← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 130

Sashe 126

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

A labour room doctor yayiwa faseelat allura pain killer,yamata steeching don ta karu sosai ,tana ta kuka suna mata sannu,

Doctor da keta mata sannu tunda ta haihu yace"why are you crying ?ki godewa Allah kin haihu lpy duka yaranki na lpy "

Hawaye sunata zuba murya harta sauya yanayi tace "my husband ,where is he ?inason ganinshi inason sanin halinda yake ciki"

Doctor yace "OK OK ki kwantar da hankalinki mijinki ze samu lpy ,"

Faseelat ta fashe da kuka me sauti tace"I want to see him inason sanin halin da yake ciki"

Yayi tsaye yanata kallonta ,tana ta kuka,ko sanin me ta haifa ma batayi ba,

Ya kalli nurse dake tsaye tana kallonta yace "ki samo mata kaya ,sannan ku kaita room nashi"

Nurse tace"OK "ta juya tafita,

Yace" its okay yanzu zaki ganshi stop crying "

Ta cigaba da kukanta ya juya ya fita,

Su sabeer Allah ya temaka cikin be zube ba sede jini yazuba sosai akasa mata jini,

Nurse ta dawo da doguwar riga ta mikawa faseelat ta saka tanata kuka ta kawo kujera me taya dakyar da cije lips faseelat ta sauko agadon ko mikewa sosai bata iyawa tahau kujerar nurse ta turata zuwa dakin da fahad yake,

Su mommy suna bakin kofa sunata kuka akawuce daita ,

Suna shiga dakin taga halinda yake ciki hawaye suka kara wanke mata fuska t shirt dinshi duk jini ,

Nurse ta turata bakin gadon ,faseelat ta dora kai jikin gadon tasaki kuka ,

Fahad ya dago hannun da jini ke shiga ze tabata nurse tai sauri ta rike hannun tace"noo plsss" tameda hannun

Faseelat ta dago tana kallonshi idanunshi jawur dasu yanata hawaye yaketa kallonta ,

Faseelat tasa tafin hannunta cikin tafin hannunshi ya rumtse yana cigaba da hawaye ,

Murya shake yace"I'm sorry I didn't help you I'm very sorry"

Faseelat ta girgiza kai tana kuka tace "basuyi ba hero Allah be basu ikon haka ba ,kayi hakuri nasan u r in so much pain"

Ya rumtse ido yanajin fin rabin ciwon jikinshi ya tafi ya bude yace "thank god for helping us"

Nurse idonta yacika da hawaye itama ,

Ya kalleta ta dawo single dinta yace "where's my babies inafatan ba abinda ya same su?"

Tana murmushi tana hawaye tarika daga mishi kai ,

Nurse ta fita dan kawo yaran koya rage pain in yaga kyautar da Allah yamishi ,

Tana fita faseelat tace "they are 5 in numbers"
Dukda batasan sex nasu ba amma tasan ta haifi biyar,

Yayi murmushin farin ciki yace "sure?"

Ta daga masa kai ,

Yace "thank you so much"

Takara daga kai tana murmushi da hawaye ,ta kalli kafarshi dake lullube da bandage ,

nurse ta shigo tareda Umma data kasa ta tsare wurin yaran suna kwance
A babies bed ,ta turosu har zuwa bakin gadon,

Fahad da faseelat sukabi yaran da kallo suna farin ciki matan ansamasu kayan mata mazan ansa masu kayan maza,

Fahad yayi ta murmushi yana bin fuskokinsu da kallo ya dago ya kalli Umma yace "Umma kingansu duk yarana ne"

Umma ta daga kai tana share hawaye ,

yafara yunkurin tashi zaune nurse ta rikeshi tace "dole ka kwanta karka bata aikin da akama "

Ya kalleta yace "plsss let me seat zaniya plsss"

Da Umma da nurse suka temaka suka jingina shi jikin bed din ,

Ya kalli Umma yace "Umma kibani Su nagansu I'm very happy"

Umma tai murmushi ta dauko namiji ta dorashi jikinshi ,yana rike da hannunta,

Ya kura mai ido yanata annashuwa kamar ba patient ba ya kalli faseelat yace " u look alike "

Faseelat tai dogon murmushi ,ta daga mai kai ,

Ya cewa Umma ta kawo shi Dede bakinshi ya mishi huduba ,

Ta daukeshi ta Dora wani shima kamar faseelat shima ya mishi huduba ,

Akadora baby girl ya mata da duk yanuwanta ,tunda aka Dora ta farko aran faseelat tace "Aisha"
Ta biyun tace "amira"
Ta ukkun kuma she don't know,

Yanata murmushi ya kalleta yace "I name them abdullahi da abdurrahman ,the baby girls kuma my Aisha ,amira and...."

Tai murmushi tace "and what?"

Yayi murmushi yace "and....and faseelat I will call her *(habibaty)*

Faseelat tai dariya duk Su Umma suma sukai dariya ,

Ya kalli nurse dake dariya yace" thannks"

Tace"congratulations "

Ya meda kallonshi gun Faseelat tana murmusawa tace "I love you Allah yabaka lpy"

Yayi murmushi me ciwo ya kalli kafarshi yace "I wish so"

Nurse tace"madam u need to rest zanme dake dakinki kiyi feeding babies "

Faseelat tace "plsss I don't want to kibarni nan"

Nurse tace "noo its not possible"

Taja kujerar ta faseelat nata wai genshi yanata kallon ta suka fita Umma tabisu da gado daya ,nurse ta dawo ta dauki sauran,

Fahad ya lumshe ido yanajin matsanancin farin ciki,

Bayan faseelat takoma saman gado aka bata diya daya ta fiddo nono da sukayi tunjum ta jona mata yarinyar takama ,
Umma ta fiddo dayan takama wa dayan yasha tanata mata sannu sannan aka medasu akabawa sauran tai musu addua sannan aka fita dasu Umma ma takoma wurinsu mommy ta zauna,

Ummi ce tafado mata arai ta dauki waya ta kirata memakon tafada mata abinda yafaru setace mata faseelat ta haifi yan biyar tafada mata asibitin Ummi nata murna tafadawa Abba ta kira omer tafada mishi yayita murna takira wasu yanuwanta kowa nata murna Abba yakira baba babba sunata sa musu albarka,

Omer duk yariga su isa besamu ganin faseelat ba se yaran sunata santinsu shida fadeela ,lokacin Ummi ta shigo sunata murna suma,

Ummi nashiga wurin faseelat taga ta baje ba dankwali ta ciro nata tana dora mata ta farka tafara hawaye tana bawa Ummi labari,

Can sega sabeer yazo dayaga halinda fahad ke ciki yakara shiga tashin hankali amma abun mamaki farin ciki ne falll kan fuskar fahad,

Sabeer yace "sannu friend Allah yakiyaye gaba yabaka lpy "

Fahad yayi murmushin takaici yace"they took all the money nasan bazasuyi hakuri ba kudin na dayawa kudin sun kai 100millions dollars nide bana dasu duka accounts dina befi 50millions dollars ba zan baka kaje kaciro su kuma I Will talk to daddy zanbada decoment na properties nawa abiyasu kudinsu inyaso ko akwai saura I will pay after"

Sabeer yayi tagumi hawaye suka ziraro masa, fahad yayi murmushi yace"stop crying plsss this is my destiny banijin komi "

Karfe goma saura gomna ya dira asibitin hakan yajawo yan jarida da yan labarai,

Sunata dauka suka shiga wurin fahad gomna ya mishi jaje ya tambayeshi nawa suka daukar mishi kuma ya sansu ?

Fahad yayi murmushi yace"I don't know them kuma kudin masu yawa ne 100millions dollars amma bakomi wannan jarabawa ce kurum kuma na amsheta da hannu biyu I will repay back there money"

Governor yace"zan biya rabin kudin kuma yau zaa fitarda kai waje insha Allah zaka samu lpy zaka taka da kafarka"

Fahad yayi murmushi yaita godiya yana faraa,

Governor yace"kuma nai maka murna da samun yara biyar Allah yaraya su akan musulunci"

Fahad yanata murmushi yace "amin nagode"

Me girma Governor yatashi anata video ting

Suka'isa dakin babies sunata bacci abinsu su biyar ringis Governor ya dauka yanajin dama nashi yanata murmushi ,

Sannan suka nufi dakin faseelat duk yanuwanta na waje ciki da Ummi da Umma da baaba ,

Governor nashiga suka mimmike suna gaisuwa Ummi kamar tasani data dorawa faseelat kallabi,

Governor ya zauna ya musu barka sunata godiya ,idanun faseelat luhu luhu,

Governor ya mata kyautar mota yabawa yara big plat house ,faseelat tai ta godiya amma sam ba faraa fuskarta,

Sannan governor da guguwarshi suka tafi,

Nan akafara shirye shiryen fita da fahad ,

Shima hankalinshi duk tashe yake don rabuwa da heart beat nashi da babies dinshi,

Itama faseelat dataji hawaye tai tayi,

Karfe goma dawani abu mommy ta samfe tatafi wurinsu oteka ,

Tana zuwa ta samu dukkansu sunyi jungum jungum duk zugar matannan basanan se guda ukku ,

Anwa oteka dressing hannunshi yanata zukar shesha dan yarage bakin ciki ,

Mommy batako zauna ba tana hawaye tace"haka mukayi daku ?nace karku tabashi kudin kawai zaku amso donme zaku harbeshi ?"

Tiger ya kwatsa mata tsawa yace "karki wannan kuskuren anan yanzu kinji ki lahira"

Oteka yayi karamar dariya yace "let her batasan me mukayi asara bane"

Ya wurga mata jajayen idonshi yace"we lost 2 of us sannan look at my hands danhaka yarjejeniya ta sauya"

ya kalli die hard yace"bring that money here"

Ya tashi ya jawo katon akwatin ya bude shi gaban oteka,

Oteka yace"divide all the money in to 3 ka kwashi kaso biyu ka shigardasu kabata 1 tatafi "

Mommy taita hawaye tana kallonsu tana kara nadama ,

Ya kalleta yace "ke dole kibiya diyyar yanuwanmu da muka rasa ga kudinki ki kara gaba"

Mommy tace "Allah yaisa se Allah yasakamin aiba haka mukayi daku ba"

Die hard ya kwasheta da mari a 2 kumci ta dafe kumatu tana kuka ,

Ya bude akwatin yakara kwasar boundles daga cikin nata yakara anasu ya tura akwatin yace "kwasarsu ki tafi wicked woman"

Mommy ta kama hannun akwatin ta kama hanya tana kuka har ta kai kofa ta juyo takara cewa "Allah yaisa"

Tiger yace "keeeee !!!!" Ya mike haba kafa minaci banbaki ba ta arce da kalilan din kudinda suka bata,

Har ze bita oteka yace "let her taji da bakin cikinta"

Mommy takai kudin mota tana kuka take driving tana zuwa gida tadora akwatin can saman wardrobe takoma asibity,

Labaran karfe sha biyun rana harda nasu faseelat ,dama da safe anyi na kaiwa Governor hari da yanfashin sukayi ,

Nan labarin ya fara zagaye duniya ,lokacin da manager yaji labarin sabeer yakira yafara masifa se anbiya duk kudin wannan abun shiri ne ,sabeer ranshi ya baci yace yau zaa biyaka kudinka gabadaya ,

Ba bata lokaci yafara bugabugar fiddo kudin fahad yana hadasu ya amso na governor ya damkawa manager,

Karfe 7 jirginsu fahad ze tashi zuwa turkey a can akwai kwararrun likitocin kashi da zasu dubashi,zasu tafi da Umma daddy ma zebi bayansu ,

Faseelat datasha wankan jego tadan gasu tana tafiya tana dan dingisawa taje dakin fahad ,

Mommy na wurinshi tana kuka shima kebata hakuri ,faseelat taje ta rungumeshi tana kuka tace "inaso nabika inaso nai jinyarka plsss"
Chapter 126 · 0% Book details