← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 130

Sashe 2

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi wanka tayi tashige daki, batareda ta waiwayi faseelat ba, itako faseelat bacci ne ya dauketa,

Can wajen 10am ummi tafara jin sallama tana fitowa taga wata kawarta a aikin hajji suka hadu matar ta girmi ummi nesa ba kusa ba amma jininsu yazo daya saboda a room daya suka zauna lokacin hajji ita kuma ummi tana matukar girmama na gaba daita, wannan yasa suka shaku da maman khalil, ko bayan Sun dawo daga saudiyya suka cigaba da zumunci.

"maraba maraba da maman khalil "

Hjy saratu tana faraa tace "yawwa Hjy asiya "
Ummi tace "shigo ciki mama naga kintsaya waje mushiga ciki "

Maman khalil na murna suka shige ummi tanata nan nan daita takawomata pure water da zobo taajiye sanan ta zauna ,"sannu Hjy ,sannu da zuwa, yasu khalil? "

Hjy saratu tace "lpyarsu lau siyama ma na gaida faseelat"

Ummi tai faraa da cewa "ihhhhn siyama kenan kullum tana gida kamar ba macen aure ba "

Hjy saratu tace "mijin tasamu me sauki shiyasa "

Ummi tai murmushi

Suka cigaba da fira can Hjy saratu tace "Hjy dama wata muhimmiyar magana nake tafe daita Allah yasa zansamu abinda nazo nema "

Ummi tai shiru tana saurarenta

Hjyar ta cigaba da cewa "kinsan yara na biyu kacal khalil da siyama, siyama de tayi aure gashi harda jikoki na samu, amma khalil shiru yaki ya fiddo mata gashi yanzu har yana batun Shiga shekara 35 kuma bayada niyya na mishi magana baso daya ba ba biyu ba amma shiru, to daga baya na Yanke shawarar zabar masa mata,saboda shi mata basa gabansa kwata kwata.
nayi tunanin ,na duba na hango yarki faseelat ce ta dace dashi, batun yau ba ina fadamiki yaranki na burgeni wannan yasa nakeso inhada Zuria dake, inaso yaro na yazo sugana da faseelat in sun dedeta se ayi buki.

Ummi hamdala kawai take cikin ranta Allah ya amshi adduarta,

ta danyi shiru sannan tace "..........
[7/12, 10:57 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

*Writing by MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

3⃣

*Dedicated to SIS ZULAIHAT RANO*

Sannan tace "naji dadin wannan maganar Hjy kuma inafatan zasu fuskanci juna Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama alheri *

Hjy saratu tace "amin amin Insha Allah gobe zezo su gaisa daita din saboda baniso a dau lokaci"

Ummi tai murmushi "tom madalla zansamu faseelat da maganar"

Hjy saratu tace "ni tunda nashigo bangantaba nade san su Mubarak ana school"

Ummi tace" inajin bacci takeyi, bari natado miki ita "

Hjy tace "aa barta bari na tashi nawuce gida "

Ummi tace "tom nagode kigaida gida "

Suka fito ummi tayo mata rakiya suna fitowa tsakar gida sega faseelat ta fito zata shiga toilet wanka tana daure da towel ,tana ganinsu ta sunkuya ta gaida Hjy saratu dasauri tashige toilet, Hjy saratu ta bita da kallon birgewa sannan tawuce,

Ummi wasai ta nufi kitchen ita kuma faseelat tai wanka tai brush sannan tafito neman abinci, tana shiga kitchen ta tarda ummi na aiki batareda tace komiba ta debi kunun tsamin daakayi tafita shaf shaf ta shanye ta dawo tace ummi ta bata tayi aikin, ummi tace "a,a barshi zan dan tayaki se muyi tare "

Faseelat tace "a, a ummi kibari nayi "

Ummi tace "to" tasamu wuri tazauna tace "miko min albasa da latas din na yanka miki "

Faseelat ta mikomata ummi nayanka take magana, "faseelat! "

Faseelat ta juyo "naam ummi "

Ummi ta cigaba da cewa "Hjy saratu ce tazo da maganar tanason danta khalil ya aure ki shine ta zo neman izini zezo kugaisa kufahimci juna"

Faseelat tai kasak'e can zuwa tace "to ummi "

Ummi tace "gobe yana nan zuwa seki shirya sannan inaso Dan Allah badanniba ki saurareshi "

Faseelat takara cewa "to ummi "

Ummi ta cigaba da cewa "Hjy saratu mutunniyar arziki ce tun bayan dawowarmu daga saudiyya ta daukeni kamar kanwa tana sona da zuria ta baki daya, gashi hartanason hada jini dani, Allah ina rokonka kasawa abinnan albarka"

shiru faseelat tai ta cigaba da tsintar waken dake gabanta.

itama Hjy saratu tana komawa gida tafadawa mijinta yanda Sukai yace Allah yasa haka shine mafi alheri .

se 2pm khalil yashigo gidan dakin Hjyar ya wuce yafada kan kujera "I'm very tired hjy "

Ta harareshi "se kace wanda yayi dako "

yace "Allah Hjy barci ne a idona sosai bari na tashi naje naci abinci na kwanta "
Har ya mike Hjy saratu tace "kai dawo kazauna"

Yace "to "yaxauna yana jiran mi zatace

"dazunnan naje munyi magana da wata kawata zakaje kaga diyarta intamaka shikenan, tunda kai kakasa fiddowa da kanka gwara ni na zabarma, kashirya gobe kaje kaganta inka tashi kamin magana zanbaka address inafatan kagane? "

Tunda tafara magana yake kallonta "amma Hjy kinaganin ba matsala ni da kinkara min lokaci banfa isa aure ba gaskiya "

Hjy ta watsa mashi harara "tashi kaban wuri "

Ya tashi har ya kai kofa ya juyo "amma Hjy kinaganin ita yarinyar zata amince? "

Hjy saratu takara watsa masa harara

Abinda yasashi juyawa kenan ya fita dakin yanajin duk ta takura masa aishi be tashi aure ba gaskiya shi ko kallon mata bayayi bare soyayya,kusanma tsoron matan yake ranar kwana yayi beyi bacci ba ya nata saka da warwara Karon farko da ze tunkari mace me zece mata? Mi zasu tattauna shine tunaninshi kawai.

Itama faseelat batai bacci ba will he be like her dream guy? gaskiya bazata taba yin aure ba harse tasamu muradin ta idan ya mata fine inbe mata ba bazata aureshi ba ko,

Haka ta kwana sake sake,

Washe gari

Bayan tagama aikace aikacenta na yau da kullum sannan ta shirya tasa ka riga da sket ta yafa gyalenta ta zauna jiran tsammani dan ummi sunyi waya da hjyar tace karfe 11 zezo,

agogo ta kalla taga karfe 11 saura ta zare gyalen tana tsoki ta kwanta kan bed baccin da bataiba ya dauketa 11 dede ya iso kofar gidan wata yarinya yasamu yace ta kira masa faseelat, gabanshi nata dukan goma -goma.

Yarinyar nashiga ummi tace kice gatanan zuwa, tashiga dakin faseelat ta tadata"kitashi kigyara
fuskarki maza "

shaf -shaf ta sauka daga gadon ta kara kallon madibi bata tsaya kara shafa komiba tafita she's eager to see him.

tana fita kofar gidan ta diba hannunta na haggu taga roba -roba fa ke ,cikin ranta tace oh God ko yar honda bedaita mtssssw.

Tayi sauri ta juya hannunta na dama, se gashi tsaye yanata son ganin fuskarta tana waigowa ya zuba mata ido itama shi take kallo daga saman sa zuwa kasa.

baki ne amma not that black idanuwansa a bit tiny hancinsa gajere with medium mouth kayan jikinsa kaftani ya taso hula gaba har kan goshi daf da ido tsawon shi takalla dogo sosai shantaly kenan 😂🙊zufar dole ce tashiga keto mata,

*da akwai matsala fa*🤣

in next page zamuji ya firarsuzata kasance.

Inaganin best wishes da adduoinku Nagode Allah yabar kauna
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

Writing by *MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

4⃣

*dedicated to sis ZULAIHAT RANO*

*All praise be to Allah*

Shi ko kallonta yake saboda ta tafi da hankalinsa tabbas faseelat mace ce da inka kalleta seka kara kallonta, kallon kallo suke wa juna and ita nata kallon tanayi ne kawai amma hankalinta baya tare daita magana ma take da zuciyarta ga abinda take cewa "allahumma ajirni fii musibaty wa aklifly khairan minha, to musiba mana gabadaya tunaninta ya Kare akan mamakin tsawon sa dama duniya a kuma Katsina akwai masu irin wanga tsawo haka? Ta cigaba da cewa ya Allah kaceceni mu rabu da bawannnan naka lpya.

Shiko tashi zuciyar tuni ta kamu da kaunar faseelat ,

Can zuwa ya tattaro natsuwarsa bakinsa na dan kyarma yace "Assalamu alaikum"

firgigit ta dawo hayyacinta still zufa na karyo mata se kace mejin kashi,

Tana mazurai tace "sannu da zuwa shigo ciki"

Wani iri yaji jin muryarta yayi tsaye itakuma tashiga cikin zauren gidan ya bita zalalo zalalo kamar rakumi da akala.

Har cikin zauren babban zaure ne dan already har an ajiye sit din roba biyu tai tsaye ta juyo sannan yakaraso tana nuna masa kujera tace" bismilla "

Ya haye ita kuma tasa gefen gyalenta ta share wata zufa data tsiyayomata ganin kafafunsa Sun dan baud'e kadan,

jiki sanyaye taja kujera ta zauna ta dukar da kai sam bata kaunar ganinsa, beyi mata ba, mi zatayi da baki?dogo kamar ba samude sam baze yiwuba.

Tunanin ta yakatse ne da yafara magana voice dinsa na vibrate saboda yadda yake jin tsoro yace "sannu malama faseelat, Da farko de sunana khalil shekaruna 35 ina teaching a all brighters academic, Hjy ta ta umarce ni nazo naganki mu dedeta ina fatan zamu fahimci juna ni da ke "

wata iriyar murya ce dashi gatanan de, ita kuma faseelat tana son miji me siririyar murya shi ko gata de, kamar wadda aka mara tashiga jijjiga kai, shiru ne ya biyo baya can ta tuna bata kawo masa drinks ba, ta tashi ta kawo masa dudu milk ta tsiyaya a cup ta mika masa, yayi kurba daya ya ajiye shiru beda abin fadi kanta na kasa amma duk dagowar da zatayi seta ga ita yake kallo,

Can zuwa yayi karfin halin cewa "kibani no din wayarki "

Faseelat gabanta na faduwa tana inda inda tace "ni banda waya"

yayi shiru can yace" ba damuwa inafatan nasamu karbuwa? "

tai shiru can zuwa ta daga kai

Yace "Alhamdullilah se na sake dawowa ko? "

Haushi ya kashe faseelat se tambaya yake kamar tsohon makaho ta dago tace "ihhhhhh"

Aiko yayi shiru ya tashi tsaye"ni nawuce "

Afili tace "tow agaida Hjy, a Zuci tace agayas "
Chapter 2 · 0% Book details