← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 130

Sashe 70

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faseelat tace "koda yaushe nima inasonku sosai kuma ina gayyatar ku gobe dafatan zaku zo "

Mansura tana farin ciki tace "zamu zo anty insha Allah "

Faseelat tace "to se kunzo ina gaida sauran sisters nawa"

Su Mansura suka fara surutu suna fadawa umma abinda tace faseelat tai dariya takashe kiran dan murna basuma san basu kashe kiran ba,

Duk yinin fahad be leka dakin faseelat ba da Maghreb tai masu dinner takoma daki tai wanka, bata ko shafa mai ba bare powder tade shafa humrah ta saka riga da sket material lace orange color ,

Tana zuge zip fahad Ya shigo bata ko kalle shi ba,

Yana shan kamshi yace mata "ki saka hijab mutafi na ajiye karfe tara zanzo daukarki "

Batare da tai mishi magana ba ta ida zuge zip din ta juya tabude wardrobe ta dauko hijab dinta, fahad yabi bayanta da kallo sket din Ya mata cif dammm ta saka hijab cikin jin haushi fahad yace "idan kinje karki cire hijab dinnan kuma karki amfani da hannun hijabin "

Hawaye suka cika mata ido ta kalleshi kamar zatai kuka tace "wace irin rayuwa ce wannan? Shikenan bazan kara sakin jiki a gidanmu ba dannayi aure? A cikin gidan na taso tun yarinta har girma na, yaya de kake magana kanshi har kashi ya wanke mun, kuma duk cikin gidan muharramai na ne ko kamutu ba aure tsakaninmu miye na damuwa kode kanason matsa ma rayuwata ne? "

Taja numfashi tace "to shikenan bazanje ba bazan kara zuwa koina ba tunda bakaso ko yaushe zan kasance mai maka biyayya "

Tafara zare hijab din jikinta,

Fahad ya rike mata hannu murya sanyaye yace "kiyi hakuri da hali na faseelat wlh bansan koda kuda namiji ya tabaki, duk sonki ne yajawo haka kimin uzuri,"

Ya jawota jikinshi Ya gyara mata hijab yace "mutafi muyiwa su ummi bankwana kinji my honey"

Tai kwance jikinshi suka fito, amira tace tana zuwa suka tafi tare,

Atare suka shiga shima Ya gaidasu ummi yabawa ummi 200k Ya tashi Ya fita,

faseelat murna kawai take ta yaye hijab ta matsa wurin ummi, ummi ta kalleta taga duk ta rame sede tai haske dan gangariyar madarar da fahad ke zuba mata lol.

Ummi tace "ya gidannaku Ya kishiyarki? "

Faseelat tace "muna lpy ummi "

Ummi tace "senaga kamar kin rame "

Faseelat tace "hakanan ne kurum "

Ummi tace "Ya naga kamar baki baki a wuyanki da gefen hannunki? "

Faseelat tafara inda inda tace "konewa nayi ummi wlh Allah Ya temakeni daddyn amira Ya siyomin wani cream nake shafawa shine Ya koma haka "

Ummi tace "to Allah yakyauta gaba ga wani tsimi nan na siyo miki kishashi yanzu ga wasu nanma a leda kitafi dasu kin kusa shanye wadancan ko? "

Faseelat tace "eh saura kadan ai ummi bani sanya"

ummi ta rike gemu tace "Allahu Akbar Allah abin godiya "
Faseelat ta rufe fuska, ummi ta mika mata tace "gasunan ki kara himma to "

Faseelat ta dauka ta shanye tsumin tass suka cigaba da fira bayan isha Ya omer Ya dawo murna kamar zata kasheta shima haka sukaita labari su ishak su abul su Mubarak kamar zasu cinyeta,
Abba Ya dawo taje suka gaisa yanata sa mata albarka,

Karfe tara fahad ya kira ta ta tashi tasa hijab ta sabi amira dake bacci ummi ta taho yi mata rakiya zuwa bakin kofa,

Faseelat suna isa kofar ta ta juyo ta kalli ummi tace "ummi zanyi missing naku Allah yasa ayi karbabba dan Allah ummi kimin addua Allah Ya amshi adduoina "

Ummi tace "insha Allah diyata Allah Ya kara baku zaman lpy"

Tace "amin Nagode ummi Allah yakiyaye"

Mubarak yazo Ya amshi amira suka fita, abayan mota Ya kwantar daita ya masu se da safe ya koma gida,

Tunkan hanya faseelat tafara rikita fahad saboda tsumin da yafara aikinshi,

Tana ta shash shafa shi tana Yi mai kiss yana driving, se lumshe ido yake dakyar suka isa gida shi Ya dauki amira ya kaita dakinta Ya koma suka cigaba da rikita juna,

Da daddare faseelat kasa bacci tayi hakanan taji farin ciki Ya dabaibayeta na zuwan sisters nashi , har fahad yayi bacci Ya barta tana ta kallonshi tai masa kiss's ta tashi tayo wanka ta kabbara salla tana ta adduar Allah Ya gyara mata mijinta ya sulhunta tsakaninshi da yan uwanshi ,

Tun asuba bata zauna karatu ba tai sauri ta gyara gidan sannan tai masu simple breakfast,

Ko sleeping dress bata cire ba ta zauna sukai breakfast fahad se kallonta yake yadda take ta murmushi ita kadai, Ya lumshe ido ya bude Ya saki ajiyar zuciya cikin ranshi yace "honey kaunar ki zata kasheni "

Shaf shaf ta samu ta karya ta wuce kitchen tafara aiki zatai wa umma meat pie da spring roll su Mansura su kai mata,

Fahad na daki kasancewar weekend ne shiru bata shigoba har 12 na rana shi kuma yanason yayi ninkaya Ya tashi ya nufi kitchen,

Kitchen din nata kamshi yayi tsaye yana kallonta tanata aiki dasauri, ta juyo ta kalleshi jin kamshin turaren shi,

Ya harde hannuwa yace "wai yau shirin mi kike? "

tana aikin tace "wlh hero baki zanyi kuma they're special and dear to me "

Fahad yayi murmushi yace "lalle kinaji da bakinnan tow Allah yakawosu lpy but ni antakura ni "

Faseelat tace "haba ga anty nan just go to her tunda ni ina busy "

Yana mata kallon mamaki yace"keda kanki kike tura ni, yau ko dan kishi na bakiyi"

Faseelat tai dariya tace "bahaka bane hero dan kasamu natsuwa nace kaje wurinta amma ai ina kishin ka sosai "

Yace "ai kece natsuwa ta, any way natafi kar na hanaki aiki "

Tai murmushi ya juya Ya tafi wurin Aisha ,

Agidan umma su Mansura da safiyya da ummu salma shiri suke tayi sunata doki,

Umma tace "kai yau faseelat se kanta yayi ciwo nasan "

Mansura tace "umma dan Allah kizo mutafi tare, daganan kiga yaya kuma nasan anty zataji dadi da zuwanki"

umma tace "ni tsoron ma ganinshi nake sede inason naga daughter eye to eye wlh inasonta yarinyar kirki ga daa gaskiya Allah yana son fahad da yabashi ita,bari nafadawa daddinku se na shirya mutafi "

Ta shiga tafada mishi yace ba matsala don shima sosai yakeson su shirya da danta,

Karfe 1 tagama komi har abinci ta masu ta wuce daki a gaggauce tai wanka tasaka gownt light purple atamfa tai simple makeup,

Karfe 1:15 su umma suka fito umma na driving su kuma sunata labari suna jindadi, Mansura takira faseelat, faseelat na cikin shiryawa ta dauka,

Mansura tace "anty gamu a hanya kinsan me? Harda umma saboda takagara taganki azahiri "

Faseelat tace "amazing I'm very happy se kunzo kuyi sauri dan Allah "

Mansura tace "OK anty "

Ta juyo ta kallesu tana dariya tace "kunji fa anty tace ai sauri "

Karfe 1:30 suka isa kofar gidan sukai horn megadi Ya bude suka shiga ciki,

Suka firfito sunata kallon gidan sukaje bakin kofa suka danna door bell,

Da gudu faseelat taje ta bude,

Ta gansu tsaye dukkansu sunyi kama da fahad more especially Mansura, tarika murmushi,

Duk sunkare umma,

faseelat tace "ina umma? "

Suka fashe da dariya suka bata wuri, faseelat ta fada jikin umma kamar sun dade tare tanajin matukar dadi itama umma dadi takeji ,

Su Mansura abun Ya birgesu yadda faseelat taiwa ummansu,

faseelat tai breaking hug din tace "umma kushigo sannunku da zuwa "

suka shiga suka zazzauna faseelat ta zauna gefen umma tace "ina wuni umma Ya hanya "

umma tace "lpy lau Ya ta Nagode da karramamu da kikai"

Faseelat tace "umma kidena min godiya ai kamar uwa kike aguna "

Umma tai murmushi su Mansura se kallonta suke kamar su hadiye ta tashi ta kawo masu abunsha ta zuzzuba musu ta dawo ta zauna,

Suka dauka suka sha,

Sunata kallon gidan duk pics din su fahad da Aisha pic daya ne na faseelat,

Kamar sundade tare suka matsa suka fara hotuna harda umma fuskarsu dauke da farin ciki,

Suna haka fahad Ya fito zai fita har yayi wanka Ya na sanye da blue shirt white jeans, tundaga step yagane ko su waye bakin faseelat, Ya daure fuska Ya cigaba da saukowa yana kallonsu da mamaki a fuskarshi,

Jin ana saukowa suka meda hankali gun step din, ganinshi duk suka sha ruwan jikinsu,

Fahad yaida saukowa yana harararsu yaja tsoki yawuce ze fita,

Umma ta mike tsaye tace "son Dan Allah kayi hakuri ka yafemin nida yanuwanka duk muna da bukatar ka "

Fahad yaja wani dogon tsoki, faseelat ta zaro ido jin yawa umma tsoki tai zumburr ta mike tsaye ta buda murya sosai tarika cewa "innalillahi wainna ilaihi rajiun,innalillahi wainna ilaihi rajiun"!!!

Fahad yayi sauri ya juyo saboda seda hanjinshi ya juya saboda yadda take maganar zuciyarshi ta rika bugawa da karfi he is expecting something bad happened to her, Ya ganta tsaye se juya kai take tana hawaye tace "ina tausayin ka mijina saboda sanin idan ka mutu yanzu akwai azabar dake jiranka, hero ka dawo hayyacinka ,ka rika tuna lahira ba duniya kadai ba,umma ce wannan mahaifiyarka data dauki cikinka tasha wuyar nakudar ka ita kake wulakantawa baka tsoron azabar Allah ne? Manzon Allah S. A. W yace

عن ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﷺ ﻗﺎﻝ: ‏« ﺭﻏﻢ ﺃﻧﻒ، ﺛﻢ ﺭﻏﻢ ﺃﻧﻒ، ﺛﻢ ﺭﻏﻢ ﺃﻧﻒ ﻣﻦ ﺃﺩﺭﻙ ﺃﺑﻮﻳﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻜﺒﺮ ﺃﺣﺪُﻫﻤﺎ ﺃﻭ ﻛﻼﻫﻤﺎ ﻓﻠﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ‏» . ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.

_An Kar6o daga Abi-Hurairah, Daga Annabi Yace: *“An Turmusa Hancinsa a Wuta. An Turmusa Hancinsa a Wuta. An Turmusa Hancinsa a Wuta. Wanda Duk Ya Riske Iyayensa da Girmansa, Dayansu Ko Duka Biyun; Sannan Be Shiga Aljannah ba”*.

Tana haki ta cigaba da cewa "se yaushe hankalinka ze dawo jikinka ne? umma na raye bata mutu ba shin bazaka nemi aljannarka ba se lokaci Ya kure maka sannan, kabude idonka sosai ka duba da kyau hawaye ne a fuskar umma kai baka da tausayi ne ga kannen ka nan duk suna kuka saboda yadda kake wulakanta masu uwa, amma duk da haka suna sonka kana gudunsu"

fahad yabisu da kallo duk sunata hawaye musamman umma da suketa zuba akan gyalenta,
Chapter 70 · 0% Book details