← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 130

Sashe 69

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tashi zata haye sama jiki sanyaye ya riko hannunta batare da ta waiwayo ba ya kalleta yace "banason bacin ranki, kisani farin cikinki shine nawa banyi haka don ranki ya baci ba, banaso ne kowa yana ganinki I love you very much ina tsananin kishinki ne honey don Allah kidena sa wani abu a ranki "

Faseelat ta juyo ta kalleshi idanuwanshi jawur yace "kiyi hakuri mutafi mommy wants to see you, she's the one that ask me to take you there "

Yajawota jikinshi yasa handkerchief dinshi dake fidda sassanyar kamshinshi ya fara share mata hawaye yana kallon fuskarta yake cewa "kiyi hakuri ki zauna bayan kinji zansa ayo miki hijabs daga yau shikenan, amin hakuri kar zuciya ta tai ciwo kinji gimbiya? "

Ta daga ido ta harareshi ta danyi dariya yace "that's my sweet wife, mutafi to kije ki gano mommy ta matsu ta ganki "

yajata suka fara tafiya tana jikinshi faseelat tuni tafara tunani tana matukar mamakin yadda fahad keson mommy she don't think umma zata taba samun irinshi koda Sun dedeta ,

Fahad ya mintsili bayanta ta daga kai ta kalleshi yana dariya yace "I'm happy da kukan ki saboda ya temakamin wurin bata kwalliyar da kikai "

Faseelat tai dariya tace "bazan sake yi ba tunda bakaso "

Sunata murmushi a makale sukazo zasu shiga mota Aisha data hangosu haka tace "ji bassu wawaye kawai "

Yazo yabude wa Aisha gaba ya kalleta yace "Aisha come to the front seat "

Ta tashi tana ya mutsa fuska ta koma faseelat ta zauna baya amira ta tashi takoma bayan ya shiga yaja suka tafi malali quarters,

Suna shiga cikin gidan Aisha tai saman benen, faseelat ta zauna kan kujera ta dan Kalli yanayin gidan, ramlat dake zaune palo ta tashi tai room dinsu tana tabe baki ganin yadda fahad da faseelat suka zauna a kujera daya, amira ma bin bayan Aisha tayi tana kwalawa big mommy kira,

Acan ciki Aisha na shiga dakin mommy, mommy ta tashi zaune tace "aa har kunzo kenan "

Aisha tace "eh gashi can ya taho da matar so wai ta gaidaki "

Mommy tai dariya tace "ni nace yakawota ai, ai diyata ce yakamata nadamu daita,abinda nakeso yagane keda ita daya ne guna "

Aisha tai dariya tace "mommy bakida kirki wlh ni zaki hada da waccan banzar I hate her well the way I hate my death "

Mommy tace "ihmmm bari nafita ni harma kyauta zanmata don nakara samun shiga "ta tashi tsaye

Aisha ta fashe da dariya har da rike ciki tace "wlh ina mugun sonki mommy kin iya kissa da tuggu "

Mommy tace "abinda ake koyamiki kenan kin kasa fahimta daace kina nuna kina sonta ina tabbatar miki da sekinfi haka agunshi amma kinki"

Aisha ta tabe baki mommy tafita, sam Aisha bata iya acting,betrying ba in tanason abu to tana sonshi in taki abu kuma ko afili zata nuna,

Mommy tana taka step tana faraa gab zata sauko tace" maraba da diyata "

faseelat ta kara masgwadawa nesa da fahad ta sunkuyar da kai ,

Har mommy tazo ta zauna faseelat tace "mommy inawuni "

Mommy fuska sake tace "lpy lau diyata ya bakunta? "

Faseelat tai shiru mommy tai murmushi ta kalli fahad daketa kallon faseelat kamar ze medata ciki tace "fahad kabarsu nan zuwa dare seku tafi bayan kunyi dinner don nakara gaisawa da ita "

Yayi murmushi yace "tom mommy bari natafi akwai Wanda ke nema na "ya tashi ya fita,

Mommy tabi bayanshi da kallo ta yatsina fuska Batasan cewa faseelat na kallonta ta cikin gyale ba ,acikin ran faseelat tace "Allah sarki mijina ka dauku da soyayyar wadda bata sonka Allah ya medo hankalinka awurin daya dace, umma ce kemaka son gaskiya ba mommy ba datake acting "

Mommy ta kira jummala jummala tazo dasauri mommy tace "ki kawomata pepper chicken din da drinks"

Jummala ta tashi mommy tadan zauna tana latsar waya, bayan jummala ta kawomata ta tashi tahaye sama ta samu Aisha suka hada kawuna suna tattauna wa ,

Faseelat ta dau exotic ta tsiyaya tasha ta fiddo waya tana latsa,

Can zuwa sega ramlat tafito tazo ta zauna tana bankawa faseelat harara, so daya faseelat ta dago ta kalleta ta meda hankali gun wayarta,

Ramlat taja dogon tsoki ta tashi ta haye sama, faseelat ta dago tabi bayanta da kallo ta girgiza kai ta cigaba da abinda take,

faseelat nanan zaune anan tayi salloli, bayan ishai fahad Ya dawo lokacin kuma duk su mommy sundawo Palo suna kallo sunata dariyar daso da suke kallo acikin wani film tana cewa "ke ni namiji beisa yasani ciwon kai ba yo miye namijin?ban taba bawa namiji amana ba kinganni nan aure na 5 dukkansu dan ubansu ni na sake su da kaina basu suka sakeni ba yo MI akai akai namiji "

itakam faseelat abun haushi ya bata ,

yana kallon fuskar faseelat yazo Ya zauna faseelat ta sakar mai murmushi ya meda mata ,

Sukayi dinner sannan suka tashi zasu koma gida, mommy ta dauko turare me tsada dake a leda tabawa faseelat, faseelat ta amsa tai godiya suka tafi, sosai fahad yaji dadin kyautar da mommy taimata da kuma yadda ta tarbeta,

Suna shiga gida kowa Ya nufi dakinshi amira na like da faseelat ta mata wanka ta kwantar daita sannan ta shiga toilet tayi nata ta fito ta shafa humra dasu roll on ta saka sleeping dress dinta ta haye gado,

Tana charting fahad Ya shigo da katuwar leda a hannu ta tashi zaune tana gyara zaman rigarta,

Yazo Ya zauna gefen gadon idonshi akan breast dinta da rabinsu ke waje, yace "honey ga hijabs din ki bada wadancan plsss "

Tace "karkadamu nima nafi jindadin hijab din akan wadannan "

Ya tashi Ya haye gadon Ya dora hannu saman breast dinta dake waje yafara shafawa yana lumshe ido,

faseelat tai murmushi ta kalleshi yadda idanunshi duk suka kankance ta janye mai hannu ya kuma medawa,

Faseelat tace "katashi ka tafi plsss banason haka "

Ya ware ido akanta yace "me ke bakiso? dan Allah kibari nadan yi wasa da babies dina wlh bana gajiya dasu bayan hq naki dake zoy ba abinda nafiso se su plsss let me suck them before leaving" Ya tura hannu cikin rigar yafara matsasu

faseelat ta lumshe ido ta bude tana matukar jindadin yadda fahad ke juyata Ya kware wurin rikita mata tunani ta daure ta zare mishi hannu ta kalleshi jiki mace tace "ni taka ce hero komai nawa is urs kuma zakaiya samun su kowane lokaci dan kullum cikin shiri nake amma ba yanzu ba, saboda zaka shiga hakkin wata ni kuma banason karika kauce hanya don inason mugudu tare mu tsira tare kabari gobe ne fa"

Ya lumshe ido yace "bazaki gane ba kwana dayan inajinshi kamar shekara "

Tai dariya tace "se hakuri, gobe inason natafi gida kasan jibi su ummi zasu tafi saudi shine nakeso inje muyi bankwana"

Nan take fahad Ya bata fuska yace "se dare zan kaiki tunda bankwana ne zakije"

Faseelat ta saki baki tana kallonshi ta marairaice fuska tace "haba hero wurin ummi ne fa wlh I'm missing her "

Ya kara tamke fuska tuno yadda take shagwaba wa omer wai tayi missing nashi ya sauka daga gadon Ya zuba hannuwa a cikin aljihu yace "ko kuma kinyi missing yayanki ba "

Faseelat ta kalleshi cikin mamaki tace "yaya kuma to mi yakawo yaya acikin maganar nan "

Yace "karki rainamin wayo zakisa bansan kina waya dashi ba, ki zauna kita mashi shagwaba wai kinyi missing dinshi "

Faseelat tace "haba hero yaya fa uwarmu daya ubanmu daya be kamata kana kishi dashi ba, kuma aiba laifi bane dan nace nayi missing dinshi saboda he love me so much he's gentle and caring, mun shaku sosai shima nasan yana missing dina dan Allah kabari natafi da safe da marece sena dawo saboda mugaisa da yanuwana ina missing dinsu all "

Haushi maganarta tabashi yace "dan iyayenku daya shi ba namiji bane seki zauna kita shashanci gabanshi yayi ta kallonki yanajin dadi,nafada maki se dare zamu tafi "

Ya juya yabar mata dakin

Faseelat tabishi da kallo tace"bangane abinda mutuminnan ke nufi ba fa "

Da safe suna dining fuskar faseelat ahade shima tashi ahade ta gaidashi ya mata banza amira ta kalli fahad tace "hero anty nagaisheka "

Faseelat ta zaro ido tana gumtse dariya, fahad fuska ta mau yacewa amira "I don't heard Her well just eat ur food "

Aisha haushi Ya cikata ta kalli amira tace "kar nakara jin wannan sunan he's ur dad call him daddy kina jina? "ta zare mata ido

Amira ta bata fuska tace "mommy ni inajin dadin sunan da anty ke kiran shine"

Aisha tazo zata tashi fahad Ya riketa tana hararar faseelat ta koma ta zauna,

Faseelat ta tabe baki ta tashi tafara gyaran gidan dan tunda tazo gidan Aisha bata kara dora ko da mofa ba da sunan gyara sede faseelat tayi,

tana gamawa tai wanka amira tazo suka fara bita ,

Shiru har azahar ba faseelat ba labarinta ummi tace bari nakira de naji ko lpya, ta dauki waya takira ta,

Faseelat ta dauka tana magana Ahankali,

Ummi tace "wai amarya bazaki zo mana bankwana ba inata dubar hanyar ki tundazu "

Faseelat tace "ummi Ya hana wai se dare "

Ummi tace "to ai ba matsala duk daya ne Allah yakaimu daren kiyi hakuri kinji "

Faseelat tace "to ummi "

Ummi takashe kiran, ba jimawa kiran umma ya shigo dan yanzu suna magana faseelat so biyu tana kiranta,

Faseelat ta dauka tana faraa tace "umma ina wuni "

Umma tace "lpy lau diyata Ya kuke? "

Faseelat tace "lpy lau umma "

Umma tace "alhamdulillah, dama cewa nai bari nakira ki dan kina debemin kewar fahad, ga kannenki duk sunason su ganki "

Faseelat tace "Nagode umma nima inason nagansu "

Kanwar fahad ta ukku Mansura (lady😉) tai sauri ta karbe wayar daga hannun umma dama kanta a jikin umma yake itada 2 sisters nata sun zagaye umma don sosai sukeson danuwansu amma su dashi sede suga pic dinshi a media ,tace "anty muna sonki sosai yaushe zamu ganki?"
Chapter 69 · 0% Book details