← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 130

Sashe 16

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faseelat tabuga tsoki ta ajiye wayar ta ture Cup din tea din gabanta har seda ya dan zuba, ta cigaba da doka tsaki, can kuma se tayi shiru tace "a, a what's happening to me ne?kode na hauka ce ne? Miyasa nake son kallon pic din shi, why nake kishi da matarshi, in na fahimta son shi nakeyi, "ta dafe kai tareda fadin "oh god" taja wani sauti da baki "shishhhhh, I'm deceiving my self fa ,ni da ke da aure, kuma ma yafini akomi koda banda aure he will not going to love me "tai shiru bata gama tunanin ba ta jawo wayarta tabi messages da aka mata hoping that taga na maman amira,

Tana ta bi har kan number tai sauri tashiga, maman amira na online faseelat har mamaki takeyi why take online ko da yaushe maybe tanada house maid ne cewar zuciyar ta, tafara karanta message din ta kamar haka "antin amira kintashi lpya? "
Ta duba time da akai message din be dade ba saboda 8 akayi shi, faseelat ta tura mata" lpya lau ,ya amira "

Maman amira na tsaka da charting taga message din faseelat tashiga tai mata reply da "lpya lau ya zafi ?"

Faseelat tace "gashi muna tasha, kuma ana maku zafi sosai garinku ?"

aisha tace "eh gaskiya katsina akwai zafi dan in muna Abuja be kai haka ba "

Faseelat tace "kina katsina anty? "

maman amira tace "eh anan mijina yake nima anan na taso, "

faseelat tace "ai nima yar katsina ce "

Maman amira ta turo mata 💃🏼"kice zanga faseelat watarana "

Faseelat tace "insha Allah "

Maman amira tace "Allah ya yarda da zanji dadi sosai "

Faseelat ta tura mata smile face sannan ta sauka jin sallamar Mubarak bakin kofa, ta aje wayar tafita suna murna suka rungume juna, sannan ta sake shi, tana dariya tace "auta se yau? Amma de wuni zakamin ko?"

Yace "eh yaya se 2 zantafi "

Tace "yawwa dan kanin muje ciki "

Tajashi cikin dakin tanajin dadi ganin dan uwanta.

da karfe 12 tashiga kitchen tai white rice da stew da coslow, sannan ta dafa mai wake daban, tana gamawa ta zuba a warmers ta kai daki Bayan ta Dora su a big plate ,

Tawuce toilet tai wanka tai shafa bayan ta saka kaya, ta zubo musu abinci itada Mubarak a plate daya suna cikin ci, Sega khalil yayi sallama.
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

*PAGE* 2⃣1⃣

Suka amsa atare itada Mubarak faseelat tace "sannu da zuwa"

Yace "yawwa ya gidan? "

Tace "lpya lau "

Khalil yace "a, a abokina kaine a gidannamu"

Mubarak yace "ina wuni "

Khalil yace "lpy lau, yasu ummi ?"

Mubarak yace "suna lpya "

Khalil yace "madalla "yana kallon yanda suke cin abincin sosai abun ya burgeshi, ya wuce daki ya rage kayan jikinshi ya shiga toilet,

Faseelat bata tashi ba seda ta koshi cin da sukeyi da Mubarak yasa takarajin dadin abincin sannan ta ajiye cokalin ta mike ta dauki tray din ta kaimishi daki, har lokacin be fito ba, tana ajiyewa tafito suka cigaba da firarsu da dan auta,

Khalil yana fitowa ya zauna cin abincin koda yabude bowl din cow slow din ya meda ya rufe ,saboda be taba ci ba donshi dan gargajiya ne, ya zuba shinkafar shi da wake yacika cikinshi saboda yaji dadin girkin ya kora da ruwa ya dan kishingida,

Se karfe ukku Mubarak ya tafi sannan shima khalil ya fito ya koma shago,

Itako faseelat bakaramin dadi take ji ba in bayanan hankalinta kwance taita charting dinta inko yana nan to duk se taji ta atakure,

*Bayan sati daya* har yau khalil be taba yunkurin kusantar faseelat ba saboda dandanan yake release da zaran ya tabata, ita kuma faseelat yanzu gabadaya batada walwala saboda a matse take ba ranar da bata ciwon mara shiko kullum se ya lagude ta wani lokaci ma se yana shago ya dawo ya lallaguda ya koma, wani mugu mugun haushin shi takeji, yanzu ko ya tabata bata jin dadi don tasan wahalar da zata sha,

A dan zaman da sukayi basu wata fira atare, kuma bawata soyayya zama suke kurum kuma kullum faseelat kara gano abinda bataso take a wurinshi, na farko de shi mutum ne me bin diddiki duk abinda ke faruwa agidan yana lura dashi, sannan duk yawancin abinda yake so ita faseelat batason su, kwata-kwata bayayin wani abu da ze burgetta, kuma yanada mako tun bayan kaji biyun da yakawo na amarci haryau be kara kawo wasu ba sede ya siyo jan nama ko kifi ayi miya dashi, dama wasu mazan da kashigo ciki shikenan, wani karin takaici se tusar da yake bugawa a gabanta hankalinshi kwance yayi ta barka tusa, to ba dole ba kullum wake kullum wake aidole arika tusa, dan dole faseelat ke kwana bedroom daya dashi,

Yanzu kusan kullum da ciwo take wuni da bakin ciki da haushi yau jumaa bayan yayi breakfast yace ta shirya karfe 12 ze dawo ya kaita gidan hjy ,in antaso masallaci ya kaita gidansu da marece se yaje ya dauketa,

Tana murna tace to ta tashi tana shiri da sauri,
Shi kuma ya fita, tana gama shiryawa taje ta dafa faten doya da wake saboda tai sauri tana gamawa tai wanka ta shirya, ta zauna jiran dawowar shi,

Wayarta dake kan center table ta jawo ta tsaya ta karewa wani new pic na fahad da ta dauko daga status din maman amira kallo sannan ta shiga what's up, zuwa yanzu Sun matukar sabawa da maman amira dan yanzu baya ga charting har waya sunayi, ita kuma faseelat son fahad bakaramin damka yayi mata ba, baya ga kyanshi kullum maman amira cikin zuzuta mijinta take a group, tana ta yabonshi tana fadin wasu abubuwa da yawa a rayuwarshi, yanzu haka faseelat tasan mi ya fiso a rayuwarshi, tasan best drink nashi tasan best food nashi tasan style da yafiso,

ita maman amira batada labari a fili amma a chart akwai surutu kuma baruwanta taita fadin mijinta kaza mijinta kaza, ga dora pic nashi a status da bata dauka bakin komi ba,

faseelat ta shiga message da maman amira ta aiko mata "kawa muntafi china kiyi hakuri ban fadamiki ba nima bansan da tafiyar ba, maybe muyi 1 month sannan mu dawo, zanyi missing naki bye "

Faseelat se taji ba dadi ,taso suyi bankwana jiya baki tai tayi shiyasa bata samu damar hawa online ba, tai shiru tana tunanin rayuwarsu maman amira su kullum cikin tafiye tafiye suke yanzu suntafi bazata kara samun pic din fahad ba ,ta bata fuska tanajin haushi, ji tayi kamar ta kirata tayi mata bankwana se ta fasa tana tunanin sun riga Sun daga,

Ana haka sega khalil ya dawo ya yi sallama ya shigo room din ta tashi zaune ta gyaggyara zaman rigarta ta mike tsaye tace "ai na shirya bari na dauko hijab dita "

Shi ko yayi sototo yana kallonta bata taba sa kayan ba, riga da sket blue atamfa kugunnan ya fito sosai, nonuwan kuma Sun yo sama, saboda dan matsewar da rigar tayi, har tafara tafiya ya jawo hannunta ta fado kan jikinshi tasaki kuwwa, ya kure ta da kallo itama ta zuba mai ido tanajin haushi yanzu kuma kwalliyar tata ze bata kila,

Ya cigaba da kallonta dan zamannan da sukayi son faseelat yakara ninkuwa a ranshi fiye da can baya, taga de beda niyyar sakinta tafara mutsu mutsun kwacewa ,me makon ya saketa se yasa dayan hsnnunshi yakara zagaye ta,

Ta turo baki gaba "ni ka sakeni plssss "

Yana mata kallon love yace "shine zakiyi gayu haka? ki rikita ni bayan kinsan fita zamuyi "

Ta balla mai harara tana kara tunzuro baki yace "to yanzu mushiga in biya wannan tsadaddar kwalliyar,

Faseelat ta fiddo ido waje cikin ranta tace "ni nabani da khalil "

tadan tsuke fuska tace "kasaken plsss mutafi idan mundawo se kabiya "

Yace "to naji amma se kinmin kiss a nan"

Yanuna gefen kuncinshi,

faseelat ta kalli wurin tace "to sakarni ai sena kara tsawo sannan "

yana sakinta ta gudu daki, ya girgiza kai yana murmushi ta sako hijab dinta tafito tana sauri tai waje yabita da kallo yatashi ya bita,

Suna tafiya bame cewa komi har suka isa gidan tana sauka yayi parking suka shiga tare ,

Hjy na cikin wanki suka shigo tabisu da ido tanajin haushi tace "aaa maraba da amare "

Faseelat ta zukunna har kasa ta gaisheta, hjy ta amsa tana fadada faraarta,

faseelat Tawuce cikin dakin hjy ,sannan khalil yace "hjy wanki ake "

Tace "eh wlh na kwana biyu banyi ba shine nake rarragewa"

Sega faseelat tafito har ta ciro hijab tunda tafito hjy ta kafeta da ido ganin surarta me cike da tsari kamar ita tai kanta, shima khalil Ita yaketa kallo,

Faseelat na kawowa wurinsu ta ja sket dinta sama ta duka ta fara dauraye kayan da hjy ta saka a bokiti,

Hjy tace "faseelat kibarshi mana karki bata jikinki yanzu nagama "

Kan faseelat kasa tace "ki barni na karasa hjy rana tayi zafi, ki koma daki "

hjy tace "daga zuwanku to shikenan bari na rage wadanda suka bushe ki samu wurin shanya "

Khalil na gefe tunda faseelat ta duka rigarta ta zazzalo yake kallon breast nata, yanajin dadin yadda ta mutunta mahaifiyarshi,

hjy ta kalleshi tace "to kai ba masallaci zaka ba? Katashi ka tafi kar ka makara "

Ya dago yana sosa kai yamike yace "to Sena dawo "

Ya juya yana tafiya yana juyowa yana kallon faseelat, so daya ta dago taga yana kallonta takoma ta duke ta cigaba da wankinta,

Hjy na kallonshi tace aranta "wawan banza kawai se wannan abu yake ko kunya beji "

Ta juya daki tana gama linke kayan ta shiga wanka shaf shaf faseelat tagama wankin ta shigo dakin tana daga kai taga duk yana ta tashi ta dauko duster ta sharo ta tayi yan kakkabe kakkabe ta share dakin tai moping tasaki labulaye ta fiddo wata madarar turare daga jikarta ta goggo a kujerun dakin,
Chapter 16 · 0% Book details