← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 130

Sashe 89

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabeer yace "Dan Allah friend karika hakuri da yadda rayuwa tazo maka, yanzu kaga Aisha daita dakai bazaa gane marar lpyar ba, ka daure karika shan magani ko kasamu lpy "

"yanzu ka kwantar da hankalinka kabani address na gidansu zanje nasamu mahaifinta nakara bashi hakuri zan kuma nemi alfarmar yafadamin asibitin da suka kaita, kaje kadubota koka dawo dede "

fahad yafada mishi adress din ,

sabeer yace "zanje nasameshi insha Allah zanyi bakin kokarina wurin shawo kanshi amma katashi kasha magani"

fahad yace "magani baze yimin wani amfani ba faseelat itace maganin rashin lpy ta "

Sabeer ya tabe baki yace "Allah yasawwake to, bari natafi gidan nasu "ya mike tsaye,

fahad ya meda kanshi cikin duvet, da hannu sabeer yayiwa Aisha dake tsaye tana hadiyar zuciya magana akan ta biyoshi, ta bishi suna fita kofar dakin, sabeer ya juyo yace "kiyi hakuri Aisha da yanayin shi, karki bari suratan shi su dameki naga kamar baya cikin hayyacin shi, kiyi hakuri ki sa masa ido "

Aisha tai murmushin da yafi kuka ciwo aranta tace aiba yanxu nafara jin irin wadannan daga bakinshi ba, afili tace "Tom nagode Dan Allah kayi bakin kokarinka wurin samo mishi address na gidan nima zanso yaganta koya dan samu sauki "

sabeer ya lumshe ido ya bude yanajin matsanancin tausayinta yace "I will do my best "

ya juya yatafi ita kuma takoma dakin ta kwanta gefen fahad don hakanan take kokari amma zuciyarta matsanancin ciwo take,

sabeer na cikin mota yana tuki hannunshi daya akan bakinshi yana tunanin maganganun fahad,yace"kammmm amma wlh Aisha na hakuri, wannan irin so haka to ko ya zaman nasu yake? nide insha Allah bazan bari matana sugane wacce nafiso ba,"

har yaisa unguwarsu faseelat gidannasu a kulle dayake komi acikin natsuwa yafi hankali seya nufi wasu samari dake zaune can gaba da gidan bayan ya musu sallama yatambaye su kosun san inda zesa mu alhaji maaruf,suka fada mishi ai shagon shi nanan kofar keke, ya musu godiya ya kama hanyar kofar keke don ganawa da abba,

gaskiya duk group din da baa comments zandena turawa aciki kunsamu awani wuri, yan groups dina kuma zanfara removing marassa magana wasu ma tunda suka shigo basuyi magana ba kar in cire mutum yaji badadi shiyasa nafada kurika comments please,

shalele novels group
Shalele value group
shalele boost group
raggon miji fans 123

duk wace batason ganinta awaje tarika comment.
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

7⃣5⃣

*page dinkune yan group dina shalele novels group, kai jiya kun matukar burgeni wannan ruwan comments haka, naji dadi sosai Allah yasa ku dore 😍*

Ba wuya ya gane shagon shi ya shiga ciki da sallama bakinshi,

Shagon ba kowa ciki don safiya ce mutane basu fito ba, abba ya amsa sallamar yana kallon sabeer,

Sabeeer yaja bench ya zauna acikin ladabi yace "abba ina kwana ya mejiki? "

Se sannan abba ya gane ba siyayya yazo ba yace " lpy lau dasauki "

Sabeer ya kara sunkuyar da kai yace "abba ni abokin fahad ne aminina ne sosai, nazo ne nakara baku hakuri akan abinda yayi wlh yayi nadama sosai yana cikin tashin hankali yanzu haka ma baya lafiya, Dan Allah abba amishi hakuri kar a rabasu domin yana sonta sosai kishi ne ya rufe mai ido har ya mata haka "

Abba yayi murmushinsu na manya yace "u only know about ur friend, yayanta da kannenta suna nan suma duk basajin dadi atare suke jinyar, kishi ai bahauka bane daze mata irin wannan dukan haka, don kishin ma nada kyau manzon Allah (S. A. W)cewa yayi wanda baya kishin matar sa baze shiga aljanna ba, amma shi nashi yawuce akira shi kishi gaskiya "

Sabeer yace "Dan Allah abba kuyi hakuri kudauki wannan abunda yafaru a matsayin kaddara "

Abba yace "mun dauki kaddara kam amma seya saketa "

Sabeer yace "kuyi hakuri dan Allah wlh duk gidannashi ya birkice rashin faseelat, shiba lpy matarshi ma yarshi ma, Dan Allah kuyi hakuri tunda yagane kuransa nasan nan gaba baze sake ba "

Abba yayi shiru sabeer ya cigaba da bada hakuri,

Jim kadan abba yace "nifa nadade da yafemasa tunda ya sameni batun saki kuma bani zebawa hakuri ba seyabari idan alhaji yadawo daga Niger yaje yasameshi idan ya yafemishi shikenan danni haifuwar yara na kawai nayi amma alhaji yafini son su yafini kula dasu danhaka nabar masa ragamarsu seyajira shi har yadawo nanda kwana goma "

Cikin ran sabeer yace "tirkashi yo shi yana kai kwana goman ma "

Afili yace "to nagode sosai abba Dan Allah ina rokon alfarma abani address na asibitin da faseelat take ,wlh yar shi ma kullum kuka takeyi tanason ganin antin ta atemaka Dan Allah "yayi kamar maroki,

Abba ya yamutsa fuska yace "nan ne asibitin turai room 9"

sabeer yace " nagode sosai abba ina kuma kara baku hakuri akan abinda abokina yayi "

abba yace "bakomi "
Sabeer ya mishi bankwana ya tafi,

direct gidan fahad yawuce, Aisha ta budemai yashiga yana shiga dakin da fahad yake ya zauna gefen shi ya furzar da iska ya dan bugi fahad yace "katashi muyi magana "

fahad ya yamutsa fuska jikinshi na fidda wani irin suraci yace "komi zaka fada kafada inajinka kaje baka samesu ba ko? Bashi ne maganar ba "

Sabeer yaja tsoki yace "to wlh zanyi tafiya ta in baka tashi ba nasameshi har shagonshi nabishi amma zan tafiya ta "

fahad ya tashi yana yamutsa fuska yace "inajin ka "

sabeer ya kalleshi duk yadda ya koma yace "look at you hmm, na sameshi nabashi hakuri sosai yace shide ya yafe amma seka saketa da nai ta bashi hakuri yace shi yahakura sede kajira yayanshi da yatafi Niger har yadawo kabashi hakuri in ya hakura shikenan yacemin nanda kwana goma ze dawo "

fahad ya tabe baki yace "kafin kwana goman na mutu ai ,wlh ina cikin hali zuciyata ciwo takemin kamar zata buga"

sabeer yace "kai kasani ai kana mutuwa ni kuma nasamu mata "

fahad ya wurga mai harara sabeer yayi karamin murmushi yace "eh mana ko haramunne?"

fahad ya koma ze kwanta sabeer yace "jira mana inada good news bayan bad one's nasamo maka asibitin da take da room number "

fahad yafasa kwanciyar yace "wace asibity room nawa? "

sabeer yace"turai room 9"

fahad naji ya yaye duvet din yatashi tsaye Aisha na gefe na kallon ikon Allah,

ba bata lokaci ya bude wardrobe ya dauko jallabiya ya zira ya dauki key din mota yayi hanyar fita ,

sabeer yace " kai malam bazaka tsaya muida maganar ba? ko godiya aikatsaya kamin "

fahad ya juyo yace "thanks ,kuma kafitomin daga dakin mata "ya juya ya bude kofa yafita yana sauri,

Sabeer yayi murmushi ya girgiza kai ya tashi tsaye, ya kalli Aisha yace "Allah yabashi lpy ni natafi aita hakuri lokacine "

Aisha batace komi ba, ya fita,

Koda yafita har fahad yabar gidan ya shiga motarshi ya nufi office,

fahad yayi ta sharara gudu cikin mintuna kalilan yaisa turai yana tafiya ahankali jikinshi ba kwari har yaisa kofar dakin,

nan kuma gabanshi yarika faduwa yayi knocking so biyu omer da tunda yazo duba faseelat yakasa tafiya saboda yadda ya ganta yana zaune yana bata abinci yace "turo "

Jiki mace fahad ya tura kofar dakin yana shiga yaga faseelat jikin omer ,zuciyarshi tayi mummunar bugawa, (ana nanfa me hali.....) dasauri yafara a'uziya yana korar shedan aranshi

Faseelat idonta a lumshe suke itakadai tasan yadda takeji abubuwa Sun jagule mata ba ciki ba fahad ga ciwo, kamshin fahad daya kewaye dakin yasa faseelat ta bude ido ta ganshi tsaye kamar bashi ba duk ya rame ya jeme yayi wani iri, tausayin kansu yakamata ta meda ido ta lumshe,

kallo daya omer ya mishi ya daure fuska tamau,

fahad yasamu yakara dedeta kanshi ya karasa ciki,

Ya mikawa omer hannu, omer yabashi sukai musabaha kowa ya zare nashi,

Omer ya dauki spoon yakara kaiwa setin bakin faseelat ,ta kauda kai idonta lumshe,

Omer ya kwantar da ita ya ajiye cup din yafita don in yatsaya bazaa kwashe lpy ba,

Bakowa dakin domin ummi tafita,

fahad yakarasa bakin gadon da faseelat take kwance yana kallonta tayi muguwar rama tayi fayau,

Faseelat kam taji dama da taganshi amma bataji dadin yadda taganshi duk yafita hayyacin shi ba,

Fahad Ya zauna kan bed din yanajin matsanancin tausayin ta ya dora hannu akan cikinta , yace "I'm sorry honey I hurt you, na rabaki da farin cikin ki I'm very sorry kiyafemin " hawaye suka zubomai ,

faseelat bata bude ido ba tai shiru se takara jin kewar cikinta don tunda yana 3wks yafara mata motsi,

Fahad ya riko hannunta ya rungume a kirji ya saki kuka, tabude ido tana kallonshi ba tayi shiru dan tanajin haushin shiba ne tayi shiru ne don kartai magana tayi kuka don inde tabude baki kuka zatai, ganin yana kuka yasa tafara hawaye,

irin muryar marassa lpy tana hadiye kukanta tace "hero kadena kuka,bakamin komi ba, nasani acikin tunaninka bazaka yimin haka ba,kayi hakuri kashare hawayenka banajin dadin ganinsu"

fahad yanata kallonta da jikakkun eye lashes dinsa tunda tafara magana ,yace "we lose our baby "

faseelat ta lumshe ido ta bude tace "Allah ze bamu wani, kadena damuwa "

Fahad be dena hawaye ba na tausayi da kaunar faseelat yariga yasan tana sonshi sosai yanzu dabata yi fushi dashi ba sonta yakara ninkuwa a ruhinshi,

faseelat tace "stop shedding ur tears pls, har yanzu inasonka mijina nayi kewar ka sosai, kewarka tafi ciwon jikina zafi amma na samu lpya da naganka "tasakar mishi murmushi,

Ya share hawayenshi ya duka ya mata kiss a wuya yace "I miss you too kidubeni yadda sonki ya medani ina wahala honey "

faseelat tai murmushi tace "I'm very sorry ina Princess?ina anty I hope suna lpy "
Chapter 89 · 0% Book details