshi.
Da zata share ta sai kuma ta bude baki a hankali tace.. Idan ya qara zuwa zan kiraku ku gaisa."
Cike da fara'a Mufeedah tace "Yaushe zai k'ara xuwa eh yaya."?
"I don't know! ta fada a kufule.
Mufida ta kama kanta don taga kamar a sama yayar tasu take.

Kamar an tsikare ta yi zumbur ta duba gefenta inda ta ajye ledar data shigo da ita.
Ta dauka da sauri cikin zakuwa take son taga menene aciki.

Da sauri ta zaro abinda taci karo da shi..wani dan box (akwatu) ne shima ta buda shi da sauri ta zaro zoben da ta gani ciki sai shek'i yake.

A hankali ta zame zoben hannunta.. wanda idan zata tuna shine na Yusuf daya kawo mata dake ba sashi take ba sai lokaci zuwa lokaci saboda haka yana nan kar kasancewar shi _Gold_ shima na yanxun gold ne mai matuk'ar kyau. Ai kuwa tana zame shi tayi cilli dashi. Idanun qannenta tun dazu akanta don haka tana yarwa mufeedah tayi zaraf ta samu. Har suna fada da Zainab.
Yadda take zura zoben a hannunta a hankali ta kuma wani irin shauk'i tana jin wata iriyar k'auna na shigar ta.

Yayi mata kyau matuka a a hannunta tana gamawa ta maida akwatun cikin ledar sai ta lura da wata yar takarda a ciki da sauri ta dakko ta a dan nannad'e take don haka ta yi saurin bude ta yar qarama ce sosai. Da rubutun biro kuma da hannu (handwriting) me kyau taga an rubuta _"I love you.."_
Ta ja wata doguwar ajiyar zuciya da tunanin dalilin kyautan haka a halin da suke ciki..
Chapter 81 · 0% Book details