← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 88

Sashe 55

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kawai sai yayiwa Fadwa nuni alamar _taje inda zata._
yana gani tana kunshe baki alamar dariya take mishi.
Yayi kwafa azuci,
"To kije gida, kada mamanki ta nemi ki, kuma ki daina fitowa irin haka, mata basa zuwa wajen maza."
Ya fad'a yana kakkauda kai.
_"To gashi_ ta mik'a mishi, ledar hannunta. Bai karb'a ba ya tsaya yana mata kallon mamaki.
"Kayan party d'inne."
Nagode yace mata, rai a had'e zai juya ya barta gun, yaji tace, "Don Allah ka karb'a.
Baya son su tsawaita, Allah ne ma ya rufa mishi asiri abba baya nan.
"Ya mik'a mata hannu, ya amsa.
Cikin k'osawa ya mata alama, _kije gida, kije gida._ yace da ita.
Yana k'ara kallon shigarta, riga da skirt na atamfa matsatstsu, sai siririn mayafi.
Tayi Jim tana kallon shi. Shima wani tunani yayi.
_Za,a iya zargin shi fa, musamman ma,aikatan gidan._
Allah yaso a iya nan suka tsaya.
Wuce muje yace mata, don yaga kallon da take mishi yayi yawa.
Don gwara agansu tare d'in.
Sai da suka zo bakin gate d`in fita, yace mata, _"Maza kije gida na gode ki gaida mama kinji."_
Tana murmushi ta d'aga mishi hannu. Ya juya ya koma ciki da ledar a hannu.
Yana shiga yayi wurgi da kayan, a k'asa, suka zubo daga cikin ledar, memo ne, me photonta ajiki, sai tarkacen su snacks.
Lallai dole yasan abinyi, tun kafin abubuwa suyi nisa , ai baisan yarinyar haka take ba.
Sai daya kintaci taje gida ya kirata.
"Ke ya akayi kika san gidanmu."
"Um da dama na sani fah."
"To ke a ina kike."
"Can gaba da layin ku."
"Kada ki k'ara min haka, kada ki sake zuwa gidan mu."
Ya fad'a cikin kaushin murya.
Sai ta fara kuka, tana fadar wasu maganganu da bai bi takansu ba, wai ita sonshi take, ta gaji kwana biyu bata ganinshi, kuma don tazo gidan su shine yake mata fada haka."?

Shidai ya katse wayar yana, takaici. Ya zama wajibi ya yanke alak'arsu dama ya gaji.

Tun lokcin duk wani block yayi amma, chanja layi take, kamar me aiki a companin _SIM card_ da yayi block zata chanja number ta kirashi, har ya gaji ya daina, idan ta kira ya share, amma haka zatayi ta kira kamar bata da aikin yi sai kiranshi, ala dole yake d`agawa ko dan ta barshi yayi aikinshi sosai. Ya gaji da abubuwan, shine ya d`auki matakin tunda yarinya ce, bara ya bita ta yadda kwakwalwarta zata iya d'auka. "Ya kirata da kanshi wata rana yace, za,a bashi mata a gidansu.
Amma ga mamakinshi bata nuna alamun damuwa ba tace, "Ta ji yayi ta biyu da ita zata jira shi.!!
Gaba-d`aya lamuran yarinyar sun dame shi, shi ba abin ya sauya number shi ba, yana da abubuwan da suke da matuk'ar muhimmanci akan number, Misali account d'inshi na banki, da sauransu.

Wasa-wasa watansu shidda shida ita, ana fama, Allah yaso babu wanda yasan da ita idan ba Fadwa ba, itama saboda ta ganta rannan ne.!

_Sometimes yarinyar na bashi tausayi, wani lokacin ta bashi haushi, yau dai tausayinta ne yafi yawa saboda shima ya fara bin layin da take bi yaji ya akeji.._ 😂

____________
Abisa dole ya hak'ura da kiran number Basheer don tak`i shiga sam, haka ya kwanta jiki a sanyaye babu k'wari, fargabarshi shine _"Kada dai ace wrong number ya bashi.!!_

_________________
Bayan su Hafsah sun koma, gida, d'aki tayi shigewar ta, tana ta tunani, so take ta samo hanyar da zata fara kudurinta akan Jamila. _Ki jawota ajiki._ wata zuciyar tace mata haka.
Kuma tabbas taga hakan don idan basu shak'u ba ko babu alak'a mai k'arfi a tsakaninsu irin ta da, babu yadda za,ayi ta iya aiwatar ta abinda ke ranta.
_Ya ilaahiy ka taimake ni._ Addu,ar da take tayi aranta kenan. Zuciyarta na k'ara hasko mata hoton Jamila a da da kuma yadda take a yanzu data ganta a yau.
_Dama can ana fad'a mata Jamila na zuwa unguwar, har gidansu tana zuwa, kawai dai wajenta ne bata zuwa._
Ta d`auki wayarta kamar zata yi wani abu da ita sai ta tuna cewa, ba ita ta amshi number Jamila ba, Jamilar ce kawai ta karb'i
tata Number.

Tana kwance, zainab ta shigo d'akin, da waya a hannunta, cikin k'asa da murya tace "Yaya ga Na'eem zaku gaisa a waya yace na baki."
Hafsah ta girgiza kai, alamar ba zata karb'a ba. Zainab tayi saurin katse wayar don kada a bata mishi lokaci ko Hafsah ta fad'i wata magana mara dad'i, ya jiyo.
Suka fuskanci juna Hafsah ta fara magana.
"Bana ce ki daina kula yaron nan ba."
Zainab tayi shuru ta sunkuyar da kai, haka kawai Hafsah bata son Na'eem ita kuma bata ga aibunshi ba.
"To zan fad'awa abbah tunda haka ne." Hafsah ta k'arasa fad'a.
"Haba Yaya wai me Na'eem din yayi ne.."?
Zainab ta fad'a cikin shagwaba.
"Ban sani ba, nidai nace ki rabu dashi."
Zainab ta turo baki sannan ta tashi ta fita.
_Duk da Hafsah bata fiya takura ba, amma bata barin k'annenta su fad'a halin da zasu cutu, haka kawai taji Na'eem bai mata ba, kuma don taga alama ba aure ne gabanshi ba kawai yana son ya b'ataw K'awarta lokaci ne._
_Shi kuma daya fuskanci cewa Hafsah bata yinshi, shine yake zuwa da siyasa, ko yaushe idan ya kira a waya sai yace a bawa Yaya su gaisa._
_Hafsah bata son hakan tana ganin ba zata zuba ido, k'annenta su fada irin halin da ta tab'a shiga ba shiyasa take tsaye kam akansu, duk wani motsinsu akan samari ta sani._

BASHEER
________________ B'acin ran Hafsah bai barshi ya zauna a gida ba. bayan sun dawo gida, yayi alwala ya fice, don ya tabbatar idan ya sake suka zauna zaman hira da ita, hirar Jamila zatayi ta masa, shikuma ba zai zauna sauraro ba, don haka daga masallacin, ya nufi wajen wata _snooker_ can bayan layinsu. Bisa Tsautsayi kuma, sai wasu suka fara cha-char baki har takai sun fara kokawa, akan musun _snooker._ Basheer ya shiga tsakiya, har da shi a masu rabon fad'an gashi wajen an cika. Lokacin kuma wayarshi na aljihun wandon shi ba baya, sai da komai yayi _settled_ sannan ya nemi hanyar dawowa gida, lokacin an kiran sallar isha'i.
Sai da ya shigo, gida, yayi alwala, zai fita ya laluba aljihunshi don yasa wayar a chaji, yaji babu komai.
Gun Hafsah ya nufa, tana palour tana cin abinci, _"Sister an sacen wayata fah._
"Ta zaro ido, a ina yaushe kuma."?
Gashi ban ganta ba, "Ina tunanin wajen snooker da naje ne."
Bata ce komai ba, tahau kiran wayar amma _is switched off_ ake ce mata itama.
_Basheer ya fice, kawai ya nufi masallaci ya barsu suna, jajantawa.._

📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*
♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄 *47*

*Da* safe Ukhasha, da kiran number Basheer ya karya, amma _still is switched off._
Wata irin zufa ce ta hau tsatstsafo mishi, _ya Ilaahi_ anya kuwa number daidai ce, kada fa ace _yaga samu yaga rashi._
Ya tuna cewa yana da d'aurin auren _JB_ dole ya tashi ya hau shiri. Yana toilet wayarshi nata ringing.
Har ya fito, kira na k'ara shigowa, ya duba, sunan _JB_ ne ya fito wato angon.
_UK me kuke nufi ne, ya zaku barni ni kadai gashi har na shirya banga ko dayan ku ba."_
"Kai Dallah can wanka nake, kaga sarkin zumudi dududu, k'arfe tara da rabi fa yanzu, zaka dami mutane."
_"Iyehh, Lallai ma UK wato kaima kabi layin su Mubarak kenan koh, kada ka manta ni yayanka ne yanzu."_
Ya shek'e da wata dariya, "Haha, gaskiya ne, dan rainin wayo."
_Please UK don Allah ka taho."_
_
"Okey ganinan Allah, k'arasa shiri zanyi kawai.
"Yawwa aboki, abokin gwauran taka."
"Hmm, Allah sai kasa na fasa, zuwa yanzu."
Ahh yi hak'uri, rufamin asiri.!!
Ukhasha yace,
"Kai da bikin naka ma, damuwa ya gadar min."?
_"Ahaba UK kada dai wannan matar, ta k'ara kiranka neh."?_
"No no no, ba ita ba, wata yarinya ce fah ranar yinin nan."
"Oh wai wacce akace ta yarfa ku koh."?
Suka shek'e da dariya duka.
Hmm, au kace har kaji labari, gaskiya su _NZee_ (_Nazeef _)munafukai ne.!!
"Ka bari kaidai ku nutsu don sai kun nemo min ita kaida amaryarka.."
_"Haha, UK ashe gaske ne, kenan ka zurma".._
Yai ajiyar zuciya. "Ya na iya.? Suka had'a baki _JB na cewa "Allah ne ya kamaka"_
Shima na cewa "Allah ne ya kamani ni."
Haha, kaima ka fad'a ko da kanka, amma babu komai aboki Allah ya sanya alkhairi.
To ya zakayi da 'yar kwailar can.
"Kai chab zaka b'atan rai wallah, kusan yadda zakuyi da ita dai."
_"Hmm, Allah ya kiyaye ka Aboki, amma akwai dan barwa.!_
Amin ango, bari na shirya kada mu b'ata lokaci.
An kammala komai anyi d'aurin aure, su Ukhasha ansha zirga zirga har zuwa lokacin kai amarya. Hidimar da suka shiga ne, yasa ya d'an manta da damuwar shi, don bai ma samu ya zauna ba. Allah-Allah yake washegari tayi, ya bujurowa da ango abinda yafi damunshi, wato inda zai sami
Hafsah..
Chapter 55 · 0% Book details