← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 88

Sashe 48

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ganin maman bata buk'atar b'acin lokaci yasa Hafsah daga kai a hankali, sai kuma ga hawaye na d`iga.
Mama ta tallafo ta da hannunta ta jigina ta da gefen k'afarta, "To menene na kuka kuma."?
Ba tambayar ki kawai nayi ba.?
Aka danyi shuru, kafin mama ta cigaba, "Idan nace ki daina kulashi zaki daina."?
Wannan tambayar daidai take da zubar garwashi a zuciyar Hafsah, don yanayin data shiga da jin maganar bazai misaltuwa ba, wannan karon kuka ta fara harda shashsheqa, _wanne irin zance ne wannan mara dad`in ji a kunnuwa."?_ Ita ta zauna ma ta kissima ('Imagine') rayuwar da babu Yusuf asara take gani saboda tasan, abu ne da bazai tab'a yuwuwa ba a wajenta.
Mama tasan za,ayi haka, don haka ba tare da nuna damuwa ba, akan Kukan da Hafsah keyi ta
cigaba da, zubo maganganunta, wad`anda baza,ace basa shiga kunnen Hafsah ba, tanajine, amma tunanin ta na wata duniyar.
_"Hafsah ita rayuwar nan da kika gani, in bakayi-bani guri ake, nasan bazakiyi mamaki ba naji komai dake tsakanin ku da yaron nan, amma tambayar da zanyi miki shine, ya sunan matsayinki a wajenshi.?_
(zuciyar Hafsah ta raya mata _"wadda zai aura mana"_)
Itama k'awar taki mene nata matsayin."? (gaban Hafsah ya fad`i, _wannan tambayar kam babu amsa, don daidai take da k'ure._ )
"Bazan zarge ki ba don ina miki kyakykyawan zato, amma tsakanin ki da Allah kin tab'a jin labarin soyayya irin taku."?
Shin kin tabajin anyi haka..?
_Bari na fada miki gaskiya, _Duk ranar da kika sake kuka cigaba da alak'a ke da shi, to ki tabbatar kema ranar kin shirya zama irin Basma ne, ko kuma kin zama irin ta.!"_
Hafsah tayi saurin d`ago kanta kamar wacce aka tsikara _ita kuma..??_ Mama ce take mata wannan magana, bata fatan ta zama irin Basma, azuciyar ta ma tana cewa _"Inaa.. sai dai idan ranar ba ni Hafsan bace._
"Hmm, a yanzu dole kiyi mamaki har ki kalleni, amma zan gaya miki wani abu, _Ba,a zama inuwa d'aya idan hali bai zo d'aya ba.!!_
_"Saboda haka, kodai ki rabu da shi, ko kuma ki zama irinshi."_
Kuma kada ki d'auka wak'ar da yake miki na zai aure ki gaske yake.. Duk k'arya ne!!.
"Ni Hafsah banda ma rufewar idanu, ki duba kiga tun sanda kika fara kulashi wacce riba kika ci a rayuwar ki, banda koma baya da kakai ta samu."?
Iyayenki na d'aukar ki mai hankali, amma yanzu kin nuna musu ba haka bane.. Da an sanki da tsoro, da sanin yakamata amma yanzu komai randomly kikeyi, kawai gaban kanki kike, har kina iya fita bada sanin kowa ba.!! Sannan kin san a baki abu ki b'oye k'iki nunawa, idan da gaske sonki yake babu abinda zai hana abbanki ya kirashi yazo, ke inya yi niyya ma, abbanki zai bawa abinda zai baki yace a baki.."
"Da yana son cigaba da kulaki ku cigaba da mu,amala ai zai nemeki duk inda kike.. Amma duk baiyi haka ba, sai ke kike
k'untatawa ziciyarki."?
_Ita dai Hafsah tayi shuru ma da Kukan tana sauraron gaskiyar dake yi mata d'aci, azuciyarta tana ta kokawar dole sai ta kare Yusuf daga abinda ake jingina masa."_
"Ke yanzu ba abin kunya bane, bayan sun kunyata ki agaban mutane an nuna baki da wani matsayi, sannan ki dawo kulashi."?
Wato kin nuna baki da class kenan, kuma babu wanda kike dashi sai shi koh."?
Abin da sukayi kin taba jin wani yaro mai tarbiyya yayi.."?
"Nidai bazan matsa miki ba, amma ina fad'a miki ki fitar da yaron nan daga zuciyar ki, ki d`auki kaddara, ayadda kika yi sati biyun nan ba tare daya nemeki ba, to ki saba a hakan ki cigaba da rayuwarki harki manta dashi. Zaki sami wanda ya fishi alkhairi in sha Allah."
Zuciyar Hafsah ta cika fal da kunci, so ya rufe mata ido, da da sa,arta take mata magana babu abinda zai hanata cewa, _"Ai Yusuf bani da wanda zaifi shi a wajena.!!_
Amma sai ta b'ige da cije leb'e kawai, mama fa tana fad'ar abinda bashi da ranar yuwuwa ne.
Ita ko Yusuf ya nemeta ko kada ya nemeta, ita zata nemoshi kuma tana da yak'inin bazai taba juya mata baya ba.!
Kamar mama ta karanta abinda ke cikin zuciyar Hafsah tace, "Nid'ai ina fad`a miki ne, duk da nasan maganata ba zata taba shiga kunnenki yanzun nan ba, amma kiyi tunani, sannan kuma daga nan zuwa duk ranar da kika sa aranki zaki rabu dashi, to kizo ni kuma zan fad`a miki hanyoyi da matakan da zaki bi in sha Allah, ko wanne irin so kike masa sai kin manta dashi."
Da a halin farin ciki, Hafsah take to da babu abinda zai hanata yin dariya, ji wasu kalmamomi wai _"wai na manta da Yusuf.!!_
Ashe kuwa ranar, zuciyata bata jiki nah.!! Abinda Hafsah ta sawa ranta kenan..
"Zaki iya tafiya, kuma daga yau zaki iya komawa dakin fateema da kwana har zuwa sanda kika ga ya dace ki tuntubeni idan zancen da na fad'a miki ya samu karb'uwa.
Da Wannan mama ta katse mata tunanin ta, wanda akwai hikima a cewar mama, _"Hafsah ta koma dakin fateema da kwana."_

Hikimar kuwa Itace, Hafsah da Fateema shekarunsu kusan d'aya ba kamar ita maman ba, sau dayawa yara sunfi yarda da shawarar sa,anninsu fiye da ta iyayensu ko kuma wanda ya girme su. Tasan Hafsah zata iya nemar shawarar Fateema akan zancenta.
"Nagode.!!
Haka Hafsah ta iya cewa kawai, shima don gudun kada aga rashin kunyarta ne, mama ta d'auka cewa zancenta bai sami shigaba."
Ki dinga addu,a, dai ki nemi zab'in Allah, shine kawai.

Sai yanzu taji sanyi, kuma taji mama ta fad'i maganar da inda addua ce zata iya cewa "amiin."
"Ki turo min fateema.!!
Mama ta rufe da wannan kalmar.
Ita dai Hafsah gaba tayi kawai, don bakinta yayi mata nauyi, mamaki ma take mama da girmanta amma take son sanya kanta cikin al,amran soyayyar yanzu, Hafsah gani take ma anya mama tasan so kuwa da take ambata mata kalmar _rabuwa,_ _rabuwa._!!?
😅
Fateema na zuwa mama ta fara fad'ar sakonta babu b'ata lokaci, "Idan yarinya can ta nemi ki ara mata waya, ki bata, matuk'ar kin tabbatar yaron nan zata kira."
Fateema ta waro idanuwa da mamaki, ya mama da ake zaton zata gyara, kuma da b'atawa."?
"Eh..!! 'Inji mama ganin kallon da fateema ke zubo mata.
_"Ai ko ni bazan goyi bayan Hafsah ta cigaba da mu,amala da wannan mutumin ba.!!_
Fateema ta fada a zuciyarta.
Mama ta katse tunaninta.
"Tashi kije idan hakan ta faru, sai ki zo ki labarta min, dalili ne ma zaisa na hanata wayarta, da tatan zan bata."
Babu fuskar yin tambaya ko nuna rashin gamsuwa, don haka fateema tayi azamar mik'ewa tana fad`in, "To mama Shikenan.!!
Mama ta bi bayanta da kallo, hikimar ta shine "Don Hafsah ta sami damar yin shawara da Fateema, tunda Itace sa,arta zatafi yadda da zancenta fiye dana maman.
Gefe kuma, tana tunanin idan suka jone da yaron, menene mataki na
gaba kuma..."?

Tabbas yarinyar na buk'atar addu,a, tuna cewa babu addu,ar da tafi ta uwa amsuwa yasa, taja waya don kiran Amina, cikin nutsuwa take kwantar mata da hankali, tana nuna mata komai ya kusa zuwa k'arshen addu,ar ta kawai ake da buk'ata."
_"Ki riqa yin addu,a nan da nan zaki ga komai yazo da sauk'i wannan ba wani babban abu bane can.._
Hakan maman ta fad'a mata...

📝
*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔

*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄 *44*
Chapter 48 · 0% Book details