← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 88

Sashe 6

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*KO* da Hafsah ta kwanta bacci tunani uku ne ya had'ar mata..
Na farko mummunan labarin data samu akan jamila ya tsorata ta sosai ya sanya mata tsoron shiga soyayya..
Na biyu kuma saurayinta na 'Seven months' daya dawo yau, hak'ika ganinshi da tsarin surarshi da wayewarshi ya chanja mata tunaninta akan soyayya... Da ta rufe idonta shi take gani,yayin da kalamanshi ke mata yawo a kunnuwanta..
Ahankali ta furta "My new found love"!!
Tayi murmushi tare da k'ara rungume pillow a k'irjinta lallai tayi farin gani ayau,bata tab'a tunanin samun kamar yusuf a cikin rayuwarta ba...
Sai dai me??
Gabanta ne ya fad'i da ta tuna da kyautarshi gareta wato (wayar daya bata)
"Innalillahi"
Ta fad'a ahankali wato wannan ne lokaci na farko data tab'a mallakar wani abu ba tare da sanin mahaifanta ba.
Bata daga cikin yara masu b'oye wa iyayensu komai.. Duk da wasu daga cikin 'yan ajinsu nayi... Misali sau dayawa idan ana hira zataji 'Basma yunus' tace "wannan wayar wani ne yaba ni amma ko maman mu batasan ina da waya ba.."
Ko wani zancen makamancin haka..
Sai take ganin "Ina iyayen nasu suke ??
Baxata tab'a iya b'oye wa mama komai ba..don koma ta b'oye mata sai ta gane, don mama bata da shamaki da ko ina a d'akin tana xuwa ta bud'e komai..
A hankali taji an turo d'akin..mama ce bisa al'adarta takan lek'o su duk tsakiyar dare domin duba su.
"Bakiyi bacci bane Hafsah"?
"Um yanxu dai na farka"
" Kin yi addu,a dai Koh?
"Eh"
"To kiyi k'ok'ari ki koma bacci gobe dai kin san da makaranta."
"To mama"
"Sai da safe" mama ta fad'a tana jawo mata k'ofar ta fita.
"Hum!!
Hafsah tayi ajiyar xuciya.
Wato yusuf dai ya had'u ko ta ina..duk yadda take bukatar mijinta ya kasance (A siffofinshi) Yusuf ya kai har da k'ari..
Ita kadai tayi murmushi tana lumshe ido,ahaka bacci ya sace ta...

*Washe Gari*
*A Makaranta*
Aji ne mai d'auke da dalibai kamar guda 30 ne kuma duka, mata ne kawai class SS 2b kenan.. Wanda SS 2a ya kasance na maxaa xallah.Haka tsarin makarantar yake..
Row d'in tsakiya desk na biyu shine maxaunin Hafsah, Itace a tsakiya.Su uku ne a desk d'in hajara Umar, sai Hafsah H. Hamid sai Fatima Mukhtar.
Saman desk en kuwa wata d'alibace Mai matsakaiciyar ki'ba fatarta coffee colour, uniform d'inta sunsha goga..
Surutu kawai take ta zubawa..
'Basma yunus kenan.' uwar rawar kai da gigi..
Tsit ajin yayi sakamakon shigowar Malamin English d'insu teacher Ahmad kenan 'Gajere Sai Fad'in Rai'🤣
Sunan da suka lak'aba mishi kenan..
Sam basma bata san da shigowar shi ba surutunta kawai take xubawa..
"Hey stupid !!
Go out from my class!!
Ya fad'a cikin wata tsawa daya sa ajin yin wani tsit, kamar babu halitta mai motsi acikinshi.
"Dim" basma ta duro daga desk en sannan ta tsaya chak a tsakiyar ajin ta kalli malamin ta wurga mishi wata uwar harara..
"I say get out"
Ya fad'a yana zare ido..
"Humm" basma ta fad'a tana hura hanci..ta k'ara galla mishi harara sannan ta fita..
Malamin ya d'auki marker sannan ya fara magana *to day our lesson is..*

Teacher Ahmad Ya iya koyarwa sai dai baya son raini, kuma baya son wasa da alama jininsu bai hadu ba da basma.Don ta tsani ya shigo,shi kuma ya tsani surutu..
Da aka fita break ne suka had'a dandalin hira. Duk da Hafsah bata fiya yawan magana ba,amma takan saka baki a hirar tasu wacce yawancinta ta samari ce ko kuma ta wani party ko birthday na wata da xa,ayi.
Basma ta d'ãkawa Hafsah duka abaya..
"Ku H. Hamid fa munafuka ce, sai dai ta zauna taji cikin mutane, amma ita baka tab'a jin hirar saurayinta!!.
Suka yi dariya "Hahh, gaskiya ne fa, ko dai rowa take mana ne..
"Hmm.. Hafsah kawai tace, sannan ta jawo basma ta rad'a mata a kunne..
"Ke biki saniba jiya nayi wani har ya kawomin I phone nak'i karba sai Samsung shima a gida ba,a sani ba..
Kut m... 😠
"Gaskiya H Hamid Baki da hankali.."
Basma ta fad'a cikin karaji..
(Kuji min ita da ake mata rada)😒

"Me ya faru?
Dukansu suka tambaya.
"Wai don iskanci a bata I phone ta mana bak'in ciki"?😏
Ta fad'a tana dungurewa Hafsah kai.
Hafsah ta toshe mata baki, "ke basma ki bari don allah..
Sai lokacin Fatima Mukhtar tayi magana
"to Menene kawai daga bata waya sai ta karb'a?
"Eh mana, meye aciki?
Inji basma.
Babu ruk'ayya ta fad'a.
Basma taja hannun Hafsah zo muyi sirri k'awata.
"Yanzu ina wayar?
Inji basma sanda suka isa can layin baya suka keb'e.
"K'arama ce fa wayar, ni tsoro ma nakeji."
"Kinjiki tsoron me?
"Abbanmu."
ta d'anyi shiru sannan ta d'ora.
"Ya hanani kula samari fa"
"Hmm to ke bari zaki yi ya gane?..
"Ni dai gobe kizo da wayar."
"K'ilama yana ta kiranki kinki kunna wayar.. Ki kunna idan kinje gida dallah."
"OK zan kunna saboda kada yaji shiru ya k'ara dawowa don yau abbanmu zai dawo."
"Ki dai zauna ayi babu ke" basma ta fad'a tana dariya..
"Hahh" Don dai kawai ya had'u ne gayen, da babu ruwana dashi.
"Hahh" ta daki bayan ta. "H Hamid anji guys"!!
To bayan ta koma gida, aiki ta tarar mama nayi na tabar abba (wanda yayi wata 'yar tafiya zuwa Abuja na kwana biyu) ta zauna sukayi aikin ita da mama ko islamiyya bata samu zuwa ba.
Suna aikin mama najanta da hira Kala -kala kamar k'awarta.
Da la,asar abba ya iso suka tare shi suna mishi Sannu da zuwa ita da mama.
"Yawwa, sannunku ku ma."
Ya sauke kallonshi kan Hafsah "Baki je islamiyya bane.?"
"Aiki ta taya ni" cewar mama suna k'arasowa falo, sannan suka shiga wata k'ofa wacce shine falon mama had'e da bed room d'inta.

"Kije kiyi wanka kema"
Inji mama sannan suka shige d'akinta ita da abba.
Gidan yayi shiru dama k'annen nata suntafi islamiyya.
Mama da daddy kam suna da'aki.
Bayan tayi wanka a toilet d'in d'akinta ta d'an yi shafa sannan ta saka wasu pink d'in riga da wando jeans saka wata pink d'in turban ta d'aure kanta dashi sai tayi kyau sosai.
Hafsah kenan doguwa ce bata da k'iba kwata-kwata kuma ba siririya bace, tana da hasken fata mai ja,
tare da bak'in gashi dogo amma bai cika yawa ba.
Bud'e wardrop d'in can k'asan kayanta ta bincika ta d'auko ledar da kwalin wayar ke ciki.

Ahankali ta k'arasa ta sawa d'akin key. Sannan ta dawo ta zauna.
Akan gadonta ta mik'e k'afarta mai zara-zaran yatsu.
Ahankali kuma cikin tsoro take bud'e kwalin wayar 'yar k'arama ce mai kyau.
Ta kunna ta..minti kad'an ta kunnu.
Chapter 6 · 0% Book details