← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 130

Sashe 52

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yan jere kau basuma samu Aisha ba don tatafi wurin wadda zata gyarata tun safe,
Sun sha kauyanci sosai agidan set din kujerunta suka samata a dayan bedroom nata da beda su, suka sa mata katuwar plasma dinta, gadonta ko bawuri sede suka koma dashi ganin na fahad yafi kyau,

Shima fahad is busy sunata shirye shiryen yadda dinner zata kasance da daurin aure, don manyan mutane zasu halarta ,

faseelat amarya tun 10 sukafita itada friends dinta, 50k tabiya me mata saloon, akai mata da kunshi se 3 akagama sannan akafara yiwa friends nasu,

dukda he's busy so biyu yana kiranta yana fadin ayi me kyau,

Se after Maghreb suka dawo ta gaji sosai kanta ma Ke ciwo saboda zama da hayaniya,

Fahad ya kirata tana lumshe ido ta dauka kanta a bude yana bin gashin kanta da kallo yace "cutie ya gajiya, naga kingaji kuma ni gani nan zuwa naga kunshin da saloon din in ga ko yayi kyau "

Ta lumshe ido tace "kayi hakuri kaina ke ciwo bazan iya fitowa ba inajin kamar ze rabe biyu ko bude ido banasonyi "

yace "sorry "cikinn nuna tausayi yace "ki daure kiyi salla kisha magani ki kwanta "

Tace "nasha magani ai "

Yace "sallar fa? "

Tana ya mutsa fuska tace "I'm off "

Gabanshi ya bada dummm ya dafe heart yace "Dan Allah kice wasa kike "

ta kalleshi tace "dagaske nake "

Yace "oh my God please help me out"

tai dariya ganin dagaske ya rikice gashi tana son yabarta ta kalleshi tace "gobe ne fa zan gama miye na damuwa "

Ya sauke ajiyar heart kusan so biyu yace "har nadawo dede ai akwai matsala cutie idan kika shigo haka, bari na barki ki kwanta ki huta se gobe Allah yabaki lpy"

tace "amin thank you for your love "

takashe kiran ta lumshe ido sede bacci sam yaki zuwar mata yau a Karon farko tafara tunanin ya zataji idan suna sex, mutane na cewa na farko da zafi itade gani takeyi labari ne yadda takejinta haka gani takeyi dadi kawai zataji, Da wannan tunanin bacci ya dauketa,

Washe gari tun 9 sukabar gida suka tafi gidan wata sistern abbansu can zasuyi setting aka kira masu decorating suka fara gyara wurin,

10 baki sukafara cika gida na nesa dana kusa yan Niger karfe 2:30 suka iso,

yan matan suka nufi gidan setting din lokacin an gama decorating wurin anata shigowa da kayan ciye ciye, se kaikawo akeyi agidan,suka ci abinci sukafara shiri,

Seda akai laasar bayan faseelat ta yi salla ifti ta zauna ta tsara mata kwalliya takoma kamar aljana saboda kyau, ta saka purple da milk lace riga da sket, har mamaki tayi yadda fahad yasan size din ta har dana shouse da brezia, head dinta milk ta yafa dankwalin kayan
ta saka shoes dinta milk me makeup din tace "wow amarya kinfito bari na daukeki pics "

Faseelat ta gyara tanayin different styles with smile on her face, nan fa suka fara daukar ta pics, suna kuma yi tare,

Nan da nan gida ya cika faseelat faraa taki barin fuskarta duk inda ta gifta sekaga kyallin hakoran,

Zuwa biyar bayan yan ciye ciye DJ yadora wuta,

Faseelat cire mayafin tayi ta dage rawa bakin rai, friends nata da yanuwa suma sunata takawa,

Suko su mommy suna can suma suna nasu shirin Aisha ma cikin 2days din nan takara yin fresh saboda gyara,

Fahad da friends nashi suka kama hotel guda duk bakin da sukayi daga abroad anan suka saukesu kuma anan cikin hole din hotel din zaai dinner.

Se 6:40 taro ya tashi saboda sallar Maghreb, se lokacin faseelat ta Tuna da wayarta, ta dauko milk pose dinta ta fiddo wayar wajen kira biyar na fahad,

Hannu na rawa tai calling back yana dauka Kafin yace wani abu tace "kayi hakuri my handsome ina cikin taro banji ringing wayar ba ma se yanzu na Daukota"

yace "OK kina ina zanzo naganki, bazan iya hakura har gobe ba "

Tai shiru seda ta nemo abun fada tace "kayi hakuri plss har goben yanzunnan zaafara waazi kuma se 10 zaa gama "

Cikin takaici yace "yanzu shikenan bazan gankiba? "

Tace "kayi hakuri gobe fa warhaka nazama taka, ta harabada miye na damuwa da yau kadai ?"

Fahad yaja numfashi yace "Amman kisani a takure nake wlh "

Tace "kadaure plss yau kadai de "

Yace "naji shikenan se anjima ko? "

Tace "noo se gobe de don baki bazasu bari nai waya ba "

Yace "to yayi "ya kashe kiran ,bataji dadi ba amma ba yadda zatai ta koma cikin dangi aka cigaba da hidima,

se 1:00am su faseelat suka kwanta don hira kawai suke anayi ana shewa,

Da safe ranar daurin aure tun asuba su faseelat suka tashi, gabadaya tunda tatashi seta rikajin kamar ansaka mata kankara a heart dinta saboda dadin da takeji cikin kwanciyar hankali suke ta hidimarsu,

Aisha ko jiya batai bacci ba da tunani ta kwana cewa gobe iwar haka fahad na tare da wata baita ba ko barawon bacci be dauketa ba da safe dangin ta suka cika gidan su nadiya yan abuja su anty kulsum yan balai su ramlat su mommy hanan sister din mommy da yayan yayarsu mommy wajen su 5 sunata hidima itako tayi sukuku ba damar tai kuka su taso mata suce batai gadonsu ba, tana kuka akan kishiya, don haka tai gum,

karfe 1:30 faseelat tai wanka tana ta faraa, baaba ta shigo dakin taga sunata shiri ta kalli rahma tana dariya tace "rahma wannan karon banji kina batun sandar famfo ba "

Rahma ta kalli faseelat tace "baaba ainaga tazama yar hannu nagama akagare take kamar ta kai kanta can "yan dakin suka kwashe da dariya,

Rahma tace "to wannan karon shawara zan baki, kinaji ki dage kirika wage kafa sosai ba wata kunya kuma kina gyara can din don kifi tunkiyarki armashi "suka sa dariya faseelat ta harareta tana ganin rashin kunyarta,

Se biyu me mata makeup tazo tayi salla akaimata kwalliyar tasaka wani tsadadden Sari red color,

Tana jujjuyawa tace "seni matar fahad "

sukayo mata ca wai ta cika zumudi tun baa daura ba,

ango fahad yasha white shadda taji aiki yanata jindadi suka nufi masallacin da zaa daura auren,

After salla karfe 2:40 aka daura auren fahad dawood da faseelat maaruf akan sadaki dubu 100, tunda fahad yaji andaura yakara fadada fararshi mutane sukafara bashi hannu suna mishi Allah yasa alheri, shiko tunaninshi duk ya koma kan faseelat soyake yakirata duk yau basu gaisa ba, bayan an daura akafara reception,

Samarin gidan ne sukafara shigowa wannan ya tabbatarwa da faseelat andora,

da gudu tana murna tayakice mayafin sarin tai hanyar toilet,

Zainab tace "Dan Allah amarya kibi sannu karki bata makeup din kinsan yanzu zamu tafi wurin waazi "

Faseelat ta juya ta kalleta tace "ke alwala zanyi ma bakidaya se asauya wata "

Zainab ta bude baki zatai magana faseelat ta shige toilet tayo alwala tazo ta kabbara salla tana godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana,

Bayan tagama aka zauna sauya mata makeup ana cikin mata makeup din fahad ya kira jin ringing din jiki na bari tace "anty fadila mikomin waya ta dasauri "

Fadila ta mika mata tana sauri ta dauka takara a kunne tanajin sanyi nabin gabban jikinta,

🎶🎼🎶🎼🎸🎻yau ranar kuce munyi murna ta aure fahad dawood ango faseelat amarya 👯🏽💃🏼💃🏼💃🏼👯🏽👯🏽👯🏽

Ina mawakan gidannan ku fito ku wake Amarya da ango,🤣

afara shirin cashewa a wajen dinner 🥰

[8/5, 6:08 PM] +234 815 712 7134: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

5⃣5⃣

Cikin farin ciki fahad yace "my wife! "yayi shiru,

Ta lumshe ido ta bude tanajin mugun dadin sunan tace "naam my husband"

Ya rumtse ido yanajin nice yace "ina cikin farin ciki na zama mijinki "

Tai murmushi tace "me too "

Sukai shiru kowa yanata dokin dare bayan seconds yace "so, what I will have from you? "

Tai murmushi tace "everything dear "

Ze magana sabeer yazo wurinshi yace "mr zumudi kayi hakuri mu sallami mutane tukun taka ce yanzu kome is now yours ,muje ga mutane can na ta nemanka suna so su tafi "

Fahad ya harari sabeer yakara kanga wayar akunne yace "sorry cutie se munhadu a dinner "

Tace "OK take care "
Ya kashe kiran yanata wa sabeer surutu suka koma cikin mutane,

Faseelat tana gama wayar ta dora ta a setin heart dinta ta sauke numfashi ido a rufe,

Me makeup da kowa kallonta suke tayi,

Fatouma takasa hakuri tace "waini faseelat yaushe kika koma haka? "

Faseelat ta bude ido shaf ta manta dasu ta rufe baki tana dariya tace "na manta da kuna wurin ai "

Fatouma ta kalli agogo tace "nanda 3hrs zamu kaiki mu huta da rashin kunyarki"

Faseelat tana dariya tace "can't wait to that time "

Suka fashe da dariya akagama mata makeup suka tafi gida halartar waazi,

suna shiga cikin gidan faseelat na washe baki take gaida mutane ummi tafito daga dakin faseelat din ta ganta tana ta faraa tai mata wani irin kallo, faseelat ta matsa tana dariya tai hugging ummi ,

Ummi tace "Allah ya shiryeki faseelat "

faseelat tai dariya tana boye fuskarta,

Ummi ta janye ta, su faseelat suka wuce kowace ta samu kujera ta zauna,

Wannan karon waazin ya tafi ne akan hakuri da shawarwari ga amarya yadda zata samu zuciyar mijinta,

Har aka gama faseelat batai kuka ba don wani wurinma se kayi dariya yadda malamar take bayyana kome a fili yadda ake tarairayar oga,

Da laasar aka gama waazi sukayi salla zasu koma gidan baba babba Dan 6 zaa dauki amarya,

Faseelat a tsakiyar dattijai anai mata huduba me shiga jiki batasan lokacin da tafara kuka ba,

Bayan angama suka tafi daita gidan ,
Chapter 52 · 0% Book details