← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 88

Sashe 84

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bacci mai cike da farinciki Hafsah tayi bayan ta koma cikin gida sun baje ice-cream d'in sannan ta mik'a wa mama katinan.. Amira ce tace "amma dai yaya ba zaki je ba koh"?
Bata ce komai ba saboda mama dake wajen..
___________________________

Yusuf ya koma gida jiki a sanyaye ya rasa me yake mishi dad'i yanxu shikenan ya rasa Hafsah."?

In ko hakane zai jinginar da zancen aure duk da yana buk'atar auren a yanzu.
Wato abinda ya nutsar dashi kan batun aure shine:
Tun lokacin da mahaifinshi ya rasu wata daya baya sanda aka k'are zaman makoki wasu daga cikin dangi suka hadu suke ta mishi nasiha da misalai iri.
Sun nuna mishi yadda mahaifinshi ya rasu ba tare da yaga jikanshi ba. Sun nuna mishi yadda rasuwar taxo bag-tatan wanda shima Yusuf ba karamin kaduwa yayi da batun rasuwar ba gani yake kamar a mafarki.. wai daddyn shi ya rasu.
Sun mishi misali da shi kadai ne wajen iyayenshi haka babanshi shi kadai kakarshi ta haifa."?
Duk da ada hakan baya damunshi amma yanzu ya damun ko dan mahaifiyar shi zata so taga ya'yanshi ita.

Sannan sun nuna mishi girma ya fara kamashi don akallah zaiyi shekaru talatin da abubuwa.

Tunda akayi rasuwar ya rage hulda da yan matan shi kuma indai ba gaisuwa zaki mishi a waya ba baya bari kuyi hira.
A lokacin rasuwar mahaifiyar shi taga tarin yan mata kala-kala wanda ta rasa daga ina suke.
Wai don ma kadan daga ciki kenan masu raguwar tarbiyya da tausayawa da suka zo mishi gaisuwar.
Sai lokacin kuma hankalin ta ya tashi tasan d'anta ya wuce tunaninta a kallah kullum ta kanga bak'in yan mata biyu zuwa uku har akayi bakwai kuma suna zuwa cewa suke "ina Yusuf."?

Yusuf bai k'ara saduda ba sai da yaga sun dawo kwana shida mum d'inshi kadai a gidan sai yan aiki gashi mum din kullum cikin kuka yake.

Babu wacce ke yawo a kwanyar shi kullum kamar Hafsah.. amma yana tsoron tunkarar ta. Ita kadaice yaji zai iya aura ba tare daya sa shakku akanta ba a ranshi.

To yau ga abinda ya tarar. Duk da bai sa ran zai ganta ba amma ganin nata ya haifar mishi da damuwa mara misaltuwa.

Ya raba dare babu bacci yana saka yadda zaiyi ya samu Hafsah amma ya rasa mafita. Gashi zuciyar shi ta kasa hak'ura. Ya zauna sosai ya dinga tariyo rayuwar da sukayi a baya cike da shauk'i da yanda komai ya dinga faruwa kamar Film, zuciyar shi na kara ingiza shi.. _shiya san yarintar ta don haka shiya dace ya aure ta!!_

Da kyar ya rik'i wani abu da yake tunanin shine mafita.

________________________
Yau tunda Hafsah ta tashi take jinta cike da nishadi ji take babu sauran damuwa.

Yau abin mamaki sai taga abban ta har dakin ta bayan ya mata knocking tana jinshine taji wata fargaba lafiya Abba har d'akinta yau.
Shiko cewa yake Yaya bude kinji muyi wata Shawara."

Ak'asa ta zauna ta dukar da kai da fargabar wane muhimmin abu ne yasa abban takowa da kafarsa."?

Abban ya zauna gefen gado.. ya fara da nasiha da rarrashi kafin ya fada wa Hafsah abinda ta k'agu taji.

Aure ba abin wasa bane Hafsah babu lallai mijinki ya yarda ki cigaba da aikin gidan TV saboda haka kiyi hakuri ki ajye in sha Allah Allah zai baki wani.. nima bana goyon bayan ki zauna babu wata sana'a ko wani aiki."
Ta dago a hankali ta kalleshi wato zancen Ukhashatu dai..badon tayi imani bazai iya yiwa Abba wannan zancen ba da sai tace shine ya roki Abba, amma tasan basu hadu ba kuma bazai wa Abba zance a waya ba.

In sha Allah Abba zan ajiye zan rubuta resigning zuwa qarshen satin nan.
Ya fad'ad'a murmurshi Allah yai miki albarka in sha Allah da kaina zan sama miki wani.
Tayi murmurshi nagode Abba. Duk da gefe tanajin babu dad'i saboda sabo da mutane..

Bayan fitowar Abba daga dakin nata cikin mamaki yaji labarin wai yayi bako a waje.

Da fitar Abba yayi mamakin ganin saurayi Abba ya mik'a mishi hannu suka gaisa.
Babu jira Yusuf ya fara bayani.

Abban nazo wajen Hafsah ne shine take cemin wai anyi mata engaged kuma wallahi yanzu da gaske nake aurenta zanyi ina sonta Abba."

Abba ya tsaya sororo yana kallonshi wane irin yaro ne wannan magana babu ladabi babu iyawa haka ake neman auren."? Shida yasan Hafsah bata kula kowa to shi daga ina yake kenan."?

Waye kai."?
Abban ya tambaya.
Nine Yusuf Abbah, I dated Hafsah years back har kace na turo..lokacin ban shirya bane..
Abba ya gane shi wato yaron daya hargitsa masa rayuwar gidanshi ne yaso ya hure wa yarshi kunne. Abin ya bawa Abban dariya har sai da ya dara sosai lallai yaron bashi da ta-ido wato har jawabi yake. Gefe guda kuma Abba ya gode wa Allah daya ga wannan yaro ido da ido.
Take ya tuno komai da sanda yasha gwagwarmaya da Hafsah.
Abba ya dan hade rai saboda ya takaita koma meye yace..
Wato sai yanzu ka shirya koh."? To anyi mata miji kaji.. kuma ka dakata da zuwa wajen ta."
Nan Yusuf ya Shiga magiya Abba ya daga mishi hannu kaje gida Allah ya baka wata kaima. Daga nan Abba ya juya ciki.
Aka bar Yusuf kamar ya fasa ihu.

Abba ya shiga gidan yana dariya, yasa a ranshi ba ma zai fadawa Hafsah ba sai dai kuma zai bawa Amina labari.

Sun kuwa sha dariya sosai shida ita.
_Kinga abu kamar mafarki ko amina."?_
Ta gyada kai.
Yace alhakin kine dana yarki ke ya dinga sawa shakku da kokarin sa miki hawan jini ita kuma tana matuk'ar sanshi shiko yana k'okarin bata ta.
Mama ta d'ora "sannan ya yaudare ta ba ai dama na roki Allah sakayya."!!
Ya kalleta suka sa dariya.

Ukhasha yazo kamar yadda yayi alqawari sun sha soyayyar mu shida Hafsan shi a hankali cikin hikima da wayo yadda bazai zargi wani abu a ranshi ba ta bashi labarin rayuwarta ta baya wacce ta kunshi Yusuf da Basma da Jamila. Daga karshe ta nuna masa yadda Basma tayi mata snatching.
"Kaga ina na d'auke ta aminiya ashe saurayina take so."
Hafsah ta fada mishi hakane don bazata iya fad'a mishi zahirin abinda ya faru ba da yadda Yusuf yake ko don gudun zargi..

To ya akayi kika gane ta kwace miki shi."?
Tayi wani murmurshi kafin tace naje gidansu ne naga yazo zance wajenta."
"Hmm..yace..
Ku fa mata haka kuke waya ce miki zance yaje."?
Ta kalleshi kallo mai kama da harara.
Yayi murmurshi "To ai gashi Allah ya baki ni koh."?
Tayi murmurshi.
Hakane."?
Ta gyada kai.
Ukhashatu yayi k'okari ya nusar da ita yadda rayuwa take. Sannan ya nuna mata ta dauki komai yadda yaxo kada tunanin baya yasa tace zata kusanta kanta da Jamila domin yanzu ba da bace.. _"wasu mutanen zama dazu sai shafa maka bak'in fenti ne kawai.."_
Idan tazo wajenki kada kiki saurarar ta amma kisan irin mu'amalar da xakuyi. Dama irin haka a rayuwa dole a dinga samun shi. Muma suna nan wadanda munyi yarinta tare dasu amma yanzu mu da su sai dai Hi hi tunda kowa akwai layin daya dauka. Kuma kowa da yadda Allah ya tsara mishi rayuwa..

Hafsah ta yarda da duk zantukan shi 100% kuma ta kuma tabbatarwa da kanta lallai Ukhashatu shine ya dace da ita kuma shi _Masoyin k'warai_ ne.

Daga nan suka shiga wata hirar yana tambayarta.. me zamu tsara ne na bikin mu uhum amarya.?
Cike da kunya ta kawar da zancen da cewa.
"Resigning.!!
Ya kalleta yana dariya.
"Ai mun gama maganar ranki ya dade."
Wannan umarnin Abba ne."
Ta fada."?
Cike da zumudi yace Allah."?
Ta jinjina kai.
Kaii Allah ya k'ara nisan kwana gaskiya na gode zanyi wa Abba godiya.
Anjima ma za'a turo kanina ya kawo mishi Invitation Abba yace bazai bani ba wai gwara ya aiko takanas tunda ni na zama dan gida."?
Hafsah ta kalleshi "ka fiya zolaya Allah."
To ba haka bane."?
Hakane.
Tace mishi.
______________________

Yau Hafsah ta k'ara karbar ba k'uncin jamila sai dai cikin wani yanayi na daban wanda Jamila tazo dashi abin tausayi domin da kuka ma ta shigo.

Sai da Hafsah tayi da gaske sannan Jamila tayi shuru ta fara sanar da ita abinda ke faruwa.

"Hafsah na dawo gida yau..Uwar dakina ta rasu yan uwanta sun kwashe komai nata gidan da muke ciki ma sun koro ni dole na dawo gida."
Hafsah ta zaro ido da mamaki "Innalillahi tun yaushe ba kince tafiya xakuyi ba."?
Da ita ne dama kuma ba muyi tafiyar ba ma ta rasu.
Tausayi ya mamaye Hafsah ganin yadda Jamila ke kuka.

D'akin yayi shuru sai da Jamila ta sha kukanta sannan ta bude baki tace fara bawa Hafsah labarin yadda rayuwarta takasance bayan barinta gida.

Hafsah ta bata dukkan hankalinta Jamila kuma ta bude baki ta fara.

"Hafsah nasan kema kina min kallon wacce take zaman kanta koh."?
Duk da hakan ne bani da maraba tunda ba gaban iyaye na nake ba... labarin nada tsaho amma tunda ya riga ya wuce babu amfanin tunawa sai dai zan fada miki wasu abubuwan a takaice ne..

_Bayan barina gida. Nasha gwagwarmaya ta rayuwa ga ciki ajiki na (don nasan kinji labarin komai.)_
Nayi rashin mahalli da tudun dafawa har takai ina na rasa inda zan nufa.

_Tunani na ya gushe na manta da k'awa ta ta makaranta._

_Da kyar na samu abinci a yammacin a wani wajen cin abinci. Wanda na zama tamkar mabaraciya a wajen._

Sai da na ci abinci sannan tunani na ya dawo. A lokacin na tuno da k'awar tawa "Samha"

_Da kyar na ari waya na kirata a rikice. Tayi min kwatancen gidansu. Bani da kudin mota haka na fara takawa a k'afa. Wanda daga karshe dai da kyar na hau abin hawa wanda sai bayan dana sauka ne nake ce mishi ya min taimako bani da ko sisi. Don ba'a barni na fito da ko biyar ba daga gida. Mutumin nan har Allah ya isa yayi min don yace kamata babu yadda zaayi akalleni ace bani da kudi. (Sanda na sami dama na mishi sadakar kudin shi.)_
Chapter 84 · 0% Book details