← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 130

Sashe 107

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

faseelat tai dariya ya fiddo waya yayi dialing no dinta tana dauka yace "hello umma I have good news for you ur daughter is 2wks pregnant "

umma taji dadi sosai tace "wow Masha Allah ,I thank to Allah the giver for giving us another blessing I'm very happy "

yayi dariya yace "umma kuma zai fara baki wahala tun yanzu don tace tuwonki takeso irin wanda kika taba kawomata tuwon shinkafa miyar gyada"

umma tace "wane irin wahala kuma nida aka zaba yabani 40 minutes yananan isowa "

yayi dariya yace "thanks umma we love you so much "

tace "don't mind "takashe kiran tana murna tashiga kitchen,

faseelat taja mishi kunci tace "baka kyauta ba zakaba umma wahala"

yayi dariya yace "bakiji me tace ba, wannan babyn dangata ne ko zaki yace yanaci ubanshi seya kaso zaki yakawo mishi "

faseelat tafashe da dariya harda rike ciki shi kuma yana tayata,

Aisha data sauko zata kitchen tahada indomei taci taji su kishi ya kara tokareta yanzu shikenan ita tazama yar kallo, ta juya takoma daki tai kwance rufda ciki tana hawaye,

a kitchen fahad ya tube ya rage short ya mika wa faseelat kayan ta nufi sama dasu yadora tukunya yanata murna ya fara kokarin dafa simple jellop supergetti,

faseelat nadawowa taji kamshin girkin zuciyarta tafara tashi ta cire dankwalin kanta ta daure hanci ta shiga kitchen din yanata hanata amma seda takama mishi suka gama tahau sama tashiga dakin Aisha,

aishar na kallo daga kwance, tace mata "anty kifito dining angama dinner"

Aisha batako kalleta ba ta juya tafita,

afili Aisha tace "nifa wlh ban yarda da mutuwar amira ba who knows koke kika kasheta don naki dan yazama babba agidan "

tagama surutun ta tafita dining din don tanajin yunwa saboda surkudarta da fahad yayi dukda de bawani cin kirki zatai ba "

tana zuwa taja kujera ta zauna,faseelat ta tashi ta zubamusu suka fara ci, dukkansu bame kallon kowa kuma tun fitowarta fahad ya hade fuska,

Faseelat ta tashi ta haye sama don kiran ummin ta tafada mata labari me dadi,

tana tafiya fahad ya kalli Aisha dake cin abinci haushi ya kamashi ya janye plate din gabanta ya medashi gaban shi,

Aisha ta rike spoon tana kallonshi, ta mika hannu zata jawo ya kara matsar dashi fuska ahade yace"kije ki dafa kici naki wannan nina dafa dakaina kuma be zama dole nai miki girki ba "

Aisha tafashe da dariya ya daga ido yana kallonta,tarage dariyar tace "haba yaya nifa kanwarka ce ina laifi ma kasamu ina cin wanann jagolgolan naka "

yace "so what karki ci mana "

tace "Tom kayi hakuri da maganganun dazu Allah yahuci zuciyar jarumi acikin matanshi"

Ya tabe baki, setaji ana knocking ta tashi taje tabude sega yar aikin umma da warmers kusan guda ukku ta amsa tashiga dasu ta zauna falo, ta bude daya tuwo daya miya daya farfesun kafar sa, ta tabe baki tace "shikenan fa zatai ta tsirface tsirfacen tsiya ita me ciki "ta bude kular farfesu tasa hannu tana yago nama tana ci,

jin shiru bata iso dining ba fahad ya taso yaganta rungume da kula tanata cin namanta,

ranshi ya baci yace "wai mike damunki ne Aisha, kinsan fa banaki bane donme zakici mata abu,ko tausayin ta bakiji aike yakamata ma ki tausaya mata kafin kowa"

Aisha ta tsame hannu tace "ni banga abun tausayi a rayuwarta ba ni din dece abar tausayi ta yaudare ni ta shigo gidana ta mallake min miji ta amshe min diya daga karshe ta kashe min ita, itakuma tayi wani cikin se in wani ji tausayinta, wlh natsane ta bazan dena tsanar taba har lokacin da zan mutu "ta ajiye kular ta gittashi ta wuce, yabita da kallo kamar ya shakota yayi ta jibga,

ya dauki abincin ya kaiwa faseelat lokacin har tagama waya da ummi tafito wanka yashigo,

Yabita da mayen kallo ya ajiye kulolin yafita ,tasaka rigar bacci ya dawo ya rungumeta ya zuba abincin yana bata abaki, so ukku kadai taci tatashi dagudu tashiga toilet Taita sheka amai yabita yana ta mata sannu kamar yayi kuka,

ya wanke mata baki ya daukota ya kwantar daita a bed, yana gefenta yanata kallonta ba jimawa bacci ya dauketa,

Yayi shiru yanata tunani inde irin wancan laulayinne to yabani don jiyake kamar yayi kuka inyaga tana wahala ba kamar wancan ba da bedamu sosai ba,

ya tashi ya meda abincin kitchen a freezer ya dawo yayi wanka ya kwanta, ya rungumeta tsam jikinshi,

da safe shi yayi musu breakfast don faseelat ma da zazzabi ta tashi, tana kwance abed yazo yayi feeding dinta, yanata rarrashinta da nuna tausayinta,
Karfe 9 umma ta aiko mata da danmalele (shashshaka)taji mai da yaji da veggies faseelat miyonta ya guda zuciyarta ta ji shaawar cin abincin sede tana ci se amai harta hanci duk tabi ta galabaitu, fahad kuka ne kawai beba yakasa fita koina,

da rana ko leko falo beba yana ciki yana jinya, Aisha ta fito ta soya indomei da kwai takoma daki taci, dukda bawani cin kirki ba,

Da Maghreb tafito ta dora girki don girkinta ne,

sede faseelat bashi ta ciba don cewa tai bazata iyaci ba tace ice cream takeso ya fita yasiyo mata da yawa yaajiye a fridge,

Shi kanshi bewani ci abincin kirki ba yatashi yakoma gunta ,Aisha tagama takoma daki tai shirin bacci, shiru be shigo ba se 12:am yashigo,

fuska ba walwala yaje ya kwanta,yabata baya, tanata kallon bayanshi tace "yaya baka min adalci kiri kiri kafifita faseelat akaina kana shiga hakkina sosai seyanzu zaka shigomin? "

abun yabashi takaici beko juyoba yace "kede anyi marar imani Aisha kin sauya yaushe zuciyarki takoma haka, faseelat bata lpy ko rantsuwa nayi haryanzu baki mata sannu ba, baki jin ko tausayin wahalar da take yanzu haka nabaro ta tana ta makyarkyata wlh daita ce bazata bari na kwana can ba zata barmiki kwanan amma ke dayake bakida hali har korafi kike Aisha! Aisha!! Anya wannan halin naki ze barki zama lpy, cikin data samu samm baki farin ciki dashi sema bakin ciki da kike lokacin da nasameki ai kuka kike,wanda nasan faseelat bazata miki bakin ciki ba don kinsamu ciki ita batadashi ,adalcin da kike cewa ayi bazaai ba, zuciyata ta fison faseelat ba jikinta kadai nakeso ba harda zuciyarta da halayyarta me kyau wadda ke kika rusa taki, inason faseelat ina tsananin sonta insha Allah zata samu lpy kuma zata haihu lpy lau sede masu bakin ciki su mutu "

tun kafin yadasa aya tafashe da kuka me taba zuciya har sarkewa takeyi tana kuka tace "I pray so Allah yadauki raina na mutu tunkafin bakin cikinka yakasheni u hate me yaya tunda kasamu faseelat baka ganin kyaun komi nawa while abaya kasha yabon halina da komai nawa nagode da wadannan kalaman "

haryanzu be juyo ba yace "kin sauya hali ne Aisha kisamu ki medo kyawawan halinki nada kuma koda zaki medosu wlh faseelat tafiki aguna , saboda tana son duk abunda nakeso, tana sonki Aisha ke kina wulakantata taso amira fiyeda tunani donme bazan fi sonta ba nace I love her I love her badly itace rayuwata "

Aisha tatashi numfashinta nason daukewa tafita tana kuka ta sauka falo tai hanyar kitchen,

Jin yadda numfashinta yasauya yasa yaji tsoro tana fita yabita,

ta na shiga kitchen ta dauko wuka ta dagata sama tazo zata sokawa cikinta yayi sauri yarike hannunta,

Jikinshi har rawa yake saboda tsoratar da yayi saura kirisss ya kwasheta da mari, idonshi jawur yake kallonta,

Itako tanata kuka idonta kulle ta gaji da rayuwa gwara ta mutu kowa yahuta,

Ya amshe wukar ya tillar murya sarke yace "Aisha kashe kanki zaki? So kike ki mutu kafira ki dawwama awuta? Aisha meyasa baki amfani da ilimi da hankalinki, nayi zaton maganganun da nake miki zaki koyi wasu abubuwan da nafiso kirika yinsu segashi kinason kashe kanki ki karamin bakin ciki akan rashin amira, waya fadamiki banasonki? I love you so much Aisha"
Se hawaye zarrr a fuskarshi zuciyarshi na zafi yacigaba da cewa "ina sonki sosai Aisha ina kuma girmama sonda kikemin domin ke masoyiyace, kina sona tsakani da Allah na shaku dake ya kike tunanin zan iya jure mutuwarki? donme zaki zabi mutuwa akan rayuwa? Yesss I know myself ina shiga hakkinki ina nuna fifikon son faseelat, meyasa bazakimin uzuri ba meyasa bazaki rokamin Allah in rika adalci tsakaninku ba se kizabi wannan hanyar ?ya kkso nai da rayuwa ta ne ina bakin kokarina wurin dedeta ku amma nakasa kullum nakan roki Allah amma shiru Aisha in kika kashe kanki mezan cewa mommy ta rikeni kamar danta ta goyani tamin duk gata "
(kai wlh makoshina har wani tururin bakin ciki yake)

Aisha daketa kuka zuciyarta na harbawa dasauri numfashinta nayin kasa tazo zata zube yayi sauri ya tallabeta jikinshi,

Yana duba fuskarta ta suma kuka ya kwace mishi ya rungumeta yana kuka wai ya zeyi ne ya zeyi da rayuwarshi,

yasamu ya dauketa ya haye sama daita, ya kwantar daita ya dauko ruwa a fridge masu shegen sanyi yazo ya kwaramata,

taja dogon numfashi ta cigaba da nishi zuciyarta na matsanancin ciwo tanata sheshsheka, a tsorace yakira doctor,

ya zauna ya rungumeta yana kuka yana mata magana "Aisha inasonki sosai dan Allah kiyafemin bazan sakeba"
(shege yo bakai kace ta mutu ba🤨)

Likita na zuwa ta dubata tai mata allurar bacci, sannan tadago fuskarta daure da takaici tace "Sir meyasa ake bata mata rai bayan namaku gargadi Adena bata mata rai ,in aka cigaba da haka very soon zuciyarta zata buga, ku bincika abinda takeso arika yi mata shi batada lpy sosai zuciyarta ta kumbura sannan bp dinta is high kukula sosai, ga wannan drugs zuwa gobe asamo mata su they will help I mean help not to cure "

ta tafi ranta bace yananan dafe dakai har 4:30 na dare sannan yatashi yashiga dakin faseelat tana ta bacci amma jikinta rau yake, yajuya ya fita ya koma gun Aisha,

Da safe Aisha ta farka kusan karfe tara lokacin har yagama bawa faseelat breakfast yayi wanka yana zaune gefenta don yaga bata farka da wuri ba hannunta cikin nashi ya rike, ahankali ta bude ido ta kalleshi,
Chapter 107 · 0% Book details