← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 88

Sashe 40

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

♥️♥️♥️♥️ *ZAZZAFAN SO* (Masoyin k'warai) *Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)* 💔💔 *By* *Karima Tijjani Mansur* *(Hajeeyah Khareemerh)* *Dedicated to unique in your love heart* 📄 *37* *Sai* bayan magriba HAFSAH ta koma gida.. Mama na kitchen ta wuce parlour inda ta tarar da abin murna.. Basheer neh qaninta ya zo gida hutun makaranta. Yana ganinta ya taho da murnar shi "Oyoyo aunty nah.!!" Ta saki fara,a saukar yaushe Basheer.?? "Da yamman nan." Ya fada tare da amsar jakar ta suka qarasa shiga cikin parlourn." Kujera daya suka zauna ta riqe haba tana kallon Basheer. "Oh ni Basheer sai wani girma kake haka.? Yayi dariya Yana shafa dan gemun shi daya soma taruwa, Yasan shi ta gani shiyasa tace mishi haka. "Mene ka wani tara gemu sai kace wani babba."? Murmurshi yayi yana kallonta qasa- qasa yace "To ai shi dinne yaya." "Hmm baka da kunya fah.!! Mama ce ta shigo parlour, "To sarakan hira an hadu koh?? "Nace, an kira sallah"!! Basheer ne ya fara miqewa "Aunty bari na dawo akwai hira fa." "Okay Basheer itama ta miqe ta nufi hanyar dakin ta." Yau wani irin farin ciki takeji, tana son ta ganta ita da Basheer suna hira shiyasa bataji dadin tafiyar shi karatu wani garin ba.. Duhu ya fara yi lokacin daya dawo suna zaune a parlour dukan su, Hafsah, Mufida, Amira, da Zainab mama tana toilet. Hafsah kallon Basheer kawai take tana mamakin girman shi. "Even She's just 25 knocking 26 shi kuma 24 yake." 'Ya miqe da wani irin tsaho irin na abban su sai farar fatar mamansu, cika da kyau sun bayyana agareshi ga wani dan gemu daya ajjye dayake qara mishi kyau. Komai nashi cikin yanga yake dole ya burge yan mata. "How time fly? ta fada a zuciyarta yaushe tayi candy ma? Lokacin da tayi candy shekarar ta 18 cif. Ta sami tsaikon shekara daya bata shiga Jami,a ba (Tuna baya wato zamanta gidan Mama) Yanzu haka ta kammala digirinta a fannin _International relationship_ sabanin burinta na son zama lawyer. tna wata na qarshe ashekarar service dinta wanda takeyi a wani gidan television. Basheer ya nemi guri kusa da ita ya zauna. "Aunty nidai hira nakeso muyi sosai." Ya kalli su mufida. "Amma Nidai bana son yaran nan suji mana hira." Amira dake danna wayar ta ta dago ido ta kalleshi, sannan ta kalli mufida suka kwashe da dariya har da tafawa." Ya miqe yana hararar su, yaja hannun Hafsah suka nufi dakin ta. Yana matuqar ji da ita. "Yaya ni nama rasa ta ina zan fara."? Ya fada bayan sun zauna a dandaryar qasa, kan carpet din dakin. "Meya faru ne Junior naga kamar a damuwa kake"? Ya shafa gashin Kanshi daya taru yake ta faman kyalli. "Hmm, babu komai boko ce kawai tamin yawa." Suka kwashe da dariya dukan su. Sannan ya dora cikin qasa da murya. "Sai wata Christian girl data takura min." Hafsah ta riqe hab'a. "Uhum? Tace dashi. "Yes Aunty, yarinyar mayya ce wallah ta takuramin she can even comes to my room fah everytime." "Even at n night"? Hafsah ta tambaya tana zaro ido." Ya jijina mata kai. Yes sister, she's beyond your expectation fah ko tsakan dare ne zata iya zuwa min, rannan fa cemin tayi dole dakina zata kwana fah." Hafsah ta riqe haba tace "Uhum?? "Ya kayi kuma.?? "Hum ya sauke ajiyar zuciya sai da na mata jan ido ta fita." Ya jaro wayar shi ya nuna mata photon ta, "See her, wai blessing sunan ta. Hafsah ta qare mata kallo sannan ta miqa mishi. Class dinku daya"? Noo amma dai faculty dinmu daya civil engineering nake, ita kuma electric amma we're in the same level. Level 3 take nima haka." "Hmm." Inji Hafsah. Yanzu ya zakayi da ita. Mafita nake nema aunty nah. Ya fada da marainiyar murya, "Allah bazaki gane nacin yarinyar ba, ni da na zaci abin nata wasa ne, wai a haukar ta aure na zatayi." "Hafsah ta toshe baki tana dariya." Bashir ya danja siririn tsaki, ya ja kwafa yarinyar class less ce sam ba aji." Hafsah ta kalleshi "Nidai suggestions dina shine.. Bashir ya bada gaba daya hankalin shi akan ta ya zaci wani abin arziki zata fada. Fada min aunty mene ne, ya fada a zak'e (cikin zaquwa/ so eagerly) Hmm Tana yar dariya da siririyar muryarta tace, zan fada a labaran mu, _A level 300 Muslim student proposed to a Christian his level mate)..._ Bai bari ta qarasa ba ya tareta cikin damuwa. Haba aunty Don Allah ki maida abin serious, wallah am seriously worried, tana hanani karatu fa kuma bana son Abba fa ya sani." "Hmm ga mafita ma, Kawai mu fada ma abban.. "Oh my God.!! Ya dafe kai. "Plz Yaya ki bari mana." Tayi 'yar dariya ta gimtse. "Okay, me kake ganin zaa yi. Uhum?" Yawwa ni cewa nayi Kodai na baki number nata ki kirata kici mata mutunci, as wacce aka zaba min agida za,a aura min."? "Umm.. Bari muga lemme think deeply gaskiya zanyi tunanin wani mafitar. "Okey yaya ta thank you. Tayi murmushi. Hmm Basheer mai 'yan mata. Shima dariyar yayi "Haha wallah Yaya na rasa what's wrong with 'Yan mata yanzu kowa tana son ka, banda ita akwai wasu fa.. Kawai su gwara Muslim ne kuma basa takuramin as she do." "Um kace kana sonsu kawai." "Noo Yaya kadan ne suke burge ni cikin su." "Hmm kaji ba." Ta fada, Sannan ta mayar da muryata serious tace, "And plz Basheer don Allah don't ruin any girls life, and not to broke her heart kaji, duk wacce baka so ka rabu da ita Kawai salin-alin bubu wulaqanci ko bata lokaci. Ya kalle ta a sanyaye yana gyada mana kai, yasan abinda ta tuno, yasan dalilinta na fadar haka, yasan ta dan-dana." "Kada ki damu Yayata ba haka nake ba." "Thanks Yayana!!" ta fada tana murmushi. Shima murmushin yayi jin tabashi girman, duk da yasan tasan yana da son girma. Kallonta yayi shima, cikin wata nutsuwa, ya gyara zama sannan yace, "Yaya Kema akwai maganar da na keson muyi dake Don Allah." Ta tattara dkukan nutsuwarta wajen shi, sannan tace cikin sanyi. "Wacce magana ce haka Basheer."? Ya danyi yar ajiyar zuciya, "Um ba wata magana bace fa mai tsaho, Kawai dai tambayar ki nake son inyi. "Ina jinka toh." "Don Allah yaushe zakiyi aure.!"? Ta ke Yanayin ta ya chanja, "Basheer aure kake tambayata koh, ka gaji da gani na agidan koh, ko na tare maka damarmaki (dama) dayawa ne."? "Calm down, my dear aunty, ya fada cikin qasa da murya. "Ba fa abin zafi bane, I just asked you ne saboda mu fara shirye shirye, ya qarasa fada yana dan murmushi. A tayi ajiyar zuciya a hankali, "Ai na zaci ka gaji da ganina ne, fah." "Rufamin asiri ya fada yana zare ido, ya nuna kanshi wane ni in gaji da yayata." "Dariya yaga tayi ta jin dadi." Duk da hankalinta daya kwanta amma dole ne ya qarasa mata zancen, don yana son ta dauki zancen da muhimmanci, don haka yace. "Aunty kinsan da na dawo me Abba yace.? Ta girgiza kai. "Ya ganni na girma, shine ya cewa Mama wai da mace ne ni tuni na isa aure har da yarana." Nace, "Haba Abba a village dai, shine yamin dak'uwa, wai a gidan nan ma haka neh." Aunty kinsan na tarar dashi kafin ki dawo ya fita. Inaji yana qara wa mama bayani after nabar wajen, "Wai Kema yaga shuru bakya wani sauraron kowa bai san meke damunki ba, Gashi even mufida ita ma ta isa aure fah." Ya sauke waccen maganar, har yanzu idonta na kashi ko motsa su batayi..ya dora. "Plz Yaya I don't say that kin gunduri Abba ko mu, infact ma ba zamuji dadie ba ki tafi ki barmu, but ke macece, shiyasa kika ga hakan." Ya daga hannun shi alamar roko. "Please before Daddy talk to you about it, please kiyi making wani decision akan abin kinji, Allah nasan baki rasa masu sonki bafa kawai baki bada fuska ne." Kinji my beautiful aunty ki daure ki manta da komai, forget your fast, wani YUSUF and wata Basma, whatever ma yanzu you're beyond their classes, ki manta dasu plz." Sai da ya ambaci YUSUF sannan yaga tayi murmushi. "Hmm Basheer kenan, azaton shi YUSUF ne ya hanata kula wasu?? Ita ko wacce irin zuciya ce da ita da zata iya riqe abubuwan shekara wajen bakwai baya, _Broken heart Time_ Haka ta bawa lokacin suna. Murmushi ta kuma yi sannan tace "Hmm Basheer kenan, naji toh naji don't mind zaka ganni da aure gobe goben nan." Suka kwashe da dariya, ta fadi hakane don kada ya dauka zancen nashi ya sa mata damuwa wanda a badini ba damuwa kadai ba, har tunanin baya sai da ya dawo mata. "Wato tunda Abba ya sake ya bayyana haka to Lallai abin yana ranshi." "Aunty nah, amaryar gobe bari na barki toh.." Ya miqe yana cewa I think Abba ya dawo lemme go and tell him gobe yana da daurin aure." Ta kaiwa bsyanshi duka ya fice yana cewa "Amarya- Amarya. Bata da zabi illa ta bishi parlourn ita ma Don haka ta mike. Ahankali take tafiya, tun daga nesa take qarewa mazauna palourn kallo, so take ta karanci, halin da suke ciki.' Abbansu ne, wanda a kujerar farko wacce take facing TV, kana ganinshi shima girma yazo mishi a qallah zaiyi shekaru 55 zuwa 57, cikar kamalar shi na nan sai ma abinda ya qaru. Akwai cigaba sosai cikin al,amran gidan a yanzu fiye da shekarun baya, kama daga kan tsarin gidan daya samu gyara sosai, akwai qaruwar arziki duk da yana dab da retire baifi saura 'yan watanni ba, bayan haka ya shiga Fagen siyasa, kuma babu laifi ana damawa dasu, suna da kyakykyawan zato su sami nasara a zab'e mai zuwa, Wanda idan hakan ta faru, gwamna zai iya bashi matsayin kwamishina (commissioner) ko kuma wani mai bashi shawara wato (Adviser) Mamansu ta qara, girma da gogewa ta zama wata babbar mace, akwai cigaba sosai akan fannin kasuwancin da take yi. Kana kallonta zaka gane babbar macece da take cikin kulawa, da kuma tsari mai kyau, kuma a tsaye take kyam kan al,amran Gidan ta.
Chapter 40 · 0% Book details