← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 130

Sashe 4

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faseelat tace "eh "tafara bin bango ummi takamata ta kaita toilet sannan tai kitchen,

Da dai daya yanuwanta suka rika shigowa suna mata ya jiki kafin su bar gidan, shi ko Mubarak harda hawaye danba karamar shakuwa sukai ba daita.

Bayan tasha tea din da magani ta koma ta kwanta,

Can wajen 12pm ummi nata aikace aikacenta wani yaro yazo yace ana kiran faseelat .

Ummi ta danyi jimmm sannan tace "gatanan zuwa "

Yaro yaje ya kai sako

itako ummi tashiga dakin faseelat har lokacin tana bacci ummi tafara tapping dinta tana kiran sunanta faseelat ta bude ido, tana kallon ummin.

Ummi tace "ki daure kitashi ki dan kimtsa ga khalil can yazo "

Faseelat gabanta ya bada dudum, tasan datace bata iyawa ran ummi ze baci dan dole ta mike tsaye ummi tace "zade kiiya ko? "

Faseelat tace "eh ta jawo hijab har kasa ta saka ai gwara tajema ta kara ganinshi maybe jiya batai masa kallon tsaf ba.

Tana saka hijab din tafita ummi ta girgixa kai tana kallon yadda take tafiya a kasalance.

Faseelat na fita taganshi a.....

Next page loading........
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

6⃣

*Dedicated to SIS ZULAIHAT RANO*

a zaune kan roba-robar shi kallo daya tai mashi ta dauke idanunta, jikin bango ta jingina kanta na kallon sama ta cije baki saboda Marar ta data murda ,

Shi ko yana ganin fitowar ta ya mike tsaye yana gyara riga ganin ta jingina a bango tana ya mutsa fuska yasa shi jin badadi,

Bakomi yasa faseelat dauke kai ba se dan ganin kara jiya da yau, shadda ce jikinshi fara kall ya kawo farar hula akanta ga takalmi fari, wayaga balbela🤣
Shi gashi baki abin se ya dagule, itada tafito ganin canji se taga gara jiya, shaddar se sheki take tsabar fari.

Shi ko be samu ganin fuskar taba saboda kanta na facing up ganin Sun kusa minti ukku yasashi cewa "barka da fitowa"

Batare da ta sauke kanta ba ta dan juya shi ta zuba mai jajayen idanunta wanda suka kumbura saboda rashin barci da kukan da tasha ,

Yace "subhanallah, faseelat lpya kike? "

Ta juya sannan tace "ban lpya "

Cikin jimami yace"miyasameki?"

Tace "fever"tana tabe baki.

Yace "ayyyah "da karfi wadda tasa seda ta mike daga jikin bango saboda yadda gabanta ya fadi, Ya cigaba da cewa "Allah shi sawwake shi baki lpya "

Faseelat kamar ta dora hannu aka tasa ihu haka takeji, ashe ba karamar illa takeso taiwa Kanta ba ko magana be iya ba, shi ga bahaushe wani abinda ta dan lura dashi shine kamar maganarshi daga hanci take fitowa.

yakatse mata tunani da cewa "ga wannan"

Ta kai kallonta ga ledojin da yake miko mata, daya babba daya karama, dan dole ta mika hannu ta amsa can ciki ciki tace "Nagode"yayi kamar be jiba sema yace "dama zuwa nai mugaisa gashi bakya jin dadi yanzu ni zantafi se munyi waya ga waya nan da sim da komi "

Batare da wata murna ba ta kalli ledar hannunta ta yamutsa fuska.

Yace "se anjima agaida ummi "

ta juya kawai ta shige gida tana saka da warwara , yadda zata kuma ganinshi in ya dawo dan kullum kara gano muninshi takeyi.

tana shiga gida ummi tayi shimfida kan barandar gidansu kafafunta a mike tana huce gajiyar hidimar da tasha, ta je ta kwanta kan kafafunta,

Ummi tace "sannu faseelat kode mutafi asibity? "

Ta girgiza Kai ummi ta kai dubanta ga ledojin da suke zube ta jawosu tana fadin "shi ya baki wannan?"

Faseelat ta daga kai idonta na kawo ruwa batare da ummi ta dubeta ba ta Fara bude ledojin, daya cosmetics ne kawai ciki, danginsu perfume, Nivea lotion, roll on, powder irin big pack dinnan wadda Zaka samu su concealer da foundation, da janbaki duk a ciki, se lip gloss.

dayar kuma waya ce ciki me suna infinix hot 6, ummi tace "aaa!masha Allah Allah yasa alheri, faseelat kinga kaya ko? "

faseelat da duk abinda zaa daga wani kululu ke tokare mata makoshi tace "ihhhhm "

Ummi tace "to ga waya faseelat tunda wayarki tasamu matsala har yau alhaji babba be aiko da wata ba toga khalil ya hutar dashi "

faseelat ta mike tsaye zata wuce dakinta dantagaji da jin maganganun ummi, kawai wayar tafara ringing, ummi tace "zo zo gashi har ya kira ashe a bude take "

Faseelat takoma ta amsa kamar zatai kuka tashige daki tana shiga ta danna ta a key dif ringing ya tsaya ummi duk a tunaninta faseelat ta dauki wayar ne, kiran na yankewa shiru be sake kira ba faseelat ta tabe baki,

Ta haye gado tana tunanin rayuwar da zatayi nangaba,

Hannunta ta dora kan kirjinta taji yadda yake fat..fat ta fara hawaye.

khalil yana be koma gida ba se 2pm dan daganan school ya wuce,

Yana shigarda mashin dinsa yayi hanyar dakinsa Hjy saratu da ke alwala zatai salla tabar alwalar tana bin bayanshi da kallo har ya kusa shigewa Hjy tace "kai zonan khalil"

ya juyo yaisa wurinta dan slope din dakinta da take kai anan ya zauna tana kallonshi tace "lpya kake naga ka dawo haka kamar marar lpya? "

ya cire hular kanshi yana fifita yace "Hjy naje gidansu faseelat na sameta bata da lpya sosai "

Hjyar tace "ummm se akai yaya? "

yace "shine nakeji nima bani lpyan "

Hjy saratu tai kasake tana kallonshi shi kuma dagaske yake maganarshi ,Hjy tace "to Allah ya sawwake ,saboda bata lpya shine kake wannan yaushin? kamar ba namiji ba, tashi da Allah kaban wuri "

Memakon ya tashi se yace "Hjy yaushe zakije ganinta? "

ta banka mai harara "se ran da na shirya "

"to me ze hana kije yau? "

Cikin haushi tace "saboda ban ga dama ba "

Ze kara magana tace "aa da Allah kyaleni fita xanyi yanzu idan na dawo zan biya ingano tan "

yace "tom "ya mike zakadai -zakadai ya shige dakinshi, wata kan jiya daga jiya zuwa yau faseelat ta zama wani bangare na cikin jikinshi, ku jifa 😂kunsan irin su dasaurin shiga hannu ,

wayar shi ya fiddo a aljihu ya kara kiranta bata dauka ba faseelat lokacin ma batasan inda kanta yake ba dan gabadaya masassara ta rufeta tana cikin bargo tana kyarma lokacinma ummi na wurinta zaune tana jiran abba yazo su tafi asibity.

Koda kiran ya tsinke ajiye wayar yayi shi a kaidar shi baya missed call biyu, (audu ka'ida kenan)

Hmmm shifa ba ordinary mutum bane shi rayuwar shi daban take da yadda aka saba gani kude biyoni muji tasu salon soyayyar.

Au 😂nayi mistake, kaso a soka ai shine so, kaso a ki ka fa?shi kuma me zaakirashi?
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LBBVKSXqmrj3oaalNYWqmS

➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

7⃣

Dedicated to *SIS ZULAIHAT RANO*

Abba na zuwa ummi ta kama faseelat da temakon kaninta abul saboda ko tafiya bata iyayi ga zazzabi ga ciwon mara ga tension abun da yawa, har cikin mota akasakata, babansu yana da mota amma ta kwana biyu sede batayi tsufa can can ba ,yayan abba wanda sunansa salisu suna kiranshi baba babba ummi kuma na kiranshi alhaji babba mutum ne me kirki da arziki duk da de bawani arziki ne me yawa ba amma ba laifi tunda yana da zuciyar temakon yanuwan sa shi yakai su ummi hajji ya siya wa abba mota shine ya dauki nauyin karatun ya umar, kuma a gidansa yake zaune a Niger Republic din da yake shi alhaji salisun shima dan kasuwa ne yana yawan zuwa can shine yayi aure kuma yabar matar a can kasar.

Shi kuma abba tuni ya dena zuwa Niger din iyakar shi nan gida Nigeria duk da ummi can duk ilahirin dangin ta suke amma alhaji be bari ya zauna a wani gida ba se a gidanshi wannan kenan.

Asibiti suka kaita da zuwan su aka sa mata ledar ruwa, bayan allurai da aka mata,

Se bayan laasar ta farka likita ya shigo yana tambayarta mike damunta yanzu,

Jiki ba kwari tace "ciwon mara da nan "
Ta fada tana nuna setin zuciyarta likitan ya dan kura mata ido ta glass sannan yayi yan rubuce rubuce,

Ya juya wurin ummi da ke tsaye tanajin duk abinda ke faruwa yace "Hjy ire iren ciwon marannan inba aure akayiwa yaranba zeyi wuya ya barsu, sannan batun ciwon heart din rashin cin abinci ne da isashshen bacci wannan kesa ulcer ke kama mutum wuf daya, se akiyaye duk abinda na fada banda abu me tsami ko yaji ko mai da yawa arika bata abinci akai akai "ya juya bayan ya gama jawabin yana kara kallon faseelat,

ummi tace "insha Allah zaa kiyaye, kuma ankusa yin bikin ta ma "

Likitan ya Mike tsaye yana gyara ta kaddun hannunshi, shi da har ya fara tunanin ya samu ta ukku, matanshi biyu, ya killace a gida dukansu farare ne tass dan yanada gurin ajiye fararen mata kuma dukansu a asibity suka hadu daya ma kauye take daga amai da gudawa ya aure ta.
Fita daga dakin yayi yana fadin ,"Allah ya sawwake, "

ko da abba ya dawo hospital din samu yayi an sallame su dan lokacin kusan 6:40 ya biya Bill suka wuce gida.

Bakin wani pharmacy suka tsaya abba ya Shiga ya siyo magungunan da aka rubuta musu sannan suka wuce .

suna isa ummi takama faseelat suka fito har zuwa dakin ta ta kwantar daita malt da milk ta hado mata tasha tasha magunguna ta kwanta baadade ba bacci ya dauketa.
Chapter 4 · 0% Book details