← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 88

Sashe 51

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta farka ma hakane, taji zuciyarta tayi mata nauyi, maganganun mama sun tsaya mata a rai, a hankali ta fara hango gaskiya a cikin su.
Yusuf? Shine ya kashe mata waya.."? Jin cewa ita ta kira shi..? To wanne irin mantawa yayi da ita haka.. Lallai tabbas ya nuna mata baya buk'atar ta. Nan take kishin kai ya shiga zuciyar ta, taji aranta tabbas ita ma abu ce mai muhimmanci ba _Banza ba._ don haka ta sawa ranta cewa ba zata k'ara neman sa ba, matuk'ar bashi ne ya neme ta ba. Basma kuwa zata barta da Allah, don tasan komai lokacine, kuma alhakin ta bazai barta ba.
Kwanaki suka shud'e mama ta daina yi wa Hafsah magana mai kama data Yusuf ko makamancin haka. Gashi ita kuma Hafsah a kullum maganganun mama suna mata yawo a zuciyarta, ta rik'i wasu daga ciki, misali addu,a, da kuma daukar kai da muhimmanci, sai kuma muhimmanta lokaci, ahankali kuma da taimakon Allah, da amfani shawarwarin hazik'ar mace, wato _Haj. Nafeesah_ a hankali taji komai yana raguwa daga cikin zuciyar ta, har zuwa yau da zata iya claiming cewa babu d`igon son Yusuf ko ragowar damuwar shi aranta, ya zama tarihi, abin ya na bata dariya idan ta tuno lukutan, babu kamar ma irin musayar kalaman da Basma sukayi a text ita da Fateema a zuwan Hafsah ce, sai bayan ta fara dawowa hayyaci, Fateemah ke bata labari.
Zaman wata 3, tayi gidan mama wanda har Abba ya gaji dashi, tana zuwa gida, amma babu kwana, ita kanta tayi kewar komai, tana ganin tarairaya a wajen mamanta.
Sanda ta cika wata biyu, a iya cewa komai ya saitu, nutsuwar ta ta dawo, to lokacin kuma mama ta nemi da a barta tayi azumi anan, tunda yan kwanaki kawai suka rage.
Daga baya kuma, mama ta dawo da ita gida, godiya kuwa sara wacce, Alhaji Habib Hamid, zaiyi wa mama, yayi sai dai fatan alkhairi, don kud'i ko wani abin duniya, sunyi kad`an.
Duk wani labarin zaman gidan da Hafsah tayi da yar gwagwarmayarta mama ta bawa mamanta labari. Sannan ta mik'a ledar kyautar graduation d`in Hafsah wacce Yusuf ya bayar ga maman tare da cewa, "Ki bata sauran ta amfana kawai ita kuma wayar ki mikata ga Abbanta duk ranar da yayi niyya saiya bata a sanda yaga ya dace ta mallaki waya. _"Ikon Allah wai yaran yanzu sun fi bawa soyayya muhimmanci fiye da komai a rayuwa.!!_
Allah ya shirya mana su." Inji aunty Nafeesa, mama tace "Amin.
Ta karbi ledar duka, da niyyar bada kayan duka
abban da hannunsa ya bawa Hafsah, bayan sun gama hirar _yaushe gamo_ a d'akin sa, ya cire wayar, ya bata sauran. Bata ga amfanin su wajenta ba, tana baro d'akin ta bawa zainab agogon, ta bawa Ameera kuma turaren, tayi cilli da greeting card d`in mufida ta d`auke. Akan idon mama, tana murmushi zuciyarta tana godewa Allah.
Hafsah ita kanta tasan rayuwarta ta chanja, ta girma, kuma yanzu shine lokacin da ya dace ta maida hankali Don gina gabanta. ( _feature_) Tana gode wa mama, da ta tsamo ta daga garari acikin wad'annan shekarun nata, da lokacin ta kassara rayuwarta to da babu, wani zancen ta yanzu, don da bata tsinana komai ba a rayuwar, da tuni ta zama abar nunawa. Yanzu kuwa ita ce da digiri, guda aka, tana shirin karbar _certificate_ dinta na NYSC, kuma idan Allah ya taimake ta, zata fara aikinta.? Wai don ma ta bata shekara d'aya, wajen gyaran jarabawa, ( _da ke akwai Matsala a result d'inta na farko._) Lokacin Abba yayi amfani dashi wajen kaita makarantar koyon _computer,_ don rage zaman banza.
A irin haka ne wata ran a hanya takan hadu da Yusuf ko Basma ko kuma dukansu, sai dai a kalli juna kawai, Yusuf ne ma ke kokarin boye kanshi baya son su had'a ido, ita tausayi ma rayuwarsu take bata, daga baya kuma lokacin ta fara makaranta take jin labari yusuf d`in ma yabar k'asar ya tafi k'aro karatu.
Alhamdulillah Allah shine abin godiya. Haka Hafsah ke fad'a bayan ta dawo daga wannan doguwar tafiyar tunanin.
Zancen daya tsaya mata arai kuma shine zancen Bashir, Tabbas gaskiya ne, amma zata sanya tunani da hankali sannan da addu,a wajen samun abokin rayuwa na gari. Ta duba agogo k'arfe d'aya har da kwata, mamaki ya cikata, gashi idanunta sun yi nauyi, ta fara jin bacci sosai, amma tana son ta tashi ta roki Allah alkhairi a rayuwarta, don haka sai da tayi sallah raka,a biyu sannan ta kwanta.....

📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*

Not edited might you face typing error!!

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔

*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*

📄 *45*

*UKHASHA*
_______________
*UKHASHA* ABUBUBAKAR (KHADI) shine cikakken sunan shi, mahaifinshi kuma, ( _Khadi Abubakar_) Babban alk'ali mai rik'e da muk'amin _Grand Khadi_ a babbar kotun Shari,ar muslinci. Sannan kuma limamin masallacin Juma,a ne.

Abubakar Khady, d'a ne a wajen malam _Na,allah,_ shahararren malami, masanin addini, wanda ya rasu shekaru ashirin da suka wuce. Ya bar mata hud'u da 'Ya'ya goma sha hud'u bakwai mata, bakwai Mazaa, mahaifiyar Khady Abubakar Itace uwar gida, kuma 'ya'yanta yawanci sune manya don babu wata tazarar shekaru tsanin aurenta dana abokiyar zamanta, saboda haka yaran nasu suke tashi kamar ( _sakwanni_) babu tazarar shekaru mai yawa tsakanin su. Sauran matan sun zo daga baya, wad`anda su kuma Allah bai basu rabo a cikin gidan ba, sai dai suma sunzo da nasu yaran daga wani wajen, duk sai aka zama d'aya babu banbanci, saboda had`in kai da yake zaunanne a gidan har kawo yau ana zumuncin, har takai acikin 'ya'yansu idan ba manyan ciki ba, basa sanin cewa ba kakansu d'aya ba.

A D'akin su Khady Abubakar, malam _Ayyuba_ ne babba, kuma shine ya gado mahaifinsu sosai, ma,ana ya gado _malintar._ Sai kuma _Khady Abubakar_ shine na biyu, sai alhaji _Auwal,_ wanda suke kira da (Baffa) Sauran duka mata ne, Haj. Zainab Haj,
Rukayya, Haj. Binta, sai Hajiya, Rabi, dukka suna da aure da albarkar 'ya'ya wasu suna zaune a garin nan, wasu kuma a wasu garuruwan, kamar sokkoto, zamfara da sauran su. 'Ya'yan d'aya d'akin, su kuma mazan ne su biyar, mata kuma, su biyu, acikin mazan biyu sun rasu a shekarun baya-bayan nan, sumbar iyalai da yawa.

Wani abu daya k'ara wa family d`in yawa shine duk cikin mazan babu mai mata d'aya banda _(Baffa_ na gadon k'aya,) kuma dukkansu daga matan har mazan, 'y
Ya'yansu zasu kai takwas zuwa goma sha, babu masu k'asa da haka.
Akwai arzik'i da yalwa, a yawanci gidajen wanda sai dai na wani yafi na wani, _wannan kuma falalar Allah ce da yake bawa wanda yaso._ Akwai tarbiyya ga yaran nasu, suna da ilimi na addini da na boko. Anyiwa familyn kyakykyawar sheda kuma an sansu sosai. wato _malam Na-Allah family._

*GIDANSU UKHASHA*
____________
Gida ne daya kunshi mata biyu, da yara goma sha d'aya. Hajiya Hafsah, wacce suke kira da _Haj._ Itace Babba, ta fito ne, daga tsatson sarauta, gaba da baya, kuma ita k'anwa ce ga sarki mai mulki a yanzu. Sannan tana aiki a wata makarantar 'yan mata a Matsayin _principal._ Amma baifi 'yan watanni sukayi saura tayi _retire_ ba.

Sai kuma Haj.Kubra suna kiranta da _Mama._ Itace ta biyu, tana aiki a wani asibiti a matsayin _Nurse_

A 'ya'yan Haj. Hafsah, Ukhasha shine na uku, Babbar 'ya a duka gidan mace ce, tana aiki da _Ministry of Women affairs, sunanta _Hajiya Na'ima_, a Abuja take da zama ita da yaranta da mijinta. Sai kuma _Dr. Sunusi_, Babban likita a asibitin Malam Aminu kano, yana da aure da yara uku, sai _Ukhashatu,_ kwararen engineer, wanda ya kware a harkar 'Civil engineering' Sai _Nura_ k'aninshi, shi kuma bangaren shari,a ya karanta, shine yayi aure, shekara d'aya data wuce, sai kuma _Fadwa,_ Itace autarsu, tana shekara ta uku a Jami,a.

D'akin mama kuma, _Nasir_ shine babba, wanda shine sa,an _Nura_, ( _wato sa,an mai bin ukhasha a d'akinsu_) sai _Maryam_, zata bawa Fadwa kusan shekara d'aya, sai _Zainab_, _Abdullahi,_ _Najeeb,_ sai autarsu ( _Mahseen_) Itace auta, duka gidan, shekarunta bazasu wuce goma sha biyu ba.

Idan har ba zaman gidan kayi na wani lokaci ba, ko kuma dama ka sansu, toh babu yadda za,ayi ka iya banbance 'yan wannan d'akin da 'yan wancan. Rayuwa ake ta had'in kai babu banbanci.

~_Connect with page 36_ (Inda ukhasha ya dawo gida daga party)~

*UKHASHA*
_____________
Yana ta son ya kauda tunanin ta, amma ya kasa, Yarinyar ta tsaya mishi arai, duk wani motsi nashi sai ya tuno ta. Matsalar d'aya ce, bai san a ina zai k'ara ganinta ba, bai san ita dawa suka zo bikin ba, bai san a wanne dangin take ba, na amarya ko na ango. _"Ya ilaahiy"_ Ya fad'a a hankali fargaba kawai yake, yana fatan kada Allah ya d'ora mishi son abinda bazai samu ba.

Wayarshi ke ta k'ara amma ko kalla baiyi ba, bare yayi tunanin d'agawa, don ya tabbatar idan ya d'aga komai zai iya faruwa, zai iya fada mata maganar da sai tayi da na sanin kiranshi.

K'arar shigowar text yaji, kamar zai share sai kuma yaga gwara ya duba.

_Allah ya huci zuciyarka, don Allah kayi hak'uri in sha Allah this wouldn't be happened again, na ajye wayar ne shine maman ta d'auka ta kiraka.. Plz am sorry, u know bazan iya jure abinda kake min ba plzx._

Ya sa, hak'oran sama ya cije leb'en shi na k'asa, daya tuno irin bak'ak'en zantukan daya sha a waya..

_"Mara mutunci,_
_mugu azzalumi wallahi ka sakar min kur,war 'ya in ba haka ba zaka ga abinda zai biyo baya.._ _Don tsabar mugunta ka asirce min yarinya!! Wa yasan abinda kake mata kana son ka lalata min yarinya!!_
~_To ba alk'ali ba koma waye mahaifin naka bazai hana nayi shari,a da ku ba.!!_~
Chapter 51 · 0% Book details