← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 130

Sashe 40

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tunzuro baki ta bude marfin motar ta shiga, shima yabude yashiga yana kallonta yace"yanzu ni na zama abin tsoro kamar ba fahad naki ba "

Ta dago ta kalleshi tai murmushi, shima ya murmusa yana juyawa ya jingina jikin kofa dan yaji dadin karemata kallo yace "kinbani wahala cutie dan kinga inasonki da yawa ko? "

Ta harareshi, wanda hakan ya matukar birgeshi tace "munsha wahala, zakace kasan yadda nai missing dinka kuwa? Nasha kuka many times saboda shareni da kayi "

Abun ma yabashi dariya yadan shafi sajenshi ya kalleta yace "ke zakice haka? Kira nawa nai miki kikai ignoring dina dubi duk yadda nafada saboda tunaninki, kincika taurin kai tunda nabada hakuri ai shikenan amma se lokacinne ma kika kara hawa kawai dan na "se yayi shiru ya saki murmushi yana shafar kanshi da hannu ya dan kalleta yaga tanata watsa mai harara, yayi dariya yace "bada gangan nai hakan ba, nide inarokon ko hakan yafaru anan gaba amin hakuri, wlh kamshin turarenki kanshi rudani yake "

Ta balla mai harara "Allah karka kuma dan bazan daukeshi a kuskure ba tom "

Yayi dariya "kinganki ko, hmmm ki koyi hakuri dani shiyafi miki "

Ta turo baki gaba, yana dariya yana nuna setin breast dinta da hannu yace "harda jibgo hijab amma dukda haka ga yan albarkannnan sunfito gaidani "

Dasauri tadora hannu biyu saman breast dinta takare su, ya kwashe da dariya itako se kallon saman hannun take taga wai dagaske ne,

Ya sassauta dariyar yace "to yazakiyi ne tunda suna sona kome zaki sa se sunfito sede in a akwati zaki rika sakasu "

Ta zumburo baki tana so tayi kuka,

Yace "I'm sorry,im joking, nadena amman kicire hannunki plsss kibari ko daga cikin hijab din nasamu narika meda miyau na,"

Taki cirewa yace "kicire kigani wasa nake yi "

Ta zame hannun tana kallon gaban nata ashe dagaske yake sunfito tai sauri tameda hannuwan akai,

Ya dafe goshi "oh ni bakina yajamin dama nai shiru na cigaba da kwasar romo na "

Su duka suka fashe da dariya,

Yanda take dariya bakaramin burgeshi yakeba, yayi shiru yana kallonta cikinso da kauna,

Jin yayi shiru itama tai shirun ganin ita yake kallo suka kure juna da kallo dukkansu sunajin feeling like to hug thereself,

itace ta dauke ido, sannan shima ya dawo tunaninshi cikin inda inda yace "I love you cutie "
Ta kalleshi ta sakarmai murmushi tace "I love you more"

Jiyayi kamar yakai mata kisss yayi sauri ya dukar dakai kamar me nazari,

Faseelat na kallon sumar kanshi dake kwance takatse shirun da "where's my angel?"

Ya dago yayi murmushi yana jindadin yadda takeson yarshi yace "tana gida, tana missing naki sosai, wani lokaci takanwa mommynta kuka akaita gum anty ita "

faseelat tai murmushi tace "I'm missing her too, inaga zanje ganinta very soon "

yace "baki tsoron aisha tagane muna soyayya? "

Faseelat ta girgiza kai tace "a, a banajin tsoro, bana tunanin akwai abinda zeban tsoro inde akanka ne, anty nasona nasan zata fahimceni, "

Yace "hmmmm"cikin ranshi yana cewa "bakisan true colors na aisha ba"

Ta katseshi da cewa "komiye de ni inasonta saboda ta dalilinta na sanka, and saboda kana sonta saboda inason duk abinda kakeso "

Ya cije lips yace "really? "

Tace "eh, insha Allah nida anty zamu zauna lpya bawanda zeji kanmu "

Yayi murmushi ya girgizakai yace "I wish so "amman yana ganin wuyar abun,

Sunata fira kusan 40 minutes ya zaro akwatin zoben da yasiya mata ya bude, tace "Wow" tana zaro ido da rufe baki ganin haduwar zoben na diamond me shegen kyau,

Yakara matsawa kusa daita yace "here's our engagement ring,plsss let me put it on your hand"

Tai mai wani kallo tana murmushi ta make kafada tace "nagano wayon naka, so kake katabani hankalinka ya kwanta"

ya kalleta yayi guntun murmushi yace "don't take me wrong Allah my intention is not to do that ,kawai I want to put it on you "

Tace "ban yarda ba "

Ya rufe akwatin ya dora akan cinyarta yace "alright have it "ya dauke kai

Ya tamke fuska tatsaya tana kallonshi feeling sad ya juyo yana kallonta yace "I want to go back home"

Tai fuskar tausayi ta dauki zoben ta dora a kan lap dinshi ta dora hannu kan dayar,

Tana mishi good look tace "feeling happy now? "

Yayi murmushi ya bude akwatin ya zaro zoben ya dago hannunta yanajin wani diffirent soft ya saka mata zoben,

Ta lumshe ido har yasaka mata tanajin nice bazato taji yayi kissing din hannun ta bude ido dasauri jin yarrrrr jikinta,

Idanunsu suka hadu yana mata love looking yace "will you marry me? "

Tanata kallonshi batare data saniba bakinta ya furta "I'm ready to marry you "

Fahad ya Saki dariya yana kallonta tai sauri ta dawo tunaninta ta rike baki not knowing me tace yake dariya,

Ya dago "inasonki me kyau da duk wani abunda kikai "

Tai dariya ta rufe fuska yace "yanzu zankoma, very soon zan aiko parents nawa yanzu mufita inbaki tsarabarki "

Tace "thank you "tana kallon hannunta

Yace "u r beautiful kome kikasa dole yamiki kyau "

Tai murmushi ya bude yafita itama tafito ya bude gidan baya ya dauko ledar ya mika mata,

Ta amsa tace "Nagode "tana murmushi

Yana mata kallon shaawa yace "I'm going "

Tace "bye take good care of yourself for me "

Ya daga kai kurum, taki tafiya yace "just go sekinshiga gida zantafi "tai murmushi ta juya tana tafiya,

Yabi kugunta da kallo da suke sababurna baburna 😂🤭 ya lashe lips yanata kara kallonsu, harta kusa shiga gida ta juyo ya sakarmata murmushi ta daga mai hannu tana murmushi ta shiga gidan, ya girgiza kai yana kara cusa lip abaki ya shiga mota yabar unguwar,

Faseelat nashiga gida taga ummi tsaye bakin kofa da hijab a hannu tace "ummi lpya inazaki? "

Ummi ta harareta tace "wace irin fira ce kuke haka har 1 hr Allah da bakishigo ba sede kiganni awajen"

Faseelat tace "yi hakuri ummi bawani abu fa dan Allah kiyarda dani ummi "

Ummi tace "bahaka bane ba rashin yarda bace ai se anayi ana duban bakin gatari ko faseelat "

Faseelat tace "hakane umminmu zan kiyaye, kinsan ummi muje kiga zoben da yabani da kayanda ya siyomun a Italy da yaje "

Ummi tace "hmmmm marar kunya muje nagani "suka wuce ciki,

Suka zauna suka fara fiddo kayan, wasu dogayen riguna biyu da turare da agogo, se dayar ledar sweet ne kala kala tun wadanda ya taba semata,

Ummi tace "kaya sunyi kyau, zobenma yayi yanzu idan abbanku ya dawo se anuna masa "

Faseelat ta kwantar da kai kan cinyar ummi tanajin dadi tana ta kallon zoben hannunta,

Ummi ta kalleta itama she's happy ganin faseelat din na son abun awannan karan,

Anahaka abba ya shigo ummi ta nuna mai kaya yagani,

Yace "naga kaya Amman waye wannan ya sunanshi aina yake, saboda inyi bincike kanshi donke ba budurwa bace da zaaita jan jiki gwara in dagaske yake yafito ayi aure shine "

faseelat kanta duke tace "sunanshi fahad dawood kuma a GRA gidanshi yake "

Abba yace "yanada mata kenan? "

Tace "eh "kanta kasa,

Ummi tabata fuska, "wai wannan yaron da bewuce 30 ba shine yake da mata har yana neman ta biyu? Gaskiya nikam abun ya siremin "

Abba yace "wannan ba matsala bace inde beda matsala, kuma ke faseelat ai kina iya zama da kishiya ko? "

Faseelat tai sauri tadaga kai ummi ta watsa mata harara tace "tashi kiba mutane wuri sakarai ni nan kinganni da kishiya ne? Kike wani murna zaki auri me mata "mtsssw

Faseelat ta tashi ta shiga daki

Abba ya duko kasakasa yace "angayamaki ita irinki ce me shegen kishi "yayi cikin zolaya.

abu a duhu abba wayasani ko itanma hakan take 🤣

ai comments ko infasa auren fahad ehe 😎
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

4⃣6⃣

*another page for you rukayya haroun(maman nour)* *and erminatou*

Ummi tace "gaskiya alhaji bazan kai diyata gidan kishiya ba "

Abba yace "haba asiya be kamata kina magana irin haka ba, ita ai ba budurwa bace jawara ce kinga mawuyacine tasamu saurayi, dan Allah kibarta tunda tanasonshi karki sage mata gwiwai "

Ummi tace "ni ban iya kishi ba bare ita hakanan kaje aimaka wani mugun abun kana zamanka lpya "

Abba yace "shikenan tunda zancen kikeso bari nabaki wuri inkingama mitar kikawomin fura ta "

Ya tashi yabata wuri, ummi tace "shikenan se inki magana, yanzun intayi auren ko nima hankali na ba kwanciya zeba bare ita, tunda taji tagani shikenan Amman dole na dage mata da gyara na musamman in inaso tai daraja "

Ta tashi ta nufi dakin abba,

Faseelat nashiga daki ta haye gado ta kunna data cikin farin ciki,

Messages nagama shigowa tabude na maman amira wanda yanzu ta meda number ta da my anty , ta bude message nata "wai antyn amira kinmanta danine?ko duk zawarcinne ya boyeki?har munyi tafiya mundawo, in bazaki zoba kibani address naki zanzo ni saboda yarki ta matsamin "

Faseelat tai dariya ta tura mata "zanzo insha Allah zuwa jibi de nima ina missing naku "

Tafita tashiga contact na fahad ta turamishi "masoyi naji dadin kyautar ka, Allah yakara maka budi ya kareka daga sharrin makiya, kanata kara kyau miye sirrin ne?"

Ta turamishi tana murmushi ta kashe datar se barci,

Da laasar fahad ya kirata suka kara shan vedio call sannan sukai sallama,

Se dare ta samu tabude data bayan sunyi bankwana da habibinta, ta shiga message din maman amira "💃🏼💃🏼💃🏼thank se kinzo inanan ina zuba eyes"

Faseelat ta tura mata "don't mind"

Tafita alokacin fahad ya turomata reply kamar haka "amin cutie karki damu da kyauta da namiki bakomai bane danko raina kikeso zanbaki, kinason kisan sirrin?"

Faseelat tace "thanks eh inaso inji "
Chapter 40 · 0% Book details