← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 130

Sashe 62

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy tuni bacin idonta ya kau taja dogon tsoki tace"banza sokuwa har seki tsaya bakin cikin kishiya ya kashe ki? Bayan fahad ba yayinki ya dena ba dan batan basira seki kwance taita yin yadda taso kenan? To bari kiji kitashi ki wartsake kifita ki kane kane da gidanki sede in ita ta tare daki, in kuma kikai sanya ita taita yadda taso ki kumshe dakin sakarai kawai, da batasan miya dace ba, ga saudat can da kishiyoyi amma ko maganar su batayi don ta masu fintinkau duk tsoronta suke se ke babbar banza se ankoya miki, seki tashi kifara hidimarki inkin ga dama "diffff takashe kiran,

Aisha tai tsit tana nazari batajin fadan mommy dan kotayi fada tana fadin mafita, tana niyyar tashi fahad ya shigo,

ta sakar mai murmushi ya meda mata hannunshi biyu acikin riga,

Tana kallonshi tace "good morning sweetheart "

Yaida isa kusa da ita ya zauna ya taba wuyanta yace "how are you feeling today"

Tace "better naji sauki "tana marmara ido

Ya sauke ajiyar zuciya yace "alhamdulillah I'm happy "

Aisha tadora hannu tana shafa sajenshi tace "thanks I missed you "

Ya lumshe ido yace "me too "

Ta sauka akan bed din tace "I'm going to the kitchen "

Yace "OK thanks you muje nima I want to sleep "

Suka fita tare,

faseelat naganin amira ta haddace don tana da kokari seta tashi tabarta tatafi kitchen don yin girki ita kuma amira ta cigaba da karatun,

Faseelat nashiga kitchen tai tsaye tana nazarin abinda zatai, ta yanke shawarar yin grilled fish da vegetable sandwich and black tea,

Shaf shaf tafara aiyukanta, Aisha na saukowa taji kamshi ta rike kugu ta shiga kitchen din taga faseelat daga ita se short tight trouser da armless riga tana ta aiki bako kallabi,

Aisha tabi bayanta da kallo cikeda kishi da balai tace "banza marar kamun kai mtswwwww "tana ta ballamata harara,

Faseelat ta juyo ta sakar mata murmushi ta kalleta up and down ta koma ta cigaba da aiki Dan bata da lokacinta ,

Aisha taja tsoki ta fita ta koma daki kamar zata fashe taita zagaye haushi takeji bataso fahad yaci abincin can,

Fahad na komawa ya samu amira nata karatu ya wuce ya haye gado ya kwanta,

Amira da kejin bacci ta tashi ta cire Arabian hijab din jikinta ta haye kan gadon ta matsa can kusa da babanta,

Fahad daketa kallonta yakara jawota jikinshi yace "har angama karatun? "

Ta daga kai tace "I'm sleepy "

Yace "OK sleep well"
Ta rumtse ido yana ta kallon fuskar ta yadda take matukar kama dashi duk duniya ba abinda yakeso kamarta ahaka shima bacci ya daukeshi,

7:30 faseelat ta gama ta harhada su a dinning table tafara aikin gyaran gidan kuma,

Se 8:00 ta shiga dakinta don ta gyarashi ta shiga wanka shi kadai ya rage mata ,

Tana shiga tagansu kwance sunata bacci ya makalkale abarshi ajiki,

Tsaye faseelat tai tana kallonsu cikin burgewa she wish amira is her daughter ta daga kai tace "Allah amin "tanata kallonsu tafara aikinta kwatakwata ma ta mance ciwon jikinta burinta gidan yayi tsafff,

Tana cikin aikin wayar fahad da baya kasheta kullum tana bude tafara ringing ,so daya ta kalli wurin ta cigaba da hidimarta,

Har ta shiga ta gyara dayan bedroom din wayar na ringing sede ringing din is very low,

Batabi takan wayar ba ta shiga toilet tana wankewa,

Shi kuma fahad umma ce keta kira, batasan zeyi aure ba se jiya kannenshi suka gani a instagram, tun lokacin taso ta kira amma dare yayi tabari har yau dukda de tasan baze dauka ba,

Har faseelat ta gama tai brush tai wanka ta gasa jikinta ta fito wayar na ringing ,cikin mamaki wake ta kira haka tana goge fuska da tawul ta matsa ta leka screen din wayar sunan da tagani yana yawo ya matukar bata mamaki *(bad woman)* keta yawo a screen din wayar, faseelat ta zaro ido waje gabanta na faduwa dukda batasan me kira ba.

*kusa nifa inbaku comments da yawa wlh barin typing zanyi har se randa nagadama don nima nagaji* eheee
[8/5, 6:09 PM] +234 815 712 7134: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

6⃣0⃣

*Dedicated to my fan's*

*Dan Allah ina cigiyar marubuciyar laifinane na manta sunanta amma tana cikin intelligent writers asso...,shiru ta boye me number dinta ya bani plssss donni fan's dinta ce*

Har kiran ya yanke ,tai shiru tana tunani to wacece kuma Bad woman? ganin batada amsa ta wuce tafara kimtsa kanta, bayan yan shafe shafe ta dauko wando pencil black color da yellow din riga da gyale black ta saka kayan ta zauna ta gyara gashinta tai styling dinshi wani ya zubo gaba ta dan kwantar dashi cikin gyalenta ta dora tana cikin fesa perfumes fahad ya bude ido ya zubasu kanta,

Tagama komi ta kara gyara daurin dankwalinta ta dan jujjuya taga komi yayi sannan ta juyo wurinsu fahad,

Fahad daketa kallonta tun dazu yana murmushi ganin yadda take ta kara gyarawa yayi sauri ya rumtse ido,

Faseelat ta isa wurinshi ta sunkuya tafara hura mishi iskar bakinta a kunne,

Dariya ta kufce mai yayi sauri ya rufe kunnenshi da kafada ,

Faseelat ta mike tsaye tana mai wani kallo tace "dama idonka biyu kenan ,oya tashi muje kayi wanka breakfast is ready there waiting for you"

Fahad ya bude ido yace "nai wanka kikace fa? Aini ke zakimin wankan "

Faseelat tai fuskar tausayi ta kalli jikinta tace "see me I already take my bath, harnayi kwalliya "

Fahad ya kalleta from head to toe ya tabe baki yace "I seen you ke bakisan kinfi kyau a tube ba? Shiyasa nakeso kimin wankan daga can seki kara kema "

Faseelat ta rufe fuska tana dariya tace "nide katashi kayi wanka "

Ya tashi ya rungumo ta ta baya yana sunsunarta yace "kinyi kyau sosai "

Tace "thanks you it's all for you "

Ya fiddo ido "haba? To bari na biya kwalliyar" ya jirkitota yafara aika mata da kisses, faseelat ta rika tureshi tana dariya take cewa "let me be I'm very tired "

Yaki denawa, dariyar su ta tada amira daga bacci ta bude ido ta tashi zaune,

Fahad yayi sauri ya Saki faseelat ya shige toilet,faseelat ta matsa wurin amira tace "princess kintashi kenan taso muje nai miki wanka muje muyi breakfast"

Taja hannun amira suka fita a dakin amira taimata wanka tasa mata kaya desame kala da nata tai mata simple makeup ta kamo hannunta suka fito,

Aisha ma gyaran daki tayi, ta zauna ta tsara kwalliya ta saka gownt ta shadda ash color ta fito ta shiga dakin amira ganin batanan yasa taja tsoki tace "wlh bakiisa ki batamin tarbiyar yarinya ba"

Ta fita ta sauka dining tana ta jin haushi, ta bude kula tai serving din kanta ta zauna tana ci don yunwa takeji saboda bataci abinci jiya ba, jin abincin yayi dadi zauu, ta ya mutsa fuska tace "a banza "

Faseelat dakin ta suka wuce fahad na gyara bottom din rigar shi Ta bude dakin, ya juyo yana kallonsu cikin burgewa, itama faseelat Kallonshi take tayi tundaga kasa zuwa sama shikuma yasaka yellow jeans da black shirt yayi matukar kyau jikin rigar an rubuta hug me darling, da yellow din rubutu,

Faseelat ta saki hannun amira taje ta rungumeshi ta dago tace "hero kayi kyau"

Yaja hancinta yace "ai ban kaiki kyau ba "

Amira ta taho tai tsaye fahad ya jawota jikinshi, zuwa can yayi breaking hug din Ya dauko waya yafara daukarsu selfie sunata farin ciki,

Bayan sun gama hannunshi rike da faseelat while amira na dauke a dayan hannun suka fito,

Aisha da take cin abinci ta dago tana kallonsu suna saukowa daga step ganin kayan jikinsu taja karamin tsoki,

Suna isowa fahad ya Saki hannun faseelat yaja kujera ya zaunar da amira yajawo ta kusa da Aisha ya zauna, faseelat ta zauna ta kusa da tashi,

Fahad ya kalli Aisha yace " nasan dole kiji yunwa dama "

Aisha tai murmushi ta kai fork baki,

Faseelat ta kalle ta tace "anty ina kwana ya jikinki? "

Aisha ta tsaya da taunar sandwich din bakinta, ta harari faseelat tace "naji sauki "ta yatsina fuska,

Faseelat tai murmushi kawai fahad daketa kallon faseelat yace "sarve us please kinyi zaune"

Faseelat ta tashi tsaye tana fadin "sorry my hero "tafara sarving nasu,

Aisha taita kallon faseelat tana mamakin ta wlh idan itace bazata taba sakin jiki ba, amma ita ko kunya bataji ta saki jiki ko nauyin Aisha bataji wai hero su Hero manja,

Ta zuba mishi ta ajiye a gabanshi ta dauko fork da knife ta dora mishi ta zuba mai black tea din ta ajiye,

Yace "thank you kinsan nakagara nafara ci don hanci na kadai ya tabbatar da dadin abincin "ya dauki fork yafara ci,

Faseelat tayi murmushi ta zubawa amira ta zuba nata ta koma ta zauna tafara ci,

tsitt wurin yayi se karar cokulla da wuka, Aisha ta kalli amira da fahad da suka dage cin grilled fish ta tabe baki aranta tace "see them plsss kamar basu tabacin grilled fish ba "

amira na taunar kifi tace "daddy! "

Yace "uhummm"bakinshi cike da kifi,

amira tace "wai nan anty Zatai ta kwana ne? "

Fahad ya kalli faseelat da take ta kallon amira suka saki murmushi,

Fahad ya meda kallonshi kan plate dinshi ya dauko tsokar kifi zai kai baki yace "siyo miki ita nai princess nan zatai ta kwana "ya kalli faseelat

Faseelat tai dariya ta kalli amira,

amira tace "daddy siye kuma? "

Yace "yess princess tariga ta zama tawa tana nan tare damu nangaba ma zata haifar miki sister "

Faseelat ta sunkuyar da kai tana dariya, fahad ya Saki murmushi, Aisha ta tashi fuuuu ta haye sama, kallo daya ya ma bayanta ya dauke ido,
Chapter 62 · 0% Book details