← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 130

Sashe 81

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

ummi na zaune da baki dake zuwa mata murna ya shigo dakin kallo daya ta mishi tagane ba lpy ba, muryarshi na rawa yace "ummi faseelat bata lpy yanzu haka suna asibity "

Ummi tace "subhanallahi miiyasameta ne? "

Idanunshi jawur yace "inaga tayi miscarriage ne "

matan dake dakin suka taya ummi sallallami ummi ta mike jikinta har rawa yake ta dauko hijab tace "mutafi asibitin naganta "

omer ya fita ummi na bayanshi Suka shiga mota suka kama hanyar hospital din,

acikin emergency room anyiwa faseelat allurar tsayarda jini jinin ya tsaya akamata allurar bacci akasa mata ledar jini don sunada jini a blood bank, sannan aka fito daita,

Fahad na durkushe yaci kuka har yagaji aka fito da faseelat ya tashi jikinshi na bari ya bi bayansu aka shigarda ita awani daki suka kwantar daita yayi tsaye yanata kallon fuskarta da ta kumbura gashi har yanzu bata dawo hayyacin ta ba ,

nurses nagama shiryata suka juya suka fita adakin fahad yakarasa bakin gadon yayi kneeling ya dora kai jikin gadon yana zubar da hawaye yana sambatu "nacuceki faseelat na rabaki da farin cikinki nayi sanadiyyar zubewar gudan jini na ihate myself kiyafemin plssss..."

Dukda saurin da omer keyi ummi gani takeyi kamar baa tafiya dandanan ta tambaya baaisa asibitin ba?

Har suka isa sunata sauri su dukan burinsu suga halin da take ciki,

omer yakira bello yazo ya samesu suka tafi ya nuna musu dakin yana jimami, be iya shiga dakin ba ya juya,

su ummi suka tura dakin suka shiga, fahad na durkeshe suka shigo ya dago face duk hawaye ya kallesu seda gabanshi yafadi ganin su awurin adede wannan lokacin,

Dasauri ummi takarasa kan bed din ta zauna gefe fahad ya matsa yabata wuri kanshi kasa, ganin halinda faseelat ke ciki ta fara salati jikinta nata rawa fuskar faseelat kamar ba tata ba ga jinin da yake jikin zanenta daba a sauya ba, ummi ta juyo ta kalli fahad tace "wai miyasameta ne accident tayi komi? "

Fahad yayi shiru kanshi kasa, ummi tace "I'm asking u meyafaru? "

Fahad yace "accident ne"Muryarshi a sarke

ummi hannunta na rawa ta kaishi bisa kan faseelat ta shafoshi hawaye suka gangaro mata,

omer tunda ya shigo yaga halin da take ciki ya rungume hannayenshi zuciyarshi awuya se cije lips yake dan ya riga yagama observing abinda yafaru,

Suna haka for some minutes har lokacin fahad na zukunne se amira tafado mai arai yadda Aisha tafita daita batako numfashi ya dago kai dasauri,

ya yunkura ya tashi jikinshi a mace yabar dakin ,ya nufi office din doctor okato,

Omer yakara matsawa gaf da gadon ya kurawa fuskar faseelat ido besan lokacin da hawaye suka zubomishi ba,

Ummi da take dafe da kanta tana hawaye ta waigo da kanta tace "omer kaina ya kulle wane irin accident ne wannan?jibarta duk yadda takoma lokaci daya kamar ba faseelat dita ba"

Omer jijiyoyin kanshi awaje yace "bawani accident ummi duka ne ya meda diyarki haka tun kafin bikinsu yafara marinta amma faseelat sonshi be bari taga laifinshi ba namata magana seta nunamin bazata iya barinshi ba, ki dubata sosai ga wasu tsoffin tabo nan ajikinta wanda nasan ba dasu tayi aure ba "yaida maganar dakyar kamar ze kuka,

Ummi tajuya wurin faseelat tafara kallonta daga sama zuwa kasa duk ga sashin belt nan a wuyanta be ida bacewa ba, ga wasu jikin kafafunta, bata damu da omer dake tsayeba ta dage zanen jikin faseelat sama nanma duk sashin belt ne, hawaye suka gangarowa omer,

ran ummi bace ta kalli omer tace "zoka zaremata wannan jinin dake shiga jikinta ka dauketa mutafi wani asibitin inason diyata ban bashi ita don yakashemin ita ba "

Ta matsa ta bashi wuri omer ya zare jinin ya sargafe shi ya dauki faseelat suka fita daga dakin sunata sauri,

sede bello yaga sunfito daita yabisu yana wa omer magana "ina zaku kaita kubarta plsss tana cikin hali "

Omer ko jinshi bayayi bello nabiye dasu saboda ganin bello securities basu Hana ba suna zaton an sauya musu asibity ne har bakin mota ummi ta bude mishi yasa faseelat itama tashiga ya kulle kofar, ya juyo wurin bello ya dafa kafadarshi yace "karkadamu zamu kaita better place thanks for your help "

ya wuceshi ya shiga motar yajata da gudu suka fita asibityn,

bello ya dafe kai yace "what I put my self into?"

daga alhayat specialist hospital suka wuce turai yaraduwa daita, anan ma a emergency aka amsheta ba jimawa aka fara dibar jinin omer akasa mata, kuma ana bukatar leda biyu,

fahad wurin likita ya shiga doctor yace mishi ya zauna yaki yace yanason sanin dakin da akai admitting amira,

doctor ya fadamishi dakin, fahad yafita ya nufi dakin ,

Yana turawa Aisha da tai tagumi ta dago ta kalleshi shima ya kalleta.

Insha Allah angama samun tsaikon posting bazan ko numfasa ba se na kai karshe mahakurci mawadaci ,kungama hakuri insha Allah 😍matsala tazama labari.
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

7⃣1⃣

*Dedicated to maman nour, soupnass, ikra rukayyat, maman 4H,hauwa lawal,kucigaba da comments*💓

Jiki a mace ya shigo dakin tabishi da ido tanata kallonshi mamaki kawai yake bata yasha jibgarta amma bai taba yi mata wannan jina jinan ba, kenan itama watarana yakan iya yi mata haka,

Bakin gadon amira yaje yayi tsaye yanata kallon fuskarta da yadda take nishi zuciyarshi takara cunkushewa yanajin tsanar kanshi ,ya dade tsaye yana kallon amira Aisha batace mishi komi ba yajuya yafita daga dakin tabishi da ido,

Office din doctor ya shiga yaja kujera ya zauna yana yamutsa fuska yace "me ke damun amira? "

Doctor dake duba wani buk ya dago face yace "she's very scared and shocked abun ya girmi brain dinta ,that force her to fainted ,amma she'll be okay, "

Fahad yace "what about my wife? "

Doctor okato yakara gyara zama yace " sakamakon dukan da akamata sosai tayi miscarriage sannan taji ciwuka sosai tana bukatar kulawa da lokaci kafin tasamu lpy "

Fahad ya daga kai ya hadiyi miyon bakin ciki,

Doctor yace "as ur family doctor I want to advise you, dukan mata baya taba kawo gyara sede yabata, mata wani lokaci they're crazy se ana kai zuciya nesa ana kaucemusu amma duka bedace dasu ba saboda they're weak , ina maka jajen rashi da kukayi Allah ya bata lpy"
(wani lokaci sekaga Christian da soft heart kuji yadda yake bawa fahad shawara)

Fahad yace "thanks you"

yatashi yafita yanajin duk duniyar tamishi zafi,

omer yakira abba yafada mashi suna asibity kuma ana bukatar jini ba bata lokaci segashi asibityn aka dibi nashi dana abul, aka cigaba da sawa faseelat dake kwance tana nishi,

Duk kansu hankalinsu tashe abba yakasa yadda da abun da yake gani,

ummi dataci kuka tagaji tacewa abba "wlh seya saketa yata bazata zauna da meduka ba, wannan shine karshen zamansu"

abba yace "kiyi hakuri asiya amma kidena rantsuwa cikin bacin rai, amma ni kaina bazanso takoma gidan shi ba"

ummi tace"hmmmmm"!

fahad dakin da akai admitting faseelat ya nufa ,akunyace ya tura kofar ya shiga wayam ba faseelat basu ummi yabi gadon da kallo zuwa jinin dake sargafe ,ya karasa ya tura kofar toilet nanma wayam hankalinshi tashe yakaiwa abunda ake dannawa for emergency bugu ya dauki kara, duk yaburkice ko 1mnt baaiba doctor yashigo da nurses biyu, sukaga gadon wayam se fahad dake tsaye kamar mahaukaci,

fahad jijiyoyi amike yace "where's my wife? Ina matata where do you take her? "

Doctor da mamaki yagama cika shi yace "this is unbelievable, how will this happened in my hospital? "

Ya kalli fahad yace "I'm sorry sir bansan komai ke faruwa ba amma we have CCTV cameras all around the hospital zamu gano mike faruwa"

Fahad ya dafe goshi kanshi na mugun bugawa ,su ummi suka dauketa kokuwa? Yana ta tambayar kanshi,

Doctor yadafa shi yace "meet me in my office "

Yajuya yafita tareda nurses ,hawaye suka zubowa fahad yace "meyasa zaku dauketa? Ni yadace na kula daita"

Ya fita ya nufi office na likita,likita yanata duba computer abunda yafaru akofar dakin faseelat ya juya wa fahad computer yace "take a look at them do you know them or seen them before? "

fahad ya kalli computer omer ya fito dauke da faseelat ranshi yakara baci yace "he's her brother, but saboda me zaabari sufitar min da mata a asibity su suka kawota ?yama akai suka san we are here? bazan kara kawo patient a asibitin nan ba tunda it's not safety "

doctor yajawo computer gabanshi yayi rewinding lokacin da bello yakawosu kofar dakin ranshi ya baci yaja telephone ya kira number office dinsu bello ba dadewa sega shi ya shigo yanata hada zufa,

fuska tamke okato yanunawa bello computer yace "meyasa ka kira wadannan mutanen waya aike ka? meyasa ?"

bello yace "I'm sorry nasan yayanta ne banyi tunanin fadamishi ze zama matsala ba kuma nayi iya kokarina na tsayardasu basu tsaya ba "

fahad jiyake kamar yakaiwa bello naushi don haka ya tashi yafita ,

okato yace "meyasa baka fadawa securities ba? U r suspended kaje sena nemeka "

Bello ya fara begging "I'm sorry sir it's a mistake wlh danasan haka zata faru da bazan kira shi ba dan Allah kayi hakuri "

okato ya nunashi da yatsa cikin nuna gargadi yace "next time idan haka tasake faruwa zaka bar nan harabada,now leave "

Bello yajuya yafita yana yamutsa fuska cikin ranshi yanata regretting kiran omer,

Fahad nafita yashiga mota ya nufi gidan umma don besan ya zaiyi ba, a mota hawaye yake tayi duk lokacin da ya tuno ihunta da jinin da ya zuba seyaji hawayen tausayinta Sun zubomishi,
Chapter 81 · 0% Book details