← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 88

Sashe 21

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*Adaidaita Sahu* (Keke Napep) suka tare suka yi wani d'an k'aramin Asibiti, da ita, aka duba ta sosai sannan suka bata magunguna, suka ce sai nan da kamar awa biyu zasu sallame ta..Sai wajen tara na dare suka dawo gida.. Jikinta duk shatar bulala, dak'yar tayi sallar Magrib da Isha'i sannan ta kwanta, mama na d'ankin a kusa da ita, don yau haushin Abba takeji. Don da suka dawo ma yana parlour shida su Mufida, amma ko kallonshi mama batayi ba. Banda sallamar da tayi a ciki-ciki.
Ita bawai laifin Hafsah ne bata gani ba, amma wannan dukan yayi yawa, sai kace wacce ya kama a gidan karuwai??
Tana d'akin har wajen goma sha d'aya na dare 11:00pm.
Ita ko Hafsah shiru tayi ta lumshe ido kamar mai yin bacci, tana jin kunyar mamanta, don bata so ta k'ara yin irin wannan kalan laifin ba, bayan abinda taga Abban yai wa maman rannan.
Sannan takaicinta shine,
'Tasan yanzu Abba zai mata dokar hanata fita..' Gashi bata da wata hanyar contacting d'in Yusuf, hawayen kewa suka zubo mata, masu zafi.. Ga jikinta da ya addabeta da zafi sai abin ya had'ar mata ya sabbaba ('Cause') mata, ciwon K
kai mai zafi wanda ya hana ta bacci.
Mama sai wajen 1:00am ta bar wajenta,.. Sai bayan nan ta d'an samu bacci.
Da safe tunda tayi sallah ta koma ta kwanta, tanajin hayaniyar su Zainab a parlour. Har wajen 10:00am, Sannan zainab ta shigo d'akin tace mata, "Yaya, wai mama tace ki zo kiyi break"
Ta d'aga mata kai.
Dak'yar ta iya mik'ewa saboda tsami da jikinta yayi,.. Duk k'annenta na tare da maman, yau akan dining ma suke, ta wuce ahankali, yaran suna, mata "Sannu Yaya" sai taji wajen na mata nauyi, mussamman da Mama keta aikin kallonta, sai ta tuna cewa bata gaida maman ba.
Cikin dashashshiyar muryarta tace, "Mama barka da safiya"
"Sannunki ya jikinki?, maman ta amsa mata cike da kulawa.
Ahankali take cin abincin, har suka gama, tana shirin mik'ewa Abba ya k'walo mata kira, cikin rud'ewa ta amsa "Na,am", ta mik'e a hanzarce ta nufi d'akinshi, ya gama karyawa, kwanunkan na gefen shi akan 'Tray' da shirin shi na fita daurin aure. tanayin, sallama tun kafin ta zauna yai mata nuni da su, ta sunkuya ta debe su, ta fita, kitchen ta kaisu tana fatan 'Allah yasa kiran da yake mata kenan'.
Ta dawo a salub'e ta durk'usa a gefenshi, kanta a k'asa saboda tana tsoron su had'a ido, cikin sanyin murya tace, "Abba ina kwana"
"Lafiya lau," kawai yace. Tayi shiru, shi kuma ya k'are mata kallo, sosai sannan ya bud'e baki ya fara mata magana.
"Ina kikaje jiyan"??
Ta yi shiru, saboda tsoron amsar da zata bashi take,
Ya daka mata tsawa,
"Ba zaki fad'amin ba"..
Jikinta ya hau rawa, wallahi babu ko ina..
K'arya zaki min, zan tattaka ki anan wajen, ki bud'e baki ki min magana, shashashar banza"..
Ya fad'a yana shirin mik'ewa ya d'akko bulala.
Cikin hawaye ta fara magana, Don Allah Abba, kayi hak'uri wallahi, bansan fita zamuyi ba, shine ya ja motar,..
Ina kika je na tambayeki,"
"Park". Me kikayi acan?? Wallahi babu komai,"
Wato saboda baki da kamun kai koh, ? To yayi miki kyau, ban tab'a yi miki dukan da kika suma, bane shiyasa. Ya nuna ta da yatsa, wallahi wallahi Hafsah ki shiga hankalinki akan abubuwan da kika k'irk'irowa kanki, idan ba haka ba, zakiyi mamakin abinda zanyi miki, shashasha kawai." kuma daga yau kada na k'ara ganin kinfita ko da k'ofar gidane, ko makaranta ma kin daina zuwa!!"
Ta d'ago a razane ta kalli, abban, wanda uwar hararar daya galla mata, yasa tayi saurin mayar da kanta k'asa.
"Innalillahi, shikenan ta, kad'e ta jawo wa kanta, Abba ya hanata zuwa school, babu batun, karatunta kenan? saura fa sati d'aya su fara 'WAEC' , yanzu ya zatayi kenan, babu zancen fita? Wane irin k'unci zata shiga.??
'Zufa ta wanke mata fuska, babu shakka zata iya cewa k'addara ce tasa Yusuf, ya fita da ita, banda haka, me sukaje yi wannan waje?.. Su basu sai komai ba, hasalima, a gurin Yusuf, baiyi yunk'urin tab'a ta ba, bare tace alhakin hakan ne' Kawai Tsautsayi dai.!!
"Tayi shiru, tana nazarin rayuwar da zatayi babu fita.
Wallahi idan baki sauya tunani ba, zaki matuk'ar shan wahala a wajena."
Tashi ki fitarmin "ana!
Kalaman Abba, kenan da suka katse tunaninta.
"Cikin kuka tace Don Allah kayi hak'uri wallahi bazan.."
Ya kuma daka mata wata uwar tsawar "Fita nace",
Ta mik'e jiki babu kuzari ta fita.
Tana fita parlour, mama ta ga yanayinta, sai ta mik'e sai d'akin Abban,..
Ta nemi kujera ta zauna.. Fuskarta fal da takaici.
Abba ya karanceta tsaf, kafin tayi magana ya riga ta.
"Amina kin bani, mamaki, wato bazatayi laifi a hukuntata ba koh,.. kin fiso abarta tayi tayin abinda taga dama babu kwab'a.. Bakya fargabar abinda zai je ya zo Kennan."
"Ni ba cewa nayi kada a hukuntata ba, amma ai dukan da kayi mata yayi yawa, macece fa"
Abba yai murmushi mai sauti, kina nufin kin fini sonta ne, ko kuma me?
Tayi shiru azuciyarta tace "Ai hakanne" _lol_
'Jin tayi shiru ya cigaba da magana cikin son fahimtar da ita, don ya fahimci itama cikin fushin take, ba zata tab'a fahimtarshi ba idan shima ya nuna mata fushinshi.'
"Amina, kullum fata na shine in sauk'e nauyin hak'k'inku dake kaina, Hafsah fa 'yata ce, bazan yi abinda zai cutar da ita ba, komai ina yin shi ne don ta sami kyakykyawar tarbiyya, ina roko'nki idan bazaki tayani ba, to ki daina adawa da duk hukuncin danayi mata."..
Ta d'ago da niyyar tayi magana amma ya hana ta, ta hanyar daga Mata hannu"
"Dakata, wallahi kema na tabbatar jiya bakiyi baccin kirkiba, saboda tunanin meyafitar da ita, ita da wani?.. Ki bar yi mata shaidar tana da hankali ko kamun kai, ni bana zarginta da komai amma, wallahi _ba,a shaidar yaran yanzu..._ kuma kema nasan daga yanzu hankalinki bazai k'ara kwanciya ba matuk'ar tafita daga cikin gidannan har sai ta dawo."
Mama tayi shiru tabbas kalamashi gaskiya ne'.
Kuma sunyi nasarar sauke fushinta akanshi, don haka ta shiga bashi hak'uri,
"Kayi hak'uri to, na fahimceka, insha Allah bazaka k'ara jin bakina, akan lamarinta ba"
Ya girgiza mata kai, "A,a ai 'yarki ce, kema kina da hak'k'i akanta,.. kiyi ha'kuri kema, ki dinga yi mata addu,a kawai."
Ta d'aga mishi kai, "To in sha Allah",.. Ni dama kawai dukan da ka mata ne, ya tsoratani kuma kasan fa duka baya gyara"
Yayi murmushi harda jijjiga k'afa "Nasani"
Cikin nutsuwa ya kuma ce mata,
"Na hanata fita, koda zuwa makaranta ne, don haka kisa mata ido, sosai.
"Tom, shikenan"
Bata da musu akan matakin daya d'auka..
Kuma ta fahimceshi sosai, saboda haka ta bar wannan zancen, ya miqe zan fita wajen daurin aure Adawo lpia Allah y tsare,
ta miqe don rakiyar shi. Kmr ban ita ke fushi da shi ba..
Hafsah ta, dawo rayuwa kamar mujiya acikin gidan, kullum tana d'akinta, babu dai wanda yake k'yararta acikin gidan amma duk ta tsargi kanta, kuma babu wanda ya damu, da hakan.
Akan idonta su bashir suke shiryawa su tafi makaranta itako ko oho, sai bashir dake Cemata "Yaya 'yan ajinku suna ta tambayata nace musu baki da lafiya ne.
'Hakan shi yafi damunta, gashi tun ranar nan, Abba, yayi watsi da ita gaisuwar ta kawai yake amsawa. Gefe kuma kewar Yusuf da tunaninshi sun addabeta, hakan yasa tayin wata 'yar rama, tayi bak'i.'
Haka har sati ya zagayo ranar lahdi, kuma washe gari zasu fara exam, kuma Abba yasan da hakan, Amma, har ya dawo babu wata magana daya yi mata...
*Kuyi haquri da wannan*👏🏼👏🏼
*Hajiyar ku ce*👌🏻
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
💔💔

Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members.*

📄 *25*
Chapter 21 · 0% Book details