← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 130

Sashe 93

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace "I promise you zan dawo gareka karage punishing kanka for me please"

ya lumshe ido yace "I will try "se sannan yatsaya karemata kallo tana sanye da white shirt transparent ta matukar yi mata kyau yanajin kamar yakai hannu ya taba yace "I will go home kiboye wayar nan sena kiraki da anjima before nan kimin good bye kisss "

Faseelat tai murmushi tana jefa mai wani kallo taiwa hannunta kiss ta jefa mai, yayi dariya yace "thanks se nakira" yakashe wayar faseelat tai murmushi ta bi list na music ta kunno wakar tana saurare hardasu hawaye setaji kamar itada fahad ne,

Sunata wayarsu bawanda yasani for 2days wadda bata ragemusu kewa ba sekarawa don duk ji sukeyi kamar suyi kurciya su samu juna,

baba babba karfe hudu yashigo katsina direct gidansu faseelat yawuce, yana zuwa yashiga da sallama, ummi ta amsa tana mai sannu dazuwa ya amsa yace "ina diyata ya jikinta? "

ummi tace "tawarware ai"ta kwalawa faseelat kira,

faseelat tafito dasauri tana ganin baba babba ta duka kasa tana gaidashi ,

Baba babba ya amsa ya mata ya jiki tatashi takoma daki,

Baba babba yace "munyi magana da alhaji yace har yanzu be bata takardarta ba wai sunata rokon alfarma "

Ummi tace "aikuwa "

baba babba yace "seya saketa tunda beda mutunci, bawani hakuri da zebada miji meduka aiba miji bane faseelat batai saar miji ba gaskiya"

ummi tai shiru ,kamin ta rufe ido tabude sede taga faseelat tsugunne gaban baba babba tana hawaye tace "baba Dan Allah kuyi hakuri wlh kuskurene ba acikin hayyacin shi yayi ba dan Allah kumishi hakuri tunda yagane laifinsa"

ummi tanata fidda ido dan faseelat tai shiru amma ita batasan ma tanayi ba seda takai aya,

baba babba yasha mamaki ranshi ya baci sosai yace "ko kinki ko kinso se yabada takardarki marar kunya fitsararra,tashi kiban wuri kona mangareki wurinnan"

Faseelat tatashi tashiga daki tana kuka ummi tai shiru tanajin kunya, baba babba yace "ai gwara ya saketan wannan Allah kadai yasan azabar data kesha wurinshi tai shiru bari naje nasamu alhajin shigowata kenan nashigo ganinta "

ummi tace "Tom angode kwarai "yafita

ummi bata shiga dakin faseelat ba tawuce dakinta, ranta ya baci takuma kara jinjina rashin kunyar faseelat,

Baba babba shagon abba yawuce suka kara tattaunawa akan maganar dawasu abunda ya shafesu sannan ya tafi gida,

Faseelat na kuka takira fahad yana dauka tace "hero baba babba yadawo, yace dole seka sakeni Dan Allah komai zasuyi karka sakeni wlh inasonka inasonka sosai"

fahad dake kwance muryarshi very low yace "kiyi hakuri kinji yanzu zanje nasamu daddy zezo yasameshi ki kwantar da hankalinki bazan iya musu abinda suke so ba"

Yadan rarrasheta yakashe wayar, yatashi ya nufi gidan umma yasamu daddy da maganar daddy ya amshi address na gidan fahad bebar gidanba seda yaga baba babba yatafi can, sannan ya koma gida,

koda daddy yaje baba babba yana cin abinci seda akadau lokaci yana jira sannan baba babba yafito ya kalleshi don betaba ganinshi ba yabashi hannu suka gaisa,

daddy yakara gyara tsayuwa yace "nasan baka gane niba, ni kamar ubane awurin fahad don nike auren mamanshi,"

baba babba yayi shiru yana saurarenshi yanajiran yakai aya,

daddy yace "nazo bada hakuri ne akan laifin da fahad yayi da kuma rokon alfarmarku da kuyi hakuri kubari takoma dakinta a janye maganar sakinnan tunda yayi nadama kuma suna matukar son junansu"

baba babba yace "alhaji nasan de bazaka iya aurawa yarka mebugun mata ba, to nima hakane aguna bamusan halinshi ba mukabashi ita yanzu kuma da mukasan halinshi rabasu shine dede don watarana in abun yazo da karshen kwana seya kasheta, Dan Allah kayi hakuri kabar maganar komawarta wurinshi Allah yahada kowa da rabonshi"

daddy yace "ayi hakuri alhaji atemaka wlh yaron rayuwarshi ta tsaya cakkk yana bukatar temako aduba "

baba babba yace "da akwai yiwuwar yin hakurin da anyi since to bacin maganar duka ma yanada wasu problem din don bayason zumunci, yahana yanuwanta zuwa wurinta"

daddy ya fiddo ido jin wata sabuwa yace
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

7⃣7⃣

*page dinnakine soupnass ke kadai wlh don jindadinki nayi shi, nagode da kaunar da kikewa buk dina da dogon sharhi da kike me zafi nagode kwarai inayinki to the core*🥰

*Manzon Allah(SAW)yacewa sahabbai shin bana baku labarin abunda yafi salla da azumi da sadaka lada ba,se sahabbai sukace wane abune wannan ya maaikin Allah seyace sulhunta tsakanin mutane yafi salla da azumi da sadaka lada*

Sulhunta tsakanin friends, couple,yanuwa and others

*MANZON TSIRA (S. A. W) ME GASKIYA ABUN GASKATAWA yace zumunci yana sargafe ne asaman Al'arshi yana cewa ya Allah duk wanda ya sadani kasadashi duk wanda ya yanke ni ka yanke mishi* Imam bukhari

Yace "gaskiya be kyauta ba kuma mu bamusan haka na faruwa ba amma zai gyara da yardar Allah adeyi hakuri"

Baba babba yace"ina kara baka hakuri don gaskiya bazata koma ba duk namijin da beson zumunci ai ba miji bane"

Ba yadda daddy beba amma baba babba be hakura ba hakanan yajuya yatafi, fahad yakoma jin good news daddy ya rufeshi da fada,

Fahad yayi shiru har daddy yagama sannan ya tashi yafita yana shiga mota ya dukar da kai jikin sitiyarin motar yafasa kuka,

Umma de tagaji da ganinshi cikin hali ganin yadda yafita ta biyoshi waje tasamu yanata kuka, ta bude motar tashiga,

Fahad yanata kuka tace "kayi shiru son, nagaji daga ninka cikin kunci ka kwantar da hankalinka namaka alkawari kwanan nan faseelat zata dawo gidanka"

Ya dago fuska face face da hawaye yace "when and how? Kinaji fa abunda daddy yafada wlh umma sora kiris na mutu "

Umma tace "kabar cewa hakanan ni namaka alkawari zata dawo very soon ka dena kuka"

Yadan rage kukan yace "kin cefa alkawari? "

Tace "eh alkawari ne kuma soon zata dawo kaide kayi hakuri kadena damuwa kuma sabeer yace baka Aiki kuma baka zuwa ,yau dinnan kakoma aikinka inhar kanason nacika ma alkawarin ka "

Fahad ya daga kai yanajin dan sauki kadan,

Tace "gobe naga canji in kuma haka kakeso heart beat din taka tazo ta sameka a kanjame to,duk kabi kasusuce kai son anya ko mutuwa nai zaka shiga irin wannan damuwar? "

Fahad yayi murmushi ya duke, tace "ko kaifa kayi hakuri nadan lokaci kawai "

Ya jinjina kai sannan tafita, ya koma gida yabude system dinshi yadanfara aiki sama sama,

Da daddare daddy yakai umma gidansu faseelat bayan gaisuwa umma tace "nazone akan maganar fahad Dan Allah kuyi hakuri dan daddinshi yace yasamu alhajin kuma basu dedeta ba"

Ummi tace "zaya hakura kude cigaba da zuwa gunshin "

Umma tace "to nagode kwarai ina faseelat? "

ummi tace "tana cikin dakinta"

umma tace "bari naje naganta se nawuce"tafita ta shiga dakin faseelat ,

Faseelat na kwance tunda sukagama waya da fahad take kwance, umma tai sallama faseelat ta tashi zaune ta amsa,

umma taje ta zauna kan gadonta ta dafata tace "daughter kikara hakuri kinji very soon zaki koma dakinki "

faseelat tadaga mata kai tayi shiru,

umma taimata bankwana tafita,

awaje daddy Sun tattauna da abba shima de cemishi yayi suyita zuwa suna bashi hakuri,

Dasafe fahad yafita office, yana zuwa ko zaunawa beyi ba manager yakirashi ya fita yaje office dinsa ya zauna,

Manager yakureshi da ido sannan yace "meye dalilinka nakin yiwa company aiki munyi loosing contract da dama kasan konawa kasa company yayi asara? "

Fahad da yake har yanzu sama sama yace "I don't know, and don't care I will repay nasan da rules na company "

manager yace "u r not serious nawa gareka da kake ganin biyan kudin is not a problem, kudin sunkai 50 millions dollars "

fahad surutun manager yafara isarshi yace "I will repay all ur money back"

ya tashi yafita, manager yabi kofar da kallo yana jin matsanancin bacin rai,

fahad ya rubuta musu check ya basu yafita abinshi, bawai kudin is not much ba, sunada yawa to bayadda yaiya dole yabiya ,

tunda dugu dugu daddy yakoma gidan baba babba, yakara bashi hakuri amma bejiba sema rokonshi da yayi karya sake dawowa,

da marece alhaji rabiu yaje wurin baba babba shima yarokeshi baba babba yabashi hakuri ya tafi,

dukda alhaji yaroki daddy amma wanshekare seda yakoma, baba babba seyaji nauyinshi tunda zuwanshi na ukku kenan,

baba babba ya kalli daddy yace "ko a lahira wani nacin darajar wani, domin Allah yakan kankare zunuban bawa in yaranshi namashi addua yakara masa matsayi a aljanna, ana sanya iyaye wadanda suka haifi mahaddatan alkurani a inuwa albarkacin yaransu, wasu daga cikin yara kananu zasu ceci iyayensu a ranar kiyama,fahad yaci albarkacinku na hakura zata koma amma da sharadi se yazonan tareda waliyanshi da suka nema mishi aure agabansu yayi alkawarin baze kara dukanta ba kuma baze hanata zumunci ba in kuma yayi daya dagaciki to zamu kaishi kotu yabata sakinta "

daddy yace "insha Allah ze kiyaye kuma zamuzo din nagode da kamin alfarma "

baba babba yace "sekunzo "yajuya yashiga gida, tun kan hanya ya kira fahad yace yasameshi gida, ba bata lokaci yatafi acan daddy yasameshi,

daddy yafadawa fahad yadda sukayi, zufa taita karyomishi don besan komi zefaru nan gaba ba yanata de rokon Allah yarage mishi kishin amma dasaura,

Ba yadda yaiya yace "ya amince da hakan "

daddy yace "to inma kakara de ni baruwana ciki katashi katafi se zuwa gobe dasafe se kasame mu acan da karfe 9am"
Fahad yayi godiya yatashi yafita,

wanshekare da daddy da alhaji rabiu da kaninshi da fahad a sitting room na baba babba, sukadanyi gaishe gaishe da jajen abinda yafaru sannan baba babba yafadawa fahad sharadinsu, fahad yace ya amince agaban su,

baba babba yace "ga waliyanka nan duk sunji yadda mukayi idan har hakan tafaru karkai tunanin zata dawo gareka, yanzu zanyi magana da alhaji sekaje kadauki matarka ku koma gida "

fahad yace "nagode zan kiyaye"

suka rufe taro da addua suka tashi,
Chapter 93 · 0% Book details