← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 130

Sashe 79

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
*
We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
*Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

6⃣8⃣

*bestowed this page to anty hauwa lawal me sunan baba thanks for the love and alheri inata godiya Allah yabar soyayya*

Sedata dau lokaci zaune tanata sake sake zuciyar ta na zafi batasan lokacin da hawaye suka silalo akan kumcinta ba tasa habar zanenta ta share tana ayyana abubuwa da dama aranta ta tashi ta kimtsa ta kwanta sede bacci kasa ko sama ba bushi har kagara tayi gari ya waye,

Titin fessss yake se mashina daidaiku dake kaikai kawo amma ba wata alamar jamila, da high speed ya isa gida beko shigar da mashin dinshi ba ya shiga gidan, tun azaure yaji kuka da ihun jamila, yaja tsoki dan haka yakoma ya shigo da mashin dinshi ciki, ya samu jamila tsakar gida a rashe tana ta kuka,

Ya daka mata tsawa "keeee !!!! Kukan ubanmi kike? "

Jamila taci gaba da kukanta ta tashi ta shige daki, ya bita dasauri ya sameta kwance akan bed tana ta kuka sekace wadda aka daka,

Yayi tsaye kanta ranshi bace yace "Ashe baki da hankali kuma bakida tunani ko kadan dan kinada brain din kaji sekije kisamu hjya kimata hauka? Saboda hauka da rashin tarbiyya irinnaki agabanta zakije kina fadamata magana "

Tana kuka tace "nagaji nagaji don me zanyi shiru a rika shiga hakkina kullum, tsofai tsofai daita ta rika kishi dani yarinyar cikinta, wlh ko gobe ka kara kaiwa dare sena je namata warning kafin infara shuka rashin mutunci "

Idanunshi jawur yake kallonta da mamaki da tarin haushi da takaici cikin fada yace "hjya zakiwa rashin mutunci saboda kina mahaukaciya duk wani rashin mutuncinki hjy ta fiki iyawa dan wlh tsabbbb zata nakada maki duka tasa ni dole na sake ki ki koma can kauyanku jaka kawai , ko yanzu ki fara rokon Allah ta hakura ta barki ahaka sakarai marar hankali inba ma da kina mahaukaciya ba mahaifiyata zaki kalla ki ciwa mutunci agabana dan iskanci"

Jamila tace "yo haka surukkan kwarai suke ai ita yakamata ta rika baka shawara ka kula dani amma itace kesaka kana tauyemin hakkina wlh har fin haka zanyi mata"

Yaja dogon tsoki da ace yana iya bugun mace da tuni yaci ubanta, yasa hannu ya ciro waya yace "bari na kira mama da baba nafadamasu abinda kikayi kafinma hjy ta dauki mataki, tunda har nima zakirika medawa magana "

Ya latso suna ya kara akunne ,jamila ta sa kuka "Dan Allah karka fadamasu kayi hakuri zanje nabawa hjyar hakuri kuma bazan sake ba in sukaji wlh har bugu na baba zeyi"

Khalil ya cire wayar daga aljihu yana mata kallon mahaukaciya yace "saboda hauka sekije bata hakuri mtswww mental tokice mata me? "

"Nide zanje nabata hakuri wlh in su mama sukaji fushi zasuyi dani "

Yakara jan tsoki "wai saboda hauka jamila kije wurin hjya ido da ido kifada mata magana, hmmmm yanzu nariga na mata karya nace iskokai ne dake in ta hakura shikenan inbata hakura ba kau akwai matsala, kuma kisani hjy ita ta haifeni tai duk wata dawainiya ta itace duniya ta itace lahira ta tafi duk matan duniya awurina ita nafi so fiye da komi idan har kinason zama dani dole kiyi hakuri da yadda take in bazaki iyaba sena sawwake miki, kamar yadda kike tsoron fushin iyayenki haka nake tsoron fushinta fin tunaninki ma kuma duk abinda zesa ta farinciki zanyi kokarin yi mata shi,kuma dole kirika girmamata inkinason zaman lpy dani useless girl kawai "

jamila ta cigaba da kuka, ya fita yabar mata dakin ya koma dayan dakin ya kwanta, shima yakasa bacci , rabin son da yakewa jamila duk ya tafi se tunanin faseelat da yadawo mashi sabo yadda take kula da mahaifiyarshi kafin taso rabuwa dashi, ya gyara kwanciya ya rungume pillows yana tuna yadda takeyin kasa da fuska saboda kunya da murmushinta idan sukaje gun hjya,sonta se yadawo mashi sabo ya rumtse ido zuciyar shi na zafi

yace "hjya duk ke kikajawo hakan ko alhakin faseelat baze barki ba nasan kema dole zakiyi kewarta, I love her so much babu wacce zanso kamarta tana da duk qualities na mace tagari amma saboda son zuciyarki hjya kikai abinda dole ta sauya hali kinja na rabu daita gashi har yau nakasa cire tunanin ta araina nikan tuno duk wani abu me kyau nata cute face, cute body, cute skin,white lulu eyes good structure ,long hair obedient tasty food and drinks shyness more over light heart and her beautiful smiling "

Ya kara matse pillow ya rumtse ido yana tuno yadda yakejin natsuwa idan ya rungumeta hawaye masu zafi suka zubo mishi ya bude ido yace "I love her I will surely die with her love, ko tana ina yanzu? "(niko nace mishi ai tayi aure 🤣)

"inafatan ki kara zama Matata akaro na biyu saboda inasonki nine nafi kowa sonki"

Jamila tagaji tai shiru cikinta se juyi yakeyi setaji kuma tana regretting abinda tayi, she love khalil so much bazata iya rabuwa dashi ba, tasan ta bata mishi rai sosai tunda har yayi mata hijira agado ta sauko daga kan bed din tabude fridge tasha ruwa kamar barauniya tana sanda ta nufi dakinshi,

Yana ta kallon silin ta turo dakin ta shigo ta durkusa kasan kujerar da yake kwance tace"dan Allah yaya kayi hakuri wlh duk sharrin shedanne da na zuciya I promise you bazan sake ba kayafemin "

Beko kalleta ba yakira sunanta "Jamila! "

Ta kura mishi ido yace "kin matukar batamin rai da kika nuna mahaifiya ta bakomi take agunki ba nayi zaton zaki bata girma fiyeda nikaina amma bahaka ba, wlh rabin son da nike miki duk ya tafi tunda har kika iya wulakanta min uwata kitashi ki tafiyar ki dakinki tunda kin fadi ta cikinki aise kije ki bacci "

Jamila ta riko hannunshi dasauri hankali tashe tana zubda hawaye tace "Dan Allah kayi hakuri karka dena sona wlh nafison ka fiyeda komi ka dawo da duk sonda kakemin zan gyara kuskurena"

Yaja tsoki a zuci yace madness its true fa jamila kanta da motsin dukda yarinta da kuma hauka,

Tace "plssss wlh zan gyara namaka alkawari zanso ta kuma zan bata girma bazan kara yin korafi akanta ba "

Yayi shiru taita risgar kuka yagaji yace "Dan Allah karkisa dodon kunnena yayi ciwo naji inasonki na kuma hakura shikenan? "

Tace"se kuma kadawo da son nawa da kace ya tafi "

Abun de na yarinta yace "to ya dawo shikenan kije ki kwanta "

Ta share hawaye da bayan hannu tace nima anan zan kwana tare da kai "

Ya dafe goshi yace "OK tashi mukoma dakinki kar jikinki yayi ciwo anan "

Ta kamo hannushi ta tashi suka tafi dakinta suka kwanta

ta matsa ta rungumeshi sosai tana kara bashi hakuri shiko tunaninshi ya tafi akan gobe yadda zasuyi da hjya,

yayi shiru yanaso tasamu bacci ne kawai saboda cikin ta,

wansafe fuska ba yabo ba fallasa yake shirin fita,

jamila tagama breakfast ta shigo ta sameshi tai zaune tana ta kallonshi so take takara bashi hakuri kuma tana tsoron ya dawo yi mata fada,

Jiki amace tace "ga breakfast dinka "

yana saka hula yace "banci ki dauke abinki"

tafara hawaye tace "kacemin ka hakura ni kawai kabarni har ita inje nabata hakuri "

yace "karki kuskura ki kara taka kafa waje bada izinina ba kinga jiya na shareki amma next time wlh sena gwadamiki nawa kalar haukan, ki kwashe kayan abincinki wurin hjya zanje nayi breakfast dina "

Ta dora hannu akai "nide nashiga ukku ni jamila "

Yace "bakwai kika shiga ba ukku ba, mental "

yazo ze fita wufff ta kamo gefen rigarshi tarike tana magiya" dan Allah yaya khalil kayi hakuri na yarda banda hankali, wlh nayi nadama bansan meyahau kaina ba "

ya kalli rigarshi ya kalleta yace "cikani "

Taki Saki ya bige mata hannu ya nufi kofa,

beko samu cikinta ba ta dafe ciki ta duke tafara ihu "wayyo Allah cikina wayyo ya khalil"

da gudu ya dawo wurinta ya duka yana fadin "lpy meyasameki ko mutafi asibity ?"

ta rika yarfa hannu" yaya cikina zaya balle marata "

hankalinshi ya matukar tashi tuni tausayinta ya mantar dashi lefin yace "sannu yi hakuri bari na samo mota mutafi asibity sannu "

ya juya yafita dasauri, ta cigaba da kuka tana kuka tace "inba haka naiba bawai hakurin zeba "

bayan 10mnt ya shigo tai shiru kanta Duke akushin ya wuce ya dauko abaya yazo ya rikota zesa mata sutafi hospital tai fuskar yaushi tace "yadena ciwon ai base munje asibitin ba "

Ya kalleta yace "a, a mutafi likita ya dubaki"

ta girgiza kai tace "kabarshi na warke"

yayi shiru yana kallonta na seconds ya tashi ya fita ya sallami me motor da ya taro,

Yadawo wurinta still tana nan daga tsaye yace mata "lpy lau de ko don fita zanyi "

ta dagamai kai tace "amma kayi hakuri bazan iya cin abinci ba in baka yafemin ba "

Ya yamutsa fuska yace "to naji na hakura ai kici abincinki nima ki ajiyemin nawa zandawo naci "

Tai murmushi ta share hawaye tace "nagode yaya "

Ya kalleta ya fita, bawai dawoma abincin zeba dan kawai tade ci natan shi bata abinci yake ba yasamu ya gama da hjya tukun,

da shigarshi gidan hjya yaganta fuskarta kumbure ,ya duka gaisheta"hjy ina kwana? "

tace"bawannan ba saki nawa kaimata?"

yayi shiru ya sadda kai gabanshi na faduwa,

Ta daka mai tsawa "bada kai nake ba shin baka saketa ba kenan?"

yayi shiru kanshi kasa de yana durkushe, tace"wlh khalil ka rako maza duniya, sammm bakai kama da namiji ba, matarka ta zagi mahaifiyarka ka kasayin komi akai da wani ne wlh seya ci ubanta sannan yatura ta gidan ubanta"

"katashi kaje ka saketa tunda sena koya ma yadda ake nuna bacin rai "
Chapter 79 · 0% Book details