← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 88

Sashe 80

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin yanayi na takaici da bak'in ciki Hafsah ta shiga wanne irin dama mutumin nan ya samu da zai dinga mata irin wadanan zantukan. Wasu sharadai akan abinda ya shafi rayuwarta."? Me ya maida ta shi yake iko da ita ko me har yake sa mata ido da wasu zantukan shi kan wai ya ganta da kawaye.. Yarinya ce ita da zai mata wannan ikon da a gida ma sam ba'ayi mata shi."? Nufin shi ita mutuniyar banza ce kenan.!!!
Yanayinta ya sauya har wani kankance ido take, so take kawai ta amaryar da abinda ke ranta, so take ta sosa mishi rai yasan bafa classless bace ita da zai dinga mata irin wannan abubuwan ko dan yaga tayi saurin aminta dashi. Haushin kanta da nashi ya turnik'eta ta fara magana cike da tsiwa tana magana wata na ingizo wata saboda ta shak'a da yawa.

"Ban gane me kake nufi ba!! Ya zaka dinga min magana kamar kana da wani iko dani."? Nace maka dole kayi mu'amala danine bare ka kafa min sharadai na mutanan da zanyi mu'amala dasu ko kana da iko dani ne har kake fadamin na saki aiki nah saboda kai ke da ikon komai a kaina ko kai kasakani tun farko."??

Ya kasa samun damar mata magana saboda maganganun da take yi. shima sai yaji ranshi ya b'aci.

Dama haka yarinyar take."?
Daga yazo mata da magana cikin maslaha shine zata dinga fada mishi maganganu irin haka."?

Ita ma ta zaci zai tanka amma taji shuru sai itama tayi tsit ta kama kanta.

_Ni kike fadawa wadanan maganganun ko Hafsah."?_
Yasa kara jin takaicin shi to mene don ta fada mishi _da gaske ai bashi da ikon akanta."_
"Nagode ya sake ce mata sannan ya kashe wayarshi."

Ta ajiye wayar a gefe tayi shuru tana tunani. "Ya bata mata rai matuk'a amma zuciyar ta ta kasa nutsuwa da maganganun data fad'a masa.

Aduniya bata son a dauke ta amatsayin mara mutunci ko kuma mara kunya.

Amma ita kanta tasan fusata tayi maganganun shi ne suka ingiza ta don tana ganin bashi da hurumi da al'amran rayuwarta da zai dinga tuhumar ta kan batun mutanen da take mu'amala dasu har gwara batun aiki wannan kamar shawara ce ya bata.

Ta dafe kai tana son ta tuno irin maganganun data fada masa amma sai ta kasa. Ta damu kanta kan abin kuma ta rasa dalilin damuwar.

Kusan awa d'aya dayin hakan kiran abbanta ya shigo wayar. Ta dauka da hanzari. Taji shi cikin farin ciki sosai, bayan sun gaisa yake ce mata.
Munyi kewarki sosai Yaya..gashi kinyi zaman ki ke..ki dawo yau mana kinga Bashir gobe zai koma makaranta fah."
"Da gaske Abba."? Ta tambaya bata son Bashir ya tafi.
Ki dawo kedai Yaya zanyi miki wani albishir nima." Cikin farinciki tace toh Abba gani nan yanzu zan taho ma."
To Allah ya kawoki lafiya.!!
Matar auncle abdullah babu yadda batayi da Hafsah ta zauna ba zuwa la'asar amma taki haka tayi wanka da tsakar ranannan. Auntyn ta bata wasu doguwar riga tasa tunda batazo da kaya ba.

Tayi mata sallama cike da zumudi ta dawo gida.
A dakin Bashir ta tsaya. Ya dake labulen yana ta shirya kaya.
Yadda taga farawa fara'arshi abin ya bata mamaki gashi sai sai kallon ta yake kamar bai santa ba.
Ta gaji ta tanka.
Bashir wai fara'ar mene haka kai da zaka tafi sai faman kallona kake kamar baka sanni ba."?
Bashir yayi murmurshi kawai.
Zaka je ka tarar da sisin ka kana kallon mutane."
Sukayi dariya ita dashi.
Sannan ta tambaye shi "Abba na ciki."?
Yace mata, "A'a ya dan fita amma ba nisa yayi ba."

"Okey tace, bari na shiga cikin."
Tana shigowa taga kowa ya rude ana "aunty.!! Abinda ya bata mamaki shine har da mama.
Ita dai ba dadewa tayi bata nan ba bare ace.
Ta tare su itama da fara'a ta gaida mama sannan ta nemi waje ta zauna.

Suka ma sannu da zuwa suma. Babu jimawa Zainab ta karasa girkin da take. Ta zubo musu su duka sukaci.
Bashir ma ya shigo aka hadu ana hira sosai ana raha.

Sai daf da sallar la'asar Abba ya shigo bayan yaci abinci babu jimawa aka kira sallah suka fita shida Bashir sukayi sannan suka dawo Abba yayi dakin shi sannan yasa aka kira mishi Hafsah, tana jin kiran ta tuno da albishir d'in daya ce zaiyi mata don haka ta mike da sauri ta nufi dakin. Sai kuma ta ganshi shida mama su biyu a d'akin ta zauna a kasa kafin tace, "Abba gani."

Yayi gyaran murya tare da gyara zama yayi mata wata tambaya da ta sata cikin mamaki.
"Yaya banda Ukhashatu waye yake zuwa wajenki kuma.?
Tayi dif tana kalli mama sannan ta kalleshi shi abban.
Jin batayi magana ba yasa yace.
"Shikenan koma mene ne lokaci ya riga ya k'ure."
Ina fatan zaki karb'i komai a yadda yazo.
Mamaki ta shiga na irin kalaman Abban. Me yake nufi kada dai Ukhashatu ne ya hada ta da Abban. Duk da tasan bai taba ganin abban su bama.
Tana wannan tunanin taji Abban na cewa.
Yaya kinsan burin ko wanne iyaye shine 'su aurar da 'ya'yansu."
Hakika na dad'e ina saka ido a kanki da yadda kike Mu'amala da mutane kuma naga kinki bada damar da har wani zai shigo har ya nemi aurenki.
Sai dai ina muku addu'a dukan ku kan Allah ya baku mazaje na gari. To dai ganina da Ukhashatu na tabbatar addua ta ta karbu nayi fatan Allah yasa kin aminta dashi.
Kiyi hakuri Hafsah na tabbatar cewa lokacin aurenki ne kawai yazo shiyasa Allah ya kaddara komai ma. Bani ne na sa ayi haka ba iyakaci na nemi ganin iyayenshi ne sai kuma gashi cikin ikon Allah daga zuwansu sun nemi na basu aurenki kuma na basu.!!
Ya dire dogon zancen anan don hutawa. Yayin da Hafsah ta shiga motsi da kafafuwanta idan ta fahimta Abba ya bada aurenta ga Ukhashatu kenan."?
Ya akayi abin ya faru haka kamar a mafarki wai yau itace akayi haka ake cewa an bada ita. Maganar Abba ta dakatar da tunanin ta inda yake cewa.

Na ganshi rannan nace inason ganin iyayen shi cikin ikon Allah sunzo jiya kuma sun nemi a bawa dansu ke...manyan mutane ne su, saboda hakane da karfin Allah da kuma yak'inin ba zaki bijure min ba na karbi kudin aurenki naira dubu d'ari. Kuma in sha Allah sun nemi asa lokacin aure wata hud'u."

Hafsah nason ta d'ago ta kalli Abba amma kuma ta kasa _tanajin nauyin shi._

"So take ta tabbatar da gaske ne Abba ke fada mata ya bada ita ga Ukhashatu."?

Ki amshi zabin Allah kinji Hafsah Allah ya yi miki albarka ya kai mu lokacin."

Mama tace "Amiin sannan itama ta gyara murya ta shiga nata jawabin.
"Nidai abinda zan fad'a miki shine "Kiyi hakuri kiyi biyayya ke macece lokacin ki takaitacce ne Hafsah shekarunki sunja ki duba kannenki su kansu sun isa aure. Don Allah kada ki watsa mana kasa a ido. In sha Allah zakiyi alfahari da zabin mahaifinki."

Hafsah tayi shuru tana d'an nazari.
_"Ita kuwa me iyayen ta zasu nema wanda bazata yi musu shi ba."? Ko da ace wani can suka dakko ba Ukhashatu ba suka bata ba zata iya yin musu ba, bare kuma suna da hujja, itace ta kawo Ukhashatu har Abba ya ganshi."_

Abba da mama suka katse mata hanzari wajen cewa. "Kiyi magana yadda zamu tabbatar kin aminta da zab'in mu.!!"

Abba ya kara da cewa, ban yanke hukunci ba sai bayan binciken da nayi kuma anyiwa yaron kyakyawa shaida nima kuma ina mishi kyakyawa zato.!!
Kiyi hakuri kinji yaya."

Ta kara kasa da kanta a kunyace tace 'Abba nagode Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Ta fadi haka ne kawai don ta kori shakkun su akanta amma a lokacin ba zata iya cewa ga taka takamaimai yanayin da take ciki ba, banda na tunane tunane barkatai.

Fara'a ta bayyana a fuskarsu suka shiga sa mata albarka da fatan alkhairi.
Nauyinsu yasa ta mike babu shiri ta fita. Ta barsu cikin farin ciki.

Ita kuwa tunanin yadda suka rabu da _angon_ ne ya dawo mata sai kuma ta tuno da salon da ya dawo kiranta dashi daga shekaranjiya wato _amarya_ Sai ta fara jin wani irin tausayi da kunyar shi don sai data baro gabansu amma _emotion_ din ya motsa.. Allah sarki ashe dama gani yake babu wanda ya kaishi iko da ita shiyasa ya dinga mata wadanan zantukan."? Amma me yasa yaki fadamata cewa ta zama mallakinshi."?

Ta fada tunanin tuhumar kai kan abinda tayi mishi, ta takura kanta har saida ta fidda wata yar kwalla. _Da wanne ido zata kalleshi... shikenan ta zubar da k'imarta a idon shi zai dinga mata kallon mara kunya.. me ya kaita ma tayi mishi haka."?? A yadda take so bazata taba barin wata b'araka ga mijin aurenta ba yadda zai dinga jin ta mishi ba daidai ba tun kafin a shiga daga ciki..bata son ya sanya shakku a kanta._

Amma inaa aikin gama ya gama.!! Tana nan jigum tana shawarwari yadda zata gyara abinda ta bata. Gashi sam bai kuma neman ta ba tun d'azun. Gefe guda kannenta sun dame ta duk wani motsi nata suna ta kiranta "Amarya!! Ko kuma aunty Amarya.!!
Tana ganin kalar farincikinsu har take mamakin ashe dama haka suka damu tayi aure."?

Duk bayan minti sai taji fargabar da wanne ido zata kalli Ukhashatu."?
Wata zuciyar ke fada mata ta kirashi ta nuna kamar wani abu bai faru ba. Amma sai ta kalubalenci hakan gani take wannan kamar _nade tabarmar kunya da hauka neh"!!_

Ya dace tun farko daya kawo mata zantukan ta bishi a hankali (ta boye fushinta) Sannan cikin hikima ta bishi da _toh din da ba'a aikatawa_ amma sai ta nuna ita macece mai aji kuma bashi da hurumin yi mata haka.
_Kuma idan zata kalli zancen shi ta wata fuskar tabbas ya fada mata gaskiya ne Basma da Jamila kowa ya gansu tabbas zai sa musu a alamun tambaya daga yadda suke yanayin shigar su._
Chapter 80 · 0% Book details