← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 130

Sashe 50

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadan kwanta idanunshi na kallon pop na dakin hannunshi daya nakan heart dinshi tana ta harbawa fat! Fat!!!, yanata tunanin faseelat, jin anyi kiran salla ya tashi yayi salla, yafara yi musu parking,

se ishai yagama har lokacin Aisha bata dawoba shi kuma gabadaya hankalinshi nagun faseelat dukda baya zuwa gunta da dare, be tsaya shawara da zuciyarshi ba ya fita da sauri ya kama hanyar gidansu yanajin inbe ganta ba koyaje ma baze iya aikin komi ba,

Omer ya fito zashi masjid yaga fahad tsaye kofar gidan, cikin jin haushin omer fahad yabashi hannu suka gaisa yace "Dan Allah kamin magana da faseelat inata kiran wayarta bata dauka "

Omer na mishi kallon up and down yace "ba damuwa "

Ya juya cikin gidan yafadawa ummi dake tsakar gida tana alwala cewa faseelat tayi bako ya juya yafita,

Ummi ta shiga dakin faseelat tace "tsuntsuwar soyayya ga tsuntsun can yazo kitashi kije kiji ko lpy"

faseelat tace "To" ta mike zaune ,ummi ta juya ta shiga daki ta kabbara salla,

Jin ummi ta shige daki faseelat ta koma tai kwanciyarta ,

Fahad yayi ta tsayuwa yanata kiranta bata dauka yaja tsoki sama da ashirin har omer ya dawo daga masjid yana tsaye,

Omer ya shiga cikin gidan ya shiga dakin faseelat tana kwanciyarta har yanzu cikin bacin rai yace "ke ba kiranki ake ba? Tundazu almost 20mnt baki fita ba, kitashi ki je malama "

Ta tashi tana share hawaye taja hijab tafita ,

Ya omer yabi bayanta ya tsaya cikin zauren gidan da ba haske can waje ko da haske daga inda yake yana hango su faseelat din,

Faseelat nafita ta juyawa fahad baya hannuwanta akan kirji ta harde su, be masan da zuwan ta ba don yabawa kofar gidan baya kuma he's busy thinking of her, kamshin jikinta ne ya sanardashi zuwanta ya juya yana Bin bayan ta da kallo,
Yace "I'm sorry cutie kishinki ne yasa har na mareki I'm regretting "

Bata juyo ba ya koma gabanta yace "nace kiyi hakuri hakan baze kara faruwa ba"

Faseelat ta dafe kunci tana tuna zafin marin tafara kuka,

Ya dafe kai yanajin kamar ya rungumota yace "kiyi hakuri cutie ni kaina I'm feeling the pain "

Faseelat cikin kuka tace "yo kishi hauka ne da zaka daga hannu ka mareni don kawai nayi welcoming danuwana "

fahad ranshi bace tuno irin wawar rungumar da omer yamata yace "don kina hauka seki je ki hugging dinshi ba namiji bane shi "

Faseelat ta bishi da kallon takaici ta juya zata shige gida,

Ya bita yasha gabanta yace "okay kiyi hakuri, amma kema kigane kinada laifi, saboda it really hurt me ganinki a kirjin wani "

Ta zagaye shi zata wuce don takaici ya cikata,
Ya riko hannunta yace "haba cutie gobe ne fa tafiya ta ko so kike wani abu ya sameni ne kiyi hakuri laifina ne to "

Tafashe da kuka, ya janyota jikinshi batare da yasan lokacin da yayi hakan ba yasa hannu ya tallabe ta cikin muryar rarrashi yace "stop crying please,inajin kukanki har cikin raina, kimin hakuri kinji my cutie kar natafi da fushinki bazan iya komi ba innaje can, kece farin ciki na, ki yafemini "

Ya omer dake zaure jiyayi kamar ya je ya janyeta yanajin haushi over

Sukau basu san dashiba ma

Jin ta rage volume na kukanta ya dago face dinta da 2 hands nashi yace "kinyafemin ko cutie na? "

Ta daga kai batare da ta kalleshi ba,

yace "thank you so much ,I'm happy "

yana sharemata hawaye yace "smile mana ko hankalina ze dawo jikina "

ta harareshi tadan yi murmushi, cikin jindadi yace "ko kefa, kinga yanzu zantafi hankalina kwance da kau duk kin hargitsa ni, I'm going to miss you "

Cikin dasashshiyar murya tace "me too "

Yace "sure? "

Ta daga kai yace "karki damu zamu rika waya as usual, yanxu I want to go back home, and I want something from you "

Tace "what? "

Ya langabe kai "good bye kiss from you "

Ta danyi dariya ta dora hannu abaki yace "please "yana kara langabewa

tace "nooo I can't, zan de yi maka addua, Allah ya tsareku ya kaiku lpy ya medoku lpy "

Yayi dariya "wayo zakimin ko? Ni yau I'm not happy with ur prayers, tunda bazaki min kiss ba let me have a good bye hug"
yamatso ze rungumeta taja baya tana dariya,,

Shima yayi dariya yace "bazaki bari ba ko zaki shigo hannu ne "

Ya duba wayar shi kusan 9 :30 maybe sunyi 40mnt a tsaye,

Ya meda kallonshi gunta yace "cutie I'm going se munyi waya kenan "

Tace "OK please take good care of yourself for me ,going to miss you hubby "

Yayi murmushi yace "I will insha Allah, kema ki kula min da kanki "

Tace "okay, agaidamin anty "

Ya daga kai ta na mishi waving ta wuce gida,

Shi kuma cikin jindadi ya ja mota yabar kofar gidan,

Acikin zaure faseelat tai kicibus da omer cikin tsoro tafara inda inda,

Ya matsa yabata hanya yace "go inside "ta wuce dasauri yajuya yabi bayanta,

Tana zuwa ta zauna gefen bed gabanta na faduwa tana fatan omer be ji firarsu ba,

ko 2mnt baaiba omer ya shigo dakin fuska hade shima ya zauna gefen bed din batare da ya kalleta ba yace "wannan shine zabinki a matsayin mijinki jagoranki uban yayanki? "

Tai shiru batace komi ba yacigaba da cewa "mutumin da besan darajar kiba da ze iya daukar hannu ya mareki with out reason shine ze zama mijinki? "

tai shiru kanta kasa yace "kiyi tunani fa sister idan ya'iya marinki awaje inkina cikin gidanshi fa se duka kenan "

Ta girgiza kai yace "nasan duk problems nashi da zuwana nakara ganin wani, anya bakinaso kiyi ganganci da rayuwar kiba yakamata ki sauya tunani "

Murya slowly tace "yaya duk wani problems da kaji insha Allah ze gyara, kuma marin da yamin it was a mistake, na tabbata baa cikin hankalinshi yayi hakanba "

Ta nisa tace "inason shi sosai yaya banajin zan iya rabuwa dashi duk runtsi "

Tunda tafara magana omer yaketa kallonta tana kai aya yace "shikenan tunda kince haka amma karki kuka da kowa in aka kara samun matsala kamar yadda kika ki bin shawarata a can baya "

Ta girgiza kai tace "insha Allah ba abinda ze faru kamin adduan hakan "

Ya mike tsaye ze fita ta riko hannunshi tanaso tai kuka tace "yaya kayi hakuri plsss naga kamar ranka ya baci "

Ya janye hannunshi yasaka a aljihu ya sauke ajiyar heart yace "karki damu raina be wani baci ba, nadeji zafin marin da yamiki sosai "

Ta langabe kai "yaya plss don't tell ummi about it "

Yayi murmushi yace "bama haka dake seda safe "yajuya yafita,

Tai shiru tana nazarin maganar omer,kafin ta tashi tafita danyin salla,

Fahad na komawa gida lokacin aisha ta dawo, amma bata dade da dawowa ba tana fitowa wanka ya shigo room din yana binta da desire looking ya kwanta kan bed yanajin dadi feeling very comfy,

Aisha ta kalleshi ta zauna kan seat din mirror ta jawo mai tafara shafawa tace "mommy tace meyasa bakaje mata bankwana ba ?"

Ya na kallonta yace "I'm busy ne akwai wasu aiyuka da naje na kammala "

tai karamin murmushi tana shafa powder tace "a office kenan ? "

yace "noo "

Ta juya tana kallonshi tana murmushi tace "a wurin amarya ko? "

Ya zaro ido ya tashi zaune yana kallonta tai mishi farr da ido tace "yeah kobahaka bane "

Ya tashi yaje yayi hugging dinta ta baya ya na kallon ta ta cikin mirror yace"yaakai kika sani? "

tai yake tunda ya shigo dakin taji kamshin different perfumes wanda ba nashi kadai ba, yanzu da ya sunkuyo takara jin kamshin sosai that means sunhada jiki da faseelat,

Tace "yaya hanci na ya dade da hardace kamshinka ko karamin canji akasamu zangane "

Ya mike tsaye dasauri yafara sosa keya ta juyo tana kallonshi tai dariya tace "karkaji komi she's your wife to be, maybe tai maka hugging din bankwana ne "

Yafara dariya ta mike tsaye da niyyar wuce shi yayi sauri ya dauketa ya dora saman bed yana mata cakulkuli sunata dariya daganan wasan ya sauya,

*6am* jirginsu ya daga zuwa dubai.

Bayan Sun sauka beko tsaya hutawa ba yayi wanka yafita meeting da zasuyi da AIRAS company,

Aisha ko kwantawa tayi don huce gajiya,

Bayan 2 days aka kawo lefen da yayi wasu Aisha iri daya Kowace 3 set that make 12, set daya me 6 se 2 set nada 3,3 color dinsu purple da pink da brown, ya kashi kudi sosai he spend more than 10 millions akan lefen ba kaya masu arha ne acikin akwatunan ba,

Lokacin da Aisha taga lefen she's not happy at all sede tayi pretending tana murna tai hugging dinshi tana godiya,

yayi murmushi yace "don't take them as kayan fadar kishiya, nayi miki sune kawai kyautar ki na nan se munkoma gida, saboda naji dadi ganin kin kwantar da hankalinki "

Aisha tai murmushi given him kiss tace "thank you "

bayan yafita tana kuka ta kira mommy suna vedio call Aisha cikin tashin hankali ta nuna mata lefen,

Mommy ta tabe baki tace "lalle fahad kudi sunmishi yawa ke kuma me kike wa kuka tunda gashi kema ya miki naki "

Aisha na kuka tace "mommy nide nagaji wlh kullum innaduba wayar yaya bakomai ciki se pictures din faseelat ba iyaka da messages nata birjik, mommy badanni ba fa yayi wadannan kayan saboda ita ne, bakiga ba yanata doki invitations ma anan aka buga yanata rabawa bussines friends nashi "

mommy taja tsoki "waya aike ki duba mishi waya ai bin diddikin ki yaja miki gobe ma seki kara dubawa, kina jina ki cigaba da daurewa kinji diyata na lokaci ne ki dena damun kanki kibari ta shigo gidan mugani yadda zaman nasu yake "

Aisha tace" to mommy "

mommy ta cigaba da kwantar mata da hankali suna gama waya ta tashi tsaye tafara zagayar daki ,abin ya daga mata hankali,
Chapter 50 · 0% Book details