← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 130

Sashe 30

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata iya bashi amsa ba se yatsunta biyu da ta motsa alamun bye, yakashe kiran,
faseelat tai zaune gun tana tunanin ta yadda zasuyi su hadu daga karshe taja tsoki, tace "kawai anan ze sameni se me? "🤷🏻‍♀

Haka akai 2 days dinnan faseelat batawa khalil girki in ma ya dafa seta dauke ta cinye koba dadi dan kawai yaji haushi,
Kuma kullum se sunyi video call da fahad ba so daya ba biyu ba dan dukkansu jindadin ganin juna sukeyi duk Sun dimauce dukansu,

Kafin ranar da zasu dawo faseelat tasha dilka ta kara kilewa ya fadamata 11am zasu sauka zezo wurinta da marece se dadi takeji kamar ta rafka ihu,

11 am su maman amira suka sauka Nigeria, suna makale da juna as usual suka isa gida sukai wanka suka fita zuwa dauko amira dan daddinta kullum cikin fadawa aisha yadda yayi missing dinta yake, dukda suna waya yana ganinta

Sun dauki lokaci agidan momy sannan ya daukosu suka koma gida, lokacin marece ne wajen karfe biyar saura.

Ya fito daga gida suna waya da faseelat har bakin kofar gidanta, yana zuwa few minutes later tafito daga cikin gidan, tana hango mota Sabuwa dal tagane shine ba bata lokaci ta isa gun motar ta bude ta shiga,

Hmmm kamshin turarenta kawai ya rikita fahad se mayen kallo yake binta dashi itama seta kalleshi tasaki murmushi,

yanajin kamar yajawota ya rungume yace "me kyau kinason kasheni ne ko "

tai dariya ta girgiza kai yace "se kara kyau kike miye sirrin ?"

Tai dariya tace"ai kaine sirrina "

Yayi dariya tace "ya hanya inafatan kundawo lpya? "

Yace "lpya lau "yana lumshe ido

Tace "ina my anti da daughter na? "

Yace "suna lpya suma "

Tace "alhamdulillah"

Duk sukai shiru sunata kallon kallo can zuwa ya fiddo wani dankaramin akwati da kwalin iPhone8s ya mika mata, ta karba tana duba kwalin wayar ta zaro ido tana kallon wayar duka befi 3wks taga tallon ta a insta ba 500,000 ta kai hannuwa ta rufe baki, sannan tabude akwatin sega haddadun zinare da yankunne da sarka da yan hannu takara rufe baki tana mamaki shiko kallonta kawai yake kamar yau yafara ganinta tace "all this for me? "

Ya daga mata kai tace "thank you very much, Nagode Allah yakara tsaremin kai ya kara buda duk kofofin arziki "

Ya lumshe ido ya bude yace "amin my baby "

cikin kasala dan gabadaya ta rudashi yace "me zaki bani? "

Tai karamin murmushi tana sadda kai Kasa tana fatan kar yace tai kissing dinshi don bazata iyayi ba a zahiri,

Yace "koba za aban komi ba? "

Ta dago tana kallon shi tace "me kakeso?"tana rufe fuska, yayi dariya

yace "nothing but you "

Tana jin kunya tace "I'm all yours "

Yace "alright I need your hot kiss that always make me go crazy "

Ta zaro ido ta tunzuro baki "plss not now, I'm feeling shyness ,"

Yace "bazan samu ba kenan? "yana langwabe mata

Tace "I will do that on the phone "

Yayi dariya yana kallonta wai kunya takeji yace "alright bani wayarki naimiki exchange na sim "don yasamu yadan taba ta,

Ta dauko ta miko mishi yahada da hannunta sannan yajanye kamar irin mistake dinnan,yana amsa ya rumtse ido again yadora kan seat jin soft and smooth na hannunta inaga b..... Fa

Tana kallonshi thinking that duk gajiya ce ya sauya mata sim card din yabata sabuwar a hannu yasaka tsohuwar a kwali ya mika mata nan ma yasamu yadan taban batare da damuwa ba tace "thank you "

ya kalleta kawai tace "I'm going inside se yaushe? "

Yace "anytime, "

Tace "OK bye ka kulamin da kanka "

tana mishi wani kallo me kara dulmiya mutum ta fita daga motar,ta shige gida yayi murmushi ya girgiza kai yace "I love you my lady "

Yaja motor yabar unguwar,

khalil isowarshi kenan unguwar yaga faseelat tafito a motar ta shige gida dauke da leda ahannu cikin daukewar wuta yabita da kallo har tashige yakuma Bin motar da tafito daga ciki da kallo har tabar layin ,yayi wuf ya sauka daga babur dinshi ko parking beyi ba yasaki mashin din ya fadi kasa, cikin sauri da bacin rai na fitar hankali ya nufi cikin gidan yana kwalawa faseelat kira.

Toh fa kaka,kara,kaka

ina kaunarku yan golden pen nagaida kowa
[7/12, 11:00 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

3⃣6⃣

*Dedicate to golden pen members expecialy*

*mijina dangatana*
*princess mazadu*
*my bazawari*
*sarauniyar golden*😏
*khadejat young novelist*
*maman ashefat*
*deeja luv*

*And all Allah yakara maku basira, wannan page din na tsakani da Allah ne 😂kar ace nafito campaign na 👑kungane de*💋

Tanajin khalil nakwala mata kira gabanta yafara faduwa ,segashi yashigo dakin komi na jikishi na kyarma yana nunata da hannu yace "ubanwa ye ya ajiye ki yanzu? "

Duk tsoro yakamata ganin yanda ya rikice sosai ta tattaro duk jarumtar tahadiye miyon tsoro tana mishi wani kallo tace "masoyi na mana wanda nike mutuwar so "taida da murguda baki.

Cikin zafin rai yace "keeeee "yakaiwa bango naushi nan hannunshi yafara zubda jini,

Batare da ya damu da ciwon ba yace "kina da hankali kuwa faseelat ko kinfara shaye shaye ne bansaniba? "

takara hadiye tsoro tace "hankali na garas sede giyar soyayya dake dibata"

Yana ciccije baki yakara kaiwa bango naushi cikin bacin rai yace "ke danubanki ni kike fadawa haka? Zan babballaki, anan"

Tana mai kallon sama da Kasa tace "Allah ko? To bismillah "

Yakara ciccije baki jijiyoyin wuyanshi awaje yace "da aure na kike fira da wani kuma kirika fita dashi? Wai faseelat kinason kiga annabi kuwa? "

Taja tsoki "yazaai inso ganinshi aise ku waliye,"

Yana binta da kallon bacin rai Ya samu wuri ya zauna ya dafe kai don inya cigaba da tsayuwa ba abunda baze faruba, Da kuma tunawa da koyar War manzo (S. A. W) da yace inkayi fushi ka canza mazauninka inkana tsaye ka zauna inkana zaune Ka kwanta in a kwancene ka sauya wuri,

Tatabe baki "ni wlh kana bani kunya mutum ba zuciya nace ka sawwakamin kaki kai wlh uwarka tayi asarar haihuwa don bata Haifi namiji ba anan "

Tuni ya mike tsaye ranshi yakara baci yace "faseelattttttttt"

Da karfi wanda seda yan hanjinta suka kada ya juya yakara kaiwa bango naushi hanninshi ya rika tarara jini, yanata huci yana waige waige kamar wanda ke neman wani abu,

tace "kuma ka sawwakemin inka haihu ga uwarka da ubanka"

Ya rika nunata da yatsa yakasa cewa komi,

Ta juya ta yaye hijabin jikinta tana jan tsoki tace "andeji haushi wlh saratu de tayi asarar haihuwarka "

yana kyarma yana ciccije makoshi yace "ke ke kije kije na sake kin "yanata huci duk ya harmutse.

Ta juyo ta mai kallon sama da Kasa tace "simple abu amma katsaya bani wahala kabawa kanka, to yanzu nasan ka haihu, Allah yabamu alheri "

Ta meda hijab dinta ta shiga bedroom don ajiye ledar hannunta cikin kayanta,

Khalil ya durkushe wurin yafasa kara yana kuka sosai hannunshi biyu yana tumurmuza gashin kanshi dasu, ga jini yanata Bin hannun.

Ta ajiye kayanta ta dauki new phone dinta tafito tana kallonshi duk yabata tausayi,

har tafita ta dawo idanunta na zubda hawaye tazo ta durkusa gabanshi tana kuka ta jawo hannunshi ta ciro head din kanta tajashi ya yage tafara kulle masa hannun nashi,

Tunda ta dafa shi yake kallonta har zuwa yanzu da take kulle mishi hannu ,

Cikin kuka tace "kayi hakuri khalil ka yafemin duk abinda namaka dan Allah ,wlh duk nayi ne saboda ka sawwakamin, amma abinda kagani yanzu ba haka yake ba Allah bantaba zina ba, kayi hakuri banso natafi da hakkinka, inaso kayafemin dan soyayyar da kakemin,dukda nasan be kamata Ka yafemin ba na cutar da kai na kuntata zuciyarka pls forgive me "
Tana gama kulle mishi tasa tafukan hannuwanta ta rufe fuska tana kuka,

Shegina faseelat seda tagama tsula tsiyarta take neman afuwa hohoho 😂🤸🏼‍♀

Yana kallonta cikin zubda hawaye bece komi ba ,

ganin bece komi ba ta tashi tsaye ta juya zata tafi ya riko hannunta ta juya tana kallonshi tana zubda hawaye, shima hawayenne ke fita daga idonshi ya girgiza mata kai yace "karki tafi faseelat plsss ki hakura ki zauna dani haryanzu inasonki "

Ta sa hannunta daya ta zare nashi tana zubda hawaye tace "khalil zama na da kai hatsari ne arayuwarmu duka, domin zan jefa kaina cikin sabon Allah kai kuma zan cigaba da tauye maka hakkinka rabuwar mu shine yafi zama alheri Nagode da duk soyayyar da kanunamin da kulawar da kabani "

Ta juya tafita dasauri tana kuka shima kukan yakara kufce mai, ya zauna yayi tayi,

Tana fita har anfara kiran Maghreb tasamu adedeta tahaye se gida,

Shima yatashi ya wanko fuska ya fito daga gidan ya tada mashin dinshi ya nufi gidan hjya ko yaje yarage jin ciwon da yakeji a duk ilahirin jikinshi.

Me adedeta na ajiye ta ta mika mai 200 ta shige gida tana kara volume din kukanta.

Ummi na ta aikin dare Mubarak na alwala ummi na kiran" auta yi sauri kagani karka rasa sal......."bata idaba faseelat tashigo tana kuka,

Ummi ta tashi tsaye faseelat ta ruga ta rungumeta, ummi innalillahi kawai take memetawa gabanta na faduwa, Mubarak me alwala tuni yamike,

ummi tasamu tace "ke lpya? Kika shigo kina kuka haka ?"

Faseelat ta dago ido da hanci jagege tace "ummi khalil ya sakeni "

Ummi ta dafe kirji "saki? Ke karya kike khalil baze sakeki ba, to ma ubanme kikamishi ya sakeki?"

Faseelat tace "banmishi komi ba kawai saki na yayi "

Ummi tace" karya kike ai ruwa baya tsami banza, hakanan khalil baze sakeki ba yaro me hankali da girmama manya, bari nakira hjya inji miyafaru "
Ta saki faseelat tai daki dauko waya takira hjya,

Mubarak yaje ya dafa faseelat yana tayata kuka.
Chapter 30 · 0% Book details