← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 130

Sashe 87

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta dawo tai tsaye kanshi tace "lpy me kazo yimin nan? "

fahad ya tashi zaune kanshi na sara mishi kamar ze kuka yace "Dan Allah umma kiyi hakuri wlh nayi nadamar abinda na aikata,"

umma tace "to ni aiba fushi nai ba, don kai kaiwa kanka ,don haka katashi katafi wadanda kawa laifi yakamata kabawa hakuri bani ba"

yace "umma nayi zarya gidansu akulle narasa yadda zanyi "

Ta tabe baki tace "to dama ya zaai ka iskesu tunda kaja musu jinya hakuri zakai har tasamu lpy insun barmaka ita to ,katashi katafi fita zanyi akwai inda nikeson zuwa "ta tafi tabarshi dafe da kai fahad ya rasa yadda zeyi kwana guda jinshi yayi kamar shekara,

umma nagama shiryawa ta sa me aikinta ta kaimata girkin da tayi da lemun da tahada a mota sannan tafita ta nufi asibitin,

abul da omer basunan suna school ,dakin daga ummi se Mubarak da ishak,

umma ta shiga tana ta faraa lokacin har ummi takama faseelat tayi wanka ta sauya mata kaya,

Bayan ta zauna suka gaisa ,

umma taiwa faseelat ya jiki sannan ta tambaya kotaci abinci, ummi tafada mata bata ciba, ta zuba farfesun kayan ciki da tayomata ta tada ta zaune tasa hannu ta rika bata abaki,

agidan hjy kau anata zaman gaisuwa dan ta tabbatar khalil ya mutu don beje batsari ba kuma baya kt hakan ya tabbatar da ya mutu tunda safe su kawu manu sunje inda akai accident din sunga yadda motocin sukai hakan yasa sukadawo suka zauna ansar gaisuwa,

mata anata zuwa yiwa hjya gaisuwa da barka lokaci daya,

Anata kiran fahad da wayoyin Suka isheshi da kara seya kashesu gabadaya donshi bata wani aiki yake yanzu ba,

yana zuwa gidan mommy ya tarar da Aisha main palo tana zaune tana kallo ga amira da tai kukan anty har tagaji kwance kan cinyarta,

amira na ganinshi ta tashi ta haye sama da gudu,

Aisha tabishi da kallo duk ya fita hayacinshi,

Fahad ya zauna gefen Aisha ya kwantar da kanshi akan cinyarta yasaki kuka me taba zuciya,

Aisha ta rungumo kanshi tana share mishi hawaye idonta tafff da kwalla tace "kayi hakuri yaya kadena kuka "duk atunaninta gudunshi da amira keyi yakewa kuka,

Yana kuka yace "meyasa zasumin haka? meyasa zasu dauketa daga gareni ina tsananin sonta bazan iya jure rashinta akusa gare niba "

Aisha ta tsaya da share mai hawayen tace ".....
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

7⃣4⃣

*ban manta daku ba,kuna raina,lady ,maman zainab, Aisha habib, Firdausi,sede kundena comments why?*😒

*soupnas* comment dinki nasani farin ciki keda *maman nour* comments dinku yana kayatarwa kucigaba da gashi 💃🏼, *maman nour* wai ina kawalliyarki *earmeenatuwa*🤣

Aisha tace "bangane ba yaya? "

Yana cigaba da kuka yace "iyayen faseelat Sun daukemun ita sun tafi daita"

Aisha farin ciki ya mamaye zuciyarta batasan lokacin da tasaki murmushi ba tace "Allah yasa daga can ai can"

Jin abinda tace Fahad ya tashi zaune yana mata kallon mamaki yace "me kk cewa ne Aisha? kina farin ciki da abinda yafaru ko? "

Aisha ta zumburo baki tace "to da so kake nace Allah yasa su medo maka ita? Saboda ita kamanta duk wata soyayyata idonka ya rufe akanta se kuma nakijin dadin tafiyarta, wlh naji dadi Allah yasa susa dole ka saketa ,hakanan batasan ya zaman mu yake ba tayi duk yadda tayi taja hankalinka har ka aurota ni ba abinda zance sede nace Allah yaraka taki gona "

Ranshi ya baci sosai da dane da seya mazge bakin amma ya dau alwashin barin dukan matanshi ya ciza lips yace "toko Allah baze amshi adduar ki ba saboda bame kyau bace, faseelat tananan dawowa gareni nida ita mutu karaba, don we love each other insha Allah we will die together"

Aisha dake jin haushin maganar shi kamar me ta turo baki gaba ,

Yaja tsoki yace "stupid bansan time din da zaki dena kishin hauka akan faseelat ba, ita kullum tana girmamaki tana sonki ke kuma ba wacce kika tsana kamarta"

ya tashi tsaye ze fita Aisha tace "bazaka jira ni mutafi tare ba? "

Beko waigo ba yace "batare mukazo ba kinsan hanyar gidan inkinso zuwa "
Yajuya ya bar gidan,

Aisha taja tsoki tace "so yake nayi addua sumedota kome?wlh yaya ya raina ni da yawa wai yagama cemin yanason ta har kuma yayi tunanin zanyi wata kyakkyawar addua can"

Mommy da tundazu tana kan dining tana jinsu tafito da cup ahannu tana kyalkyata dariya,

Tace "ke kuma dan ubanki waya ce kice mishi haka keda yazo ki rarrasheshi "

Aisha tace "mommy ba abin dariya bane wannan yazaai yazo yana fadamin wai he love her inba raini ba"

Mommy tace "to seme dan yace yanason ta tuntuni ina fadamiki kidena fiddo mai kiyyyar ta a fili kirika nuna kinasonta"

Aisha ta mike kafarta akan kujera tace"bazan iyaba niba wacce natsana kamarta Allah nagani da nasota kafin nagane hainta ta take ita ,ni wlh har mamakin zuciya ta nayi duk yadda natsaneta ranar da ya nakada mata duka seda naji tausayinta "

Mommy ta zauna ta kurbi tea tana murmushi tace "kin shirya zaman gida ko? Tunda kinsan ba zuwa zeyi daukar ki ba "

Aisha tace "hmm zezo ai Wadda ake makalewar batanan kinanan zaki ganshi "

mommy tai dariyar manya tace "amma kinyi kuskure karki kara irin wannan "

Aisha tace "to"

Fahad gida yakoma yayi kwance zuciyar shi na kuna yarasa ina zesa kanshi ba arziki da yunwa ta cishi ya tashi ya hada tea yasha,

akai akai yakan leka unguwarsu faseelat amma gida kulle, har dare yagaji yakoma gida,

Aisha taci wanka tana jiran yazo daukarta har 9:30 shiru bezo ba ta tashi ta dauko gyale mommy ta kalleta tace "ina zaki? Bakince ze dawo ba kijira shi "

Aisha ta yafa gyale akafada tace "mommy baze zo ba tunda har aka kai wannan time din bezo ba tafiya zanyi maybe yanacan ko abinci beci ba "

mommy tace "aiko baki isa ba ki samu wuri ki zauna, har se randa yaga dama yazo da kanshi daukarki "

Aisha ta turo baki gaba tace "Dan Allah mommy kibarni in tafi wlh hankalina duk baa kwance yake ba, yaya yana bukata ta yanzu "

mommy tace "yanzu kikasan haka ai, kicire gyalen nan "

Aisha ta turo baki ta tafita daga dakin mommy nata kiranta taki amsawa, daga karshe mommy tace "zakizo kisameni ne "

Aisha ta fita tasamu napep ta haye yakaita bakin gidansu, ta kwanwasa baba tsoho ya bude ta shiga ciki,

Ta kitchen tabiyo ta shigo gidan, fahad na kwance akan gadon faseelat rungume da kayanta ta shigo dakin,

Dukda yaji kamshinta amma be nuna ba, tana sanye da riga da wando na Sari ta haye gadon idanunshi a lumshe ta riko hannunshi tana cewa "yaya kaci abinci kau? "

yayi banza ya kyaleta tace "yaya kayi hakuri da abunda yafaru plsss katashi kaci abinci kar ciwo yakama munkai"

Fahad ya bude ido yana kallonta ,ta langabe kai tace "plsss katashi kaci abinci? "

ya yamutsa fuska yace "Aisha plss leave me alone ba ruwanki da naci abinci ko banci ba just go to ur room "

kamar zatai kuka tace "yaya da ruwana mana yanzu in wani abu yasameka fa?bansan ganinka cikin wannan halin na damuwa kayi hakuri katashi kaci wani abu "

Yace "bazan ci ba ko dole ne, kitashi kibani wuri, damuwa kuma zan cigaba da zama acikinta har lokacin da farin cikin rayuwata zata dawo gareni "

Aisha ta tashi tafita daga dakin tana kuka, fahad yaja tsoki yace "u don't love me da kina sona da kinso faseelat"

Aisha tafada kan bed ta cigaba da rusar kuka, ita ba maganganun nashi ba suka fi kona mata rai aa yadda yabi ya rude harda sukin cin abinci saboda mace, ta sha kuka har tagaji, har 2 takasa yin bacci shima ba baccin yake ba idonshi biyu,

Kanta na ciwo Ta tashi ta shiga kitchen ta hado mishi tea me kauri ta dawo dakinshi, yana kwance yanata kallon silin tazo ta zauna akan gadon murya dishe tace "Dan Allah yaya katashi kasha ko da tea ne ba don ni ba "

yayi mata banza tai ta magiya hardasu kuka sannan ya tashi zaune ko kallon fuskarta be ba ya mika hannu ze amshi cup din, taki bashi ta kai cup din bakinshi seda yashanye shi tasss sanan ta dauke cup din,

Tai murmushi ta share hawayenta tace "nagode da ka daure kasha "ta ajiye cup din a bedside table ta tashi zata bar dakin ya riko hannunta yace "anan zamu kwana"

Ta dawo ta kwanta gefenshi ta rungumeshi ba dadewa bacci ya dauketa,shiko yakasa koda rumtsawa sema kukan faseelat da yayita masa yawo akunne kamar lokacin yake dukanta duk da AC dake dakin yayita zufa,

Da safe,

tun 7 ya isa kofar gidansu faseelat lokacin har abba yafita yana tsaye bakin kofa omer yafito cikin shirin shi ze tafi school, fahad ya mika mai hannu ya mishi sallama fuska murtuke omer ya mika mai hannu ya amsa gaisuwar, ya zare hannunshi tun kafin fahad yace komi omer yawuce ya shiga mota yayi tafiyarshi,

fahad yayi tsaye zuciyarshi na kara zafi,can sega abul yafito shima ze tafi school ko kallon fahad beba yawuce warshi, sega su ishak da Mubarak sunfito suma zasu tafi school kasancewar yau Monday abun yabashi mamaki suma basuko kalleshiba ishak ya garkame gida suka juya suka tafi abun su,

dana sani yakara cika zuciyar fahad yara kananu ma Sun dena ganin girmanshi ,ya dade tsaye sannan ya shiga mota ya nufi gida time to time seya share hawaye bakin ciki da suke fitowa ta gefen idonshi,
Chapter 87 · 0% Book details