← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 130

Sashe 45

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta medo hankalinta kan Aisha taja ta tazaunar daita kan cushion tace "haba Aisha inafada miki abinda yakamata kiyi kina kaucewa, kiyi hakuri kibari ayi auren karkimanta fahad a tafin hannuna yake ya daukeni tamkar uwa, ba abinda waccan zata fiki awurinshi inde zakibi shawarata "

Aisha takara saka kuka mommy nata ban baki amma taki denawa,

Seda fahad yafara zuwa hospital akai mishi dressing sannan ya taho gidan mommy,

Yana shigowa ya gansu main pallow yaude fuskar mommy ba walwala dan taji zafi da ya mari diyarta akan wata,

Yazo ya zauna gefen kujera Aisha ta dago ido tana kallon hanninshi da bandage ta cigaba da kuka kanta kan cinyar mommy,

fahad yace "Aisha kiyi hakuri kizo mutafi gida banso na dakekiba "

Aisha batace komi ba mommy na kallonshi tace "inaganin kabarta anan ta danyi kwana biyu tadan samu natsuwa sannan se ta koma don naga duk tafita hayyacinta, kayi hakuri daita da duk abinda zatayi anan gaba, nide namata duk nasihata taki ji "

Fahad gabanshi ya fadi don be tunanin zeiya 2days batare da matarshi ba wannan nema yasa yake tafiya daita duk inda zashi,

Cikin rarrashi yace "Aisha kiyi hakuri mukoma gida, kinsan bazan iya kwana nikadaiba "

Ta dago fuska ta watsa mishi harara ta meda kai kan cinyar mommy,

Mommy ta canza maganar tace "dama inadawowa daga gidan kawunku se gata ai naso nakiraka tazo ta hargitsamin lissafi, naje nasameshi munyi magana yace kaje kuyi maganar kasameshi a office "

Aisha tatashi ta haye bene dagudu jin abinda mommy tace

Fahad Yace "Nagode mommy bari naje nasameshi "

Ya tashi yafita yaja motar zuwa gidan kawunshi rabiu,

Yana fita mommy taja tsoki, tace "dole fa intashi tsaye kar abinda na raina yazo yafi Karfina "

Fahad har cikin office din alhaji rabiu ya shiga ya zauna suka gaisa alhaji rabiu yace "danbaba mommynka tazo mun da maganar kanaso ka kara aure, naji dadi sosai ka girma kazama babban mutum ai karin aure sunna ce kuma mutum nakara girma,sede bata fadamin gidansu yarinyar ba nace ta turoka muyi maganar"

fahad yayi murmushi yace "Daddy sunanta faseelat gidansu a kofar durbi yake bazawara ce babanta sunanshi alhaji maaruf "

Alhaji rabiu yayi dariya yace "ai zawarawannan ma sunfi hankali da dadin shaani yanzu yaushe ka ke ganin zanje na musu maganar mommynka tace bataso bikin yafi wata amma inaso naji ta bakinka "

Fahad yayi dariya yasan kawunshi dama da barkwanci yace "yau nikeso inde akwai damar hakan, kuma su zasu zabi tym sede banson komi daga garesu kuma inaso ayi komi kamar auren budurwa "

alhaji yayi dariyar manya yace "to maganar kudi fa? "

fahad yace "zan rubuta maka chek kaje kacire yanzu de kafara zuwa tukun, anjima zan kawomaka kudin "

Alhaji yace "to yayi Danbaba Allah yasa ayi damu "

Fahad yace "amin se nazo anjiman ya tashi yafita "

Shiko abba gidan baba babba yawuce dan suyi shawara dan bayayin komi seda shawarar shi,

bayan an mashi iso ya shiga alhaji yace "lpya kake naganka somehow kamar kana cikin damuwa "

Abba yace "tunda safe asiya tazo takecemin bataga faseelat ba se yanzunnan gata tadawo jikinta duk jini wai taje wurin yaron sunyi lalata inaga, ni tundazunma muna ciki muna tattaunawa da ita akan batun saboda jiya matar yaran takira ita faseelat taci mata mutunci d daddare har mungama yanke shawarar tirsasata ta rabu dashi sega wannan abun "

baba babba yace "subhanallahi ashsha abu be dadi ba "

abba yace "shine nayi shawarar fadama yaron ya fito amma yakace? "

Baba babba yace "hakane dede ayi mishi magana yafito inda gaske yake, tunda gashi har yayi mata fyade, tunda ai tataba aure this means dakarfi ya kwata "

abba yace "to Allah masani nima abun ya dauremin kai amma tunda tana sonshi zanmasa magana yafito ayi musu auren suje can su cinye kansu tunda da kafarta tabar gida ai "

Baba babba yana jimami yace "Allah ya kyauta "suka cigaba da labari, sannan sukai sallama abba yawuce wurin kasuwancinshi.

Kafin sha biyu zazzabi da ciwon kai me zafi ya rufe faseelat, ummi Takoma dakin da niyyar takara cin ubanta ta sameta cikin bedshit dukunkune taja tsoki tafita tana ta maganganu ita kadai ta dora bagaruwa da karamfani da dankumasu da ganyen magarya saman wuta ta dahu sosai ta tace ta cika uwar robar wanka takai toilet tazo ta yaye zanin gadon da faseelat ta rufa dashi tace "kitashi ki tube muje nagasa miki jiki in Iskanci dadi ne gobe seki kara zuwa sakarai wadda batasan ciwon kanta ba, "

Faseelat dakyar jikinta yayi tsami ta mike zaune tafara jijjiga kai, zataiwa ummi magana,

Ummi tace "karki cemin komi anan kitashi ki abinda nace "

faseelat ta sunkuyar da kai cikin tausayin kanta ta tashi ta daura zane tana dafa bango zata fara tafiya ummi ta kamata tajata har cikin toilet ta zame mata zane cikin bacin rai tace wa faseelat ta shiga ciki,

Faseelat tafara matso kwalla ganin yadda ruwan ke suraci,

Ummi ta daka mata tsawa jiki na bari ta shige ta zauna ciki tanata cije lebo Tana rumtse ido saboda zafi.

Bayan wani lokaci
Ummi tajawo karamin towel ta rika tsomashi tana mammatsa wa faseelat jiki tanayi tana mata fada hawayen azaba yarika wankowa daga idon faseelat .

Team faseelat kuje ku fadawa ummi ba abun bane tukunna 😂

all teams ana tare 💋
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELENKU)*💃🏼

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

5⃣0⃣

*🎶🎶ashe haka soyake shiga zuciya yake,yasamu wurin fake cireshi wuya yake 🎻🎻🎸araina kena rike ,kimance komi kirike, koina kin mallake, nakine amshi kirike🎼this page is for you lady my habibaty Nagode da alherin da kikamin Allah yakara budi, thanks once again lady*

*Dedicated to lady*😘😘

Ummi nagama gasa mata taja tsoki tace "shasha kawai seki tashi ki wankan abinda kukai kizo ki amshi magani "

Tafita tabar mata toilet din, faseelat ta rufe ido da hannu daya tana kuka, ranta na mugun baci idan ummi taimata mummunan zato ,bare na yau da har abba seda yaji, ta share hawayenta tafito tai wanka saboda ruwan da ummi tai mata gashi sunyi duhu dan haka tasaka soso da sabulu ta wanke jikinta ta fito ta koma daki tasamu tasaka vest ta koma ta kwanta,

Wajen 2:00 ummi ta dawo da abinci da paracetamol and ibuprofen tana kallon ta tace "kitashi kisha magani seki koma ki kwantan"

Faseelat ta tashi zaune tana yamutsa fuska tai spoons biyu na jelop din pasta din ta dauki maganin tasha, duk ummi na tsaye na kallonta ta koma ta kwanta,

Ummi tadade tsaye tana kallonta sannan ta dauki plate din tafita,

Karfe 3:00 abba ya dawo, bayan ummi takawomishi abinci yaci yake bata labarin yadda sukayi da baba babba,

Ummi tace "ai gwara dakamishi maganar dan faseelat tayi nisa inajin yadda takeson yaran nan koni bataso haka "

Ana haka akaiwa abba sallama ya tashi ya fita, ganin sabuwar fuska dabe taba ganiba sukai musabaha da alhaji rabiu,

Sannan alhaji rabiu yace "nasan baka sanniba nine kanin mahaifin fahad yaron dake neman yar wajenka, nazo ne neman izini muzo neman aurenta "

abba yace"to alhamdulillah sede banine madaurin aurenta ba, don haka zan baka number din yayana shi medaura mata auren se kuyi magana dashi"

Alhaji rabiu yace "to masha Allahu badamuwa "

abba yabashi number din baba babba tareda yimishi kwatancen gidanshi,

Alhaji rabiu gidan baba babba yawuce sukai kicibus kofar gida dede shi kuma ze fita, bayan Sun gaisa yafadi abinda yakawoshi, baba babba yace "bamatsala zakuiya turowa amma zuwa gobe don zan danyi tafiya zuwa niger,"

Alhaji rabiu yace "alhamdulillah haka ma yayi insha Allah munanan zuwa goben"

Baba babba yace,"Allah yakaimu lpya "

Alhaji rabiu yace "da karfe nawa zamuzo?"

baba babba yace "zuwa de 10 to above"

Alhaji rabiu yayi godiya ya tafi,

Fahad bayan ya bar wurin alhaji yawuce gida ya kimtsa yafita aiki, zuwa 3 ya dawo tunda ya shigo gidan yaji gidan ba dadi, yanata kallon falon da yanzu amira nanan na wasa, tunanin Aisha yafado mai da yanzu tazo ta tarbeshi ,ya samu kujera ya zauna ya fiddo waya ya kira Aisha tana ta ringing taki dagawa, har ta tsinke ya ja tsoki besan haka aisharshi take ba sedaga jiya zuwa yau,

Ya tashi ya haye sama ya watsa ruwa yayi sallah, ya shiga kitchen ya hada ruwan tea ya dawo dashi ahannu da snack ya zauna yana ci yana latsa waya ya shiga gallery ya latso pics din faseelat yana binsu one by one yana kallo besan meyasa ba ko kallon pic dinta kadai yayi seyaji yana samun natsuwa sosai,

Aje tea din yayi dukda bawani abu yaci ba rabonshi ma da abinci tunjiya amma yakasa shan tea din saboda rashin kwanciyar hankali,
Yayi dialing number faseelat yanabin screen din da kallo yaji tana kashe abun yabashi mamaki jin wayarta kashe ya tashi yakoma bedroom yana aiki da system dinshi yaji yanajin bacci ya kwanta ,yana baccinshi har 4:30 sannan yatashi yana duba agogo yayi sauri ya tashi ya shiga shaf shaf yayo alwala ya dawo ya kabbara salla ,

aisha ko tasha kuka har tagaji, mommy de batako leko taba tunda batajin magana ta shareta,

ramlat tashigo dakin tazauna gefen Aisha tace "anty maganar da mommy ke fadamiki fa gaskiya ne, yanzu an waye kishi da kissa ake baa fitowa aita haukannan nide kinmun dede da kika jibgi shegiya Amman tunda kin rage zafi seki hakura kinga har mommy tayi fushi tafita har karki ,kiyi yadda tace kurum tun kafin asamu matsala dan kinga fayanzu har marinki yayi akanta nangaba Allah abinda yafi mari ze miki, kirika daurewa de hakanan"

Aisha tana kallonta tace "yanzunnan yaya har seya iya kwana da wata baniba ?"

Ramlat tace "namiji nefa, cabb bare yaya da dama can beda wata kunya sosai, kinagani agabanmu se ya rungumoki ko yamiki kiss fa ,aikede ai shaani kawai "
Chapter 45 · 0% Book details