Sashe 58
Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ina ka sanni ni.? Hmm, na ganki a wurare da dama." ka fad`amin, kawai." Na ganki a television ne kina _program_ d'inki." Bata san sanda tayi murmushi ba tare da cewa sai kuma ina."? Shima murmushin yayi, zan fad'a miki sauran amma ba yanzu ba. "Hmm, ka fad`amin wanda ya baka number ta. "Allah ne ya bani." Ya fad'a da zolaya. Hmm, _I knew that._ Tace mishi. Ya k'ara yin murmushi, "Yawwa don shi na rok'a kuma ya bani." Bata k'ara cewa komai ba. Suka danyi shuru. Sannan tace, "Okay toh sai anjima." "Kiyi hak'uri by time zaki gane wane ni, sannan ki min alfarma guda d'aya." "Tame fah."? "Kiyi saving d`in nombar nan don Allah. "Banyi alkawari ba.!" "Girmanki ne ai, nagode, ki huta lafiya. Ya katse wayar lokaci d'aya. Ya barta da tunani. Wanene wannan, me nutsuwa, dad`i da kuma sanyin murya."? Me yasa ya kirata ya mata haka."? Babu alamun k'uruciya a Yanayin muryarshi da zantukan shi, bare tayi tunanin rainin hankali ne irin na samari. Yace, _by time zata gane wanene shi._ To Yaushe yake nufi kenan."? Yace _Allah ne ya bashi number ta._ Yana nufin ba zai fad'a mata inda ya samu ba kenan.? Kai akwai alamar tambaya.!! Ita ko irin mutanen da ke kiranta ne, ba haka ta saba amsa gaisuwar su ba, yawanci ma anfi kulata a chat ko ta email. Idan kuwa aka kirata kai tsaye za,ace _muna jin dadin shirinki, kina burgeni wallahi, abubuwa makamantan haka dai._ _Amma shi fa?_ Sam ba da haka yazo mata ba, sai ma afuwa da yake ta nema akan ya kirata, bada izini ba. Kuma yace a TV ya ganta, ta kasa yarda da hakan. Duk yanda akayi yayi mata kyakykyawan sani, data gaji da b'ata lokaci wajen tunane tunane sai kawai ta share abin, amma fa takan tuno muryarshi lokaci zuwa lokaci. Bangaren shi, farin cikin daya shiga bazai misaltu, bisa jin muryar ta da yayi ayau d'innan. "Alhamdulillah Alhamdulillah yake ta maimaitawa. Azuciyar shi, yana addu,ar Allah ya mallaka mishi ita. Kowa na gidan ya gane yana cikin farin ciki yau, haka kawai ya fita yayiwa driver ( _wanda ya kaishi gidan baffa_) kyauta, bisa tuno kalaman shi masu hikima. _Ranka ya dad'e ai aure yana cika darajar mutum ne.. Tunda manya sun nuna suna so sai ayi musu kodan biyayya._ To shi ba auren yayi ba ma, amma farin cikin da yake ciki Allah ne kad'ai yasan adadinshi. Bai k'ara kiran ta ba, har washegari, gwara ya barta ta huta, tunda babu sanayya a tsakaninsu, bata sanshi ba sam. Kada ta gaji da shi. Sai da daddare ya kirata bayan kwana biyu, batayi saving number d`in ba, amma muryarshi ce tasa ta gane shine. "Assalamu alaykum. Ta amsa mishi itama. "I hope ba kiyi bacci ba na tashe ki." Ya fara da haka. "No." Tafad'a. "Kingane mai magana."? Azahiri amsar ita ce "Eh, amma saboda ta ja _class_ sai tace, "Aa." Yayi murmushi, _"To Ukhasha d'innan ne dai mai nacin nan."_ Ya bata dariya babu shiri. _"Hmm_ tace mishi kawai. Yayi k'asa da murya, yana rok'o. "Please ki taimaka kiyi saving number nan mana."? "No banyi alkawari ba." "Meyasa." "Saboda bansan ka ba." Cikin marairaice murya, irin ta wanda ake tuhuma yace, "Wallahi sunana ukhasha, ba karya na miki ba.!!" Ya bata dariya sosai, wannan wanne irin mutum ne, mai barkwanci haka Allah ya had'ata dashi..? Gashi sai yayi magana kamar bashi yayi ba, da nutsuwa a muryarshi sosai haka daga jin shi babba ne da saita ce, _irin rainin hankalin samari ne._ "Hmm, inda ka sami number ta shi nakeson in sani." Ta fad'a bayan ta gimtse dariyarta. "Oh tun a duniya ne fah na samu.!! Sai da tayi da gaske sannan ta tsayar da dariyarta wannan karon. "Hmm, Bazaka fad'amin ba koh."?