← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 88

Sashe 41

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Zainab tana level 2 yanzu inda take karanta pharmacy, a qallah zatayi shekaru, 21. Sai Ameera, me jiran admission, sai mufeeda da take year din qarshe a secondary. Dukkansu babu wacce baza,a kaita gidan miji taki zama ba, ko waccen su ta girma sosai akwai wayewa tattare dasu, ta fuskar komai, amma waye wa irin ta masu ilimin addini. Suna da class amma sam ba,a taba kwatanta su da masu wulaqanci ko wani girman kai..' Hakan ya isa abin godiya ga Allah a wajen, iyayensu sun haifi 'ya'ya kusan dukka mata, kuma sun iya da tarbiyyar su, abin alfahrin daddy ne ace cikin yayanshi har da wacce ta hadda ce al,qur,ani (Zainab) yaso hakan ga Hafsah, amma komai nufin Allah ne, domin falalar sa ce, da yake bawa duk wanda yaso." Itama tana da izufi talatin cif, akanta, wanda ba gazawa ce ko wani abin makamancin ta, ya hanata karasawa ba sai dai abin na Allah neh..' Sauran suna iya kokarin su don suma suna karatun daidai gwargwado ciki harda Basheer. Kullum fatan iyayensu shine Allah ya kawo musu miji na gari. Duk da ba su rasa masu sonsu ba sai dai abin komai lokaci ne. "Yayah, ? Abba ya kirata kamar yadda ya saba karanta ko yaushe. "Na,am Abba." Yau Basheer yaxo koh, ana ta hira." Tayi murmushi. Kin gaji koh"? Ta daga kai alamar "Eh" "To aje aci abinci a kwanta koh tunda ya cika ki da hira ya fice koh."? Dariya ta danyi, tabbas tana son ta kwanta ta huta. Kitchen ta wuce, cike da farin ciki tana son wannan kulawar da take samu awajen abban ta, bata jin wani daga cikin su yana samun irinta, dole ta yi abinda zai dinga faranta mishi rai shima indai tana son ta dace da rahmar ubangiji. Kad'an ta zuba abincin, ta fito ta sami guri akan center carpet kusa da, zainab da take fama da litattafai ta zauna. Mama ta kalli plate din, "Shikenan dan abincin da zakici Hafsah."? "Banajin yunwa sosai mama." Bama ta cinye abincin duka ba, ta tashi ta mayar kitchen, sannan ta musu sallama ta shige dakin ta, wanda mallakinta ne ita da mufeeda har yanzu. Yayin da Ameera da Zainab suke da d`aki d`aya, sai dakin Basheer shi kad`ai. Sallar isha ta fara yi sannan ta cire kayan jikinta ta mayar dana bacci. A gajiye ta haye gadon ta kwanta da tunanin fal cikin zuciyar ta. "Lallai maganar Basheer, abar dubawa ce, abin yana tsorata ta idan ta tuna wai ita ce me shekara 25, a duniya, lokaci yana matuqar gudu, bata tab'a zaton zata kawo irin wannan lokacin baa gidan mijinta ba, tasan haka ma burin Abbansu yake. Mates dinta da yawa anyi aurensu, ciki harda Aisha, wasu ma harda yara biyu harda masu uku, amma ba ta taba sawa ranta damuwar hakan ba, tunda tasani kowa da yadda Allah ya tsara mishi tashi rayuwar.' Bazatace bata da masu sonta ba ko kuma wanda taji yayi mata, amma xata iya cewa zuciyar ta rabu da son wani D`an adam, kwatankwacin irin son da ta yiwa Yusuf, ko da rabin hakan ne. Sai muka wani abu da ake cewa _"Ko wacce kwarya..._ Ita ba raina arziqi bace ko kuma buri da son abin duniya, amma ya zama wajibi ta duba wanda zasu samu daidaito, Domin shi zaman auren ba wai zamane na wata daya ko shekara ba, zama ne na din-din -din, ta yuwu tun kana iya jure tsanani da hakuri, har azo _level_ din da zakaji bazaka iya jurewa ba." Saboda haka ita ba sauri take ba sam, abbansu ya hore ta da gudun gaggawa acikin al,amra. Har tana tuna wata magana da take cewa, _''One day it will just happens, you will meet the one that will love you the way you deserved to be love, and you no longer have to fight for it.._ In ta tuna tana samun nutsuwar zuciya, da hakan, kuma tasan Tabbas wata rana zata iya samu, kasancewar tasha haduwa da wadanda kai tsayen zata iya cewa basu dace da ita d`in ba ta fuskar mu,amala, suna mata kamanceceniya da irin ta Yusuf, ko kuma ta fuskar dabi,u da Yanayin fahimtar rayuwa. A haka har ta tattara su ta watsar ta mayar da hankalinta gabadaya kan karatun ta wanda dashi take fatan gina feature dinta. To irin haka ce tayi ta gara rayuwarta da zamaninta, har kawo yanzu, da shekaru suka shud`a ba tare da ta ankare ba, amma yanzu bulaliyar da Basheer yayi mata ta farkar da ita, cewa Tabbas akwai buqatar ta matsa ta bawa 'yan baya waje, suma suci nasu zamanin. Don da tuni ma Ameerah tayi mata tsallake, sai aka samun akasin tafiya k`aro course da mijin da ta samu yayi wanda zai kai shekara d`aya, zuwa da rabi, da tuni ansa rana, kuma abinka da itama karatu take sai duk ba,a damu ba. Da ire-iren qananun tunanin nan ta fada kogin tunanin tuno rayuwarta ta baya wato shekarun zaman ta gidan Mama, wanda ta kirasu da shekarun gwagwarmaya....
Chapter 41 · 0% Book details