← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 88

Sashe 31

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Story and writing by: *Karima Tijjani Mansur* *(Hajeeyah Kareemerh)* *Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members* 📄 *33-35* *Basma* ta saki ajiyar zuciya tana wa yusuf kallon tuhuma, shikuma ya had'e hannayenshi biyu alamar Afwan sannan ya fice da hanzari, yafi su Hafsah.' "Hafsah, hafsah baby.. Please ki tsaya mana". 'Kiranta yake amma Aysha sai faman janta take, tana d'aga mata kafada, alamar kada ta tsaya.' 'Abin mamaki sai ganin Hafsah, tayi ta fizge hannunta, ta d'an yi baya, ta tsaya cak.' 'Ya saki ajiyar zuciya, sannan ya k'araso cikin sassarfa.' Am sorry Baby, wllhi banci amanarki ba, kuma, ki believing me, bazan tab'a rabuwa da ke ba, even if i got everything from Basma.." "Ya isa,!! Ta fad'a cikin tsawa.' Kana nufin hakan ba cin amana ne ba koh?" 'Ya dafa kai, ke kika janyo koma menene, i have tell you for multiple times, idan baki yarda dani ba, komai ya faru kada ki zargeni." "And I swear to God, ko yanzu kika daina guduna, zan rabu da Basma." "Ki yarda ban miki cin amanar rabuwa da ke ba'! 'Ji tayi hankalin ta na neman barin jikinta. 'Wanne irin soyayya kenan sukeyi, Zai rabu da basma idan ta aminta da buk'atar sa,.. Idan kuma ba haka ba zata zauna da kishiyarta kenan wato Basma?? "A hankalce ma abin babu tsari. 'Ta rasa wanne martani zata mayar mishi, iya bak'in ciki dai ta shak'a acikin kalamanshi, har wani abu ne ya tare, mata mak'oshi.' 'Ta girgiza kai cike da k'uncin rai tace cikin sanyin murya.' 'Yusuf na gode da sakayyar da kayi min.' Kuma nagode, da matsayina da ka nuna min.' ta nuna kanta, "Yusuf wai ni kayi wa haka koh? "Na gode, wasu hawaye masu zafi, suka sakko zuwa, kan kuncinta.' 'Cikin gudu gudu, tayi saurin bar mishi wajen.' 'Kiranta yake amma ina tuni Aysha ta janye ta sukayi gaba.' 'Mai gadi ya yana musu a sauka lafiya,Hajiya.' 'Cikin sa,a suka sami Napep, cikin layin duk da GRA ne, 'Tunda suka shiga Hafsa keta faman aikin kuka, Aisha na faman rarrashinta, amma ina, abu yaci- tura, babu abinda take fad'a sai "Aysha yusuf yaci amanata, ya cuceni." 'Ita dai Aysha hak'uri kawai take bata.' Sun kusa isa gidansu Hafsah, aka kira Aisha a waya, ta d'aga.' "Hello mama,.. Ok, tom ina hanya yanxu zan dawo.' 'Ta Kalli Hafsah.' Kinga mama ce ke kirana, idan aka sauke ki sai ya wuce dani da nayi niyyar in raka ki gida.' 'Hafsah ta gyad'a kai kawai.' "Amma don Allah Hafsah ki saita kanki kada mama ta gane, halin da ake ciki." 'Hafsah ta gyad'a mata kai.' ta d'akko 'Handkerchief' daga cikin Jakarta, ta mik'a mata.' "Please ki goge hawayenki." 'Ta karb'a tana gogewa wani na k'ara fitowa.' 'Har k'ofar gida, aka kaisu.' Kuma, tun sanda suka shigo layin, ta cikin madubi, Hafsah ta lura da motar Abbansu dake bayansu.' "Don Allah ki cire damuwa ki mai da komai kamar bai faru ba, please H. HAMID." cewar Aysha kenan sanda akayi parking a k'ofar gidansu Hafsah.' 'Dak'yar Hafsah iya cewa, "Nagode, sosai Aysha ki gaida mamanku." Tana fitowa daga cikin Napep, d'in motar Abba na sako kai, kuma ta tabbatar ya ganta.' 'Tayi saurin tura gate ta shige ciki tana k'ara goge fuskarta.' 'Tun daga yanayin data ga mama tasan da akwai matsala, gashi kuma maman ta k'ura mata ido tun amsa sallamar ta.' 'Tasha jinin jikinta sosai, sai lokacin ta tuna cewa 'rufe gidan tayi ta fita.' 'Tayi hanyar d'aki kenan mama tace, "Ke, zonan." Cikin rawar jiki ta juyo ahankali take takawa takowa.' "Daga ina kike"? 'Cikin tsawa maman ta tambayeta.' 'Nan ta hau kame- kame,.. "Um..wai ni..? in.. dama Aysha ce.." 'Mama ta daka mata tsawar data sata razana.' "Zaki fad'amin min ko sai ranki ya b'aci."?? 'Dai dai lokacin Abba ya shigo falon, jin mama na yin fad'a yasa yace, "Menene wai yake faruwa, lafiya."? 'Hmm inji mama, tare da yin kwafa 'k' ta nuna Hafsah, da yatsa, gatanan sai ta fad'a maka tunda kazo kai.' 'Cikin rashin fahimta Abba yace, "Me yake faruwa ne ki fad'a min me ta yi kuma."?? 'Mama ta nuna ta, ka ganta, wai na fita na bar mata jiran gida, shine ta fice ta kulle gidan ta fice yawonta.." 'Abba yayi dogon numfashi, ya zauna kan kujerar bayanshi, ya kalli, hafsah data durk'usa a k'asa. cikin kaushin yace Ke, ina kika je. ehe"? 'Cikin rud'ewar murya tace "Abba dama Aysha ce tazo na rakata asibiti.." "Shine kuma fuskar ki ta kumbura koh"? 'Ya katse hanzarin ta da tambayar.' 'Ta kai hannunta ta shafa fuskar, sai yanzu itama Mama ta lura da jan da idon Hafsah yayi.' 'Hafsah tayi kus, ta kasa bud'a baki tayi magana, sai hawaye ma da suka cika idanunta, na k'uncin da zuciyarta ke ciki.' 'Duka, da Abba da Maman ido suka zobo mata ta lura sosai da kallon tuhumar da dukkansu, suke mata.' 'Kwakwalwar ta chakud'e, gefe na k'okarin tariyo mata abinda ya faru da gidan su Yusuf, gefe na karanto mata tsoro da kuma neman abinda zata fad'awa Abba.' 'Ta d'an runtse idonta, kawai sai photon, abinda ta gani ya hasko cikin idonta, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, tama manta gabansu abba take.' 'Abba ya fusata, ya kawo mata duka, mama da zuciyarta ta shiga rud'u ta tare shi tana cewa, "Don Allah kada ka daketa ka kyaleta ta yi magana.' Cikin fad'a Abba ya fara magana "In kyaleta koh, kina sangarta ta koh? "Don iskanci daga tambayarta sai ta hau yiwa mutane kuka"? "Yayi kyau, shikenan ki goyi bayan ta!" 'Ya Mike fuu yayi daki, yabar Hafsa durk'ushe a wajen, har ya dakko abinda ya zo nema ya dawo ya fice cikin sauri.' 'Mama da tun sanda ya shige tayi shiru ta rasa abin da zata cewa Hafsah ma.' 'Har wajen tsawon minti biyu, sannan maman ta k'irkiro abin cewa, cikin tsawa ta yi mata magana.' 'Zaki fad'i inda kika je ko sai nayi ball da ke anan wajen.'? Hafsah ta d'ago a razane, har yanzu k'wallar bata daina d'iga ba.' "Basma aka kwantar um.. a asibiti shine aysha,mukaje..Asibiti duba ta.." 'Tana dire zancen mama ta d'auka. "Karya kikeyi" "Wallahi Hafsah idan baki fad'amin gidan uban da kika je ba sai na k'arya ki anan." "Wallahi, Mama can muka.." Ta, doka mata tsawa.' "Dubiya da tsakar ranar nan koh,?.. To uban meye ya kumbura miki ido, fuskarki tayi ja ehe." "Um, wallahi tun jiya mama nake ciwon ido dama." 'Mama tayi shiru, ba, wai don ta yarda da shiryayyen zancen Hafsah ba, kawai dai ta shiga rud'ani ne.' 'Kuma akace,' 'Mace' tana da rauni.' To agurin mama, raunin shine yayi tasiri, sai tunanin ta ya chanja gabad'aya zuwa wani layi daban.' Bisa wani karatu da zuciyarta tayi mata.' 'Ta fara tuno abubuwan da suke faruwa tun had'uwar Hafsah da Yusuf.' 'Zuwan Hafsah gidan Hajiyah na k'arshe, sai babban tashin hankalinta 'ranar bikin uncle abdallah, fitar da hafsah tayi ita da wani.'.. To yau ma gashi ta fita ba,a sani ba, kuma yadda mama ta kiyasta tafi awa d'aya bata gidan.' 'Don ita kanta maman wajen awarta d'aya da dawowa. Mamaki da tsoro suka mamaye ta data ga gidan a k'ulle.' 'Duk da tana da 'Spare' na muk'ulli acikin jakarta, hankalinta bai kwanta ba sai da tayi ta zagayen mak'ota tana cikiyar ko Hafsah ta shigo.' 'A farko tunaninta ko ta gaji da zaman shiru ta shiga mak'otan, duk da tasan Hafsah bata da tsoron zama ita kad'ai cikin gida sannan kuma bata da shige shigen mak'ota.'. 'Ashe ita Hafsan ta tafi wani wuri can abinta.' To ina taje kenan,? Ita da wa,? 'Allah ya kiyaye kada dai Hafsah na k'okarin kama wani layi na daban ne.' idan ta duba zata ga gaba-d'aya Hafsah ta canja dabi,u.' 'Zaman shiru yawan tunani sai kuma b'oye b'oyen da ta tsiri yi mata yanzu, sai fita bada saninta ba.' 'Wanda ada ba haka bane.' 'To Meyake faruwa? ka da dai ace ansami wani ya gurb'atawa 'yarta tunani da kuma tarbiyyar da suka dad'e suna tattalinta.' 'Wannan tunanin na Mama, ya jawo abubuwa da dama..' 'Sallamar Hajiya ita ta farko da Mama daga dogon tunanin da ta tafi.' 'Ta amsa cikin sanyi, ta fara yiwa Hajiya sannu da zuwa.' 'Yawwa inji Hajiya, Hajiya ta zauna, sai lokacin ta lura da Hafsah, zatayi magana Mama ta hau gaisheta.' "Sai da ta amsa, cikin sakin fuska, sannan ta juyo ga Hafsah, "Ke kuma fa? 'Kinyi wani jugum dake ba kya gaida mutane"? 'Hafsah ta d'ago tare da dai dai ta fuskarta.' 'Hajiya sannu da zuwa, ina wuni.' "Lpia lau" 'Hajiyan ta amsa, sannan ta dire tambayarta, "Me akayi miki ne.' 'Kunya ta hana Hafsah amsawa, ita da tayi laifi kuma ake tambayarta me akayi mata'?? 'Mama ta cafe zancen' "Laifi tayi." 'Hmm ko da naji, sai wani wuk'i wuk'i kike da ido kamar mara gaskiya." "Ashe kuwa baki da gaskiyar." 'Mama taji gabanta ya fad'i rashin gaskiya kuma.'? To me Hajiya take nufi,? 'Kada dai ta gano wani abu, game da Hafsah, tun da dai ita Babba ce.' 'Nan lissafin Mama ya k'ara jagule wa.' 'Ta mik'e ta nufi kitchen don debowa Hajiyah abinci.' 'Lokacin kuma aka kira sallar la,asar, saboda haka Hajiya ta mik'e don yin alwala, ta kalli Hafsah, "Ja,ira sai ki tashi an kira sallah.." "Naji yace kin k'are boko koh."? "Ai, ashe bokon naku bana k'arau bane, kin gama secondira" 'Hafsa ta gyad'a kai. "To Allah yasa albarka." 'Ta mik'e ta nufi d'akinta, tana godewa Allah, da Hajiya tazo da tuni har yanzu Mama na faman tuhumar ta.' 'Maimakon tayi alwala, sai alhinin abinda ya faru ya danne k'arfinta ta kwanta ta fashe da wani matsanancin kuka, tana jajanta wa kanta, wannan cin amana da aka dad'e anayi mata, da sai yau, Allah ya nufa ta sani.' 'Taci kuka ta goge Allah har ta tausaya wa kanta, babban abinda yafi tasar mata da hankali shine, 'Yanzu a wanne matsayi take gun Yusuf.'? 'Ashe Yusuf duk soyayyar da yake karanta mata ta k'arya ce.'? Ita data rik'i Basma aminiya, shine zata ci amanarta.'? 'Ashe da gaskene sauyin data dinga gani a wajen Basma.'.. Wayasan lokacin da suka d'auka suna aikata haka,? 'Sun ninke ta abai-bai.. 'Ta
Chapter 31 · 0% Book details