← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 130

Sashe 86

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

fahad da tundazu yake kallon sabeer kamar ya kaimishi naushi, ya hadiye miyon bakin ciki yace "u r very stupid da kake tunanin ina hada Aisha da faseelat kowace da matsayinta in Kana bani shawara kabani in bazaka bayarba senai tafiya ta "

Sabeer ya janye hannunshi da yadora kan fuska yarage murya yace "gaskiya baka kyauta ba duk son da yarinyar nan ta nuna maka amma har kaiya mata haka "

fahad yace "I known, ya zanyi yanzu they took her bansan ina suka kaita ba nikuma inason ganinta inason sanin halin da take ciki "

Sabeer yace "dole kayi hakuri kaita zuwa har kasamu ganin mahaifinta kabashi hakuri sosai kila su hakura , don inajin tsoron kar su rabaku, saboda diyarsu tana da komai dahar wanda yafika zata iya aura "

Fahad ya dafe goshi yace "bazan iya rayuwa babu ita ba, she's my life, I'm regretting bazan iya bacci ba batare da nasan halinda take ciki ba ,ina son sanin halin da take ciki "se hawaye sharr sharrr

sabeer ya dafashi yace "kayi hakuri kabi komai asannu faseelat takace,ka kwantar da hankalinka kacigaba da zuwa gidannasu har kasamu ganin abban nasu sede sekayi hakuri bazan boyemaka ba duk mutuncin da suke ganinka dashi yanzu babushi "

fahad yayi shiru yana tunanin yadda ze tunkari abban nasu,

sabeer yace "amma dan Allah ka rika kiyayewa,karage kishinnan karika hadiye shi don gudun nadama "

Fahad ya share hawayenshi yace "thank you, nagode "ya tashi ya shiga motarshi yabar gidan,

Sabeer yabi bayanshi da kallo ya girgiza kai,

har bayan isha seda fahad yaje gidan har lokacin yana rufe, yajuya yanufi asibity yanaganin basanan yayi tunanin an sallame su ya nufi gida,

faseelat na nan tazuba ido jiran hero shiru babushi,hankalinta duk yatashi ,jinin na karewa ummi ta jona heater ta kamata suka shiga toilet, ta temaka mata ta tube se lokacin ummi taga tashin hankali jikinta duk bakin tabo ne ga kumburi da tayi, ummi takara hawa fiyeda baya, ta gasa ta tai mata wanka ta sauya mata kaya sannan takamata suka fito,

faseelat ta kwanta tana meda numfashi, ba dadewa abba yashigo da maltina da madara aka hadamata ,ummi ta tadata tabata don dole tasha sannan ummi ta kwantar daita ,

ummi ta kalli su abul da tundazu suna asibitin kamar masu azumi tace "yakamata ku tafi gida hakanan har tara tawuce"

Suka fita jikinsu a mace, ya omer ma ya masu seda safe yafita,
Ummi ta kalli baaba tace "baaba yakamata kitafi gida kihuta kema "

baaba tace "to Allah yakara lpy bari natafi "

ummi tace "a, a kijira alhaji ya kaiki "

abba yace "to inde ana bukatar wani abu ki kirani"

ummi tace "to insha Allah "

Abba yafita baaba tabi bayanshi yana cikin tafiya baba babba yakira ya dauka bayan sun gaisa,baba babba yace"ya me jikin?"

abba yace "dasauki zaace"

baba babba yace "Allah yabata lpy, da Allah ko mijinta yazo karka saurare shi ,ya saketa kawai "

abba yace "to Allah yasa haka shine mafi alheri"

Baba babba yace "amin"sukai sallama,

abba na ajiye baaba ya wuce gida,

fahad na zuwa gida besamu su Aisha ba yajuya ya nufi gidan mommy, yana zuwa ya zauna a kujera ya kwantar da kai jiki kanshi na mugun ciwo,

mommy tafito daga kitchen taganshi tabata rai tazo ta zauna, tace "yanzu fahad rayuwar da kazabar wa kanka kenan? matanka kamedasu kamar jakkai kaita bugunsu kamar dabbobi? "

Fahad hannunshi akanshi yace "mommy it's a mistake baason raina nayi ba "

mommy tace "idan de zakai hankali kayi idan kana dukan Aisha nayi shiru ita wagga iyayenta ba shiru zasu yi ba "

tatashi zata haye sama murya sanyaye yace "ina Aisha? "

mommy tace "tayi bacci katafi kawai gobe kazo ka dauketa, ita kuma amira anan zata zauna tunda kagama tsorata ta"
Ta juya ta hayewarta,

Fahad ya tashi yabar gidan, yakoma gida ruwa kadai ya iya sha ya shiga dakin faseelat yayi kwance kan bed dinta yanajin kewarta sosai, ya tashi ya bude wardrobe dinta ya dauko sleeping dress dinta ya rungume a kirji yana hawaye,

gidansu umma ma duk basu cikin walwala har 10 tayi umma taji bata iya bacci ta tashi ta nufi dakin lady, Lady na waya da Hussein dasuke matukar son juna yanzu, umma ta shigo lady takashe kiran ta meda hankalinta kan umma,

Murya sanyaye Umma tace"waikinsan gidansu faseelat ne? "

lady tace "eh nasani"

umma taji dadi tace "yawwa kitashi kisa hijab can zamuje yanzu bari naje na dauko mayafi na"

ta juya tabar dakin, Lady ta tashi ta dora after akan kayan baccinta tafito, umma tafadawa daddy suka tafi gidansu faseelat,

suna zuwa sukai parking suka fito suka tsaya bakin kofa sunata knocking, can zuwa abulkhair ya bude gidan unguwar dun dum dan babu nepa, sede hasken farin wata,yagade mata ne yayi tunanin kawayen ummi ne,

abul yace "inawuni "

Umma tace "lpy lau ya me jiki an sallamosu ne"

yace "dasauki suna asibity "

umma tace "wace asibity suke room nawa? "

Yace "turai, aminity ward room 9"

umma tace "to nagode sosai "ta kalli lady tace "mutafi asibitin "

suka juya suka tafi abul yameda gida ya rufe,

akan hanya suka sai kaza me dawafi da drinks suka tafi asibitin,

Bawani wahala suka gane dakin suka tura suka shiga da sallama bakinsu, ummi kadaice ta rage itama tana salla, da lady da umma hankalinsu bakaramin tashi yayi ba ganin halin da faseelat ke ciki,

idon faseelat akulle umma takarasa kan bed din dasauri tana kara ganin barnar da danta yayi,

jin kamshi na daban faseelat ta bude ido taga umma, tafara hawaye,

Umma tace "sannu faseelat Allah yabaki lpy"

Faseelat tariko hannun umma murya shake tace "umma! ya sakeni ko? "

umma tace"me kike cewa ne? Yazaai fahad ya iya sakinki yana sonki sosai baze iya rabuwa dake ba "

Tace "ban ganshi ba har yanzu bezo wurina ba, Dan Allah umma kikiramin shi inason ganinshi "

Umma tace "ki kwantar da hankalinki yananan zezo "tasa hannu tana share mata hawaye,

ummi da tundazu ta sallame tai shiru tana kallon gadon da faseelat ke kwance tanajin takaici kamar me,

lady ta matsa tace "sannu anty "

faseelat ta daga mata kai tana cigaba da hawaye,

ummi ta tashi tana linke carpet tace "sannunku da zuwa "

umma ta juya wurinta tace "ina wuni yame jiki Allah yabata lpy"

ummi tace "amin "

Itama lady ta gaida ummi, shiru dakin nawani lokaci sannan umma tace "Dan Allah ummi kuyi hakuri akan abinda fahad yayi baa cikin hayyacin shi yayi haka ba, shi kanshi yana cikin tashin hankali don koda yazomun da labarin kuka yakeyi ,nasan yanacan cikin tashin hankali, kuyi hakuri Dan Allah wlh ni kaina abun yabatamin rai sosai don faseelat kamar diyata na dauketa, yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba"

ummi tace "ihhhm bakomi"

umma tace "kuma wlh naji dadi sosai da kuka dauketa, sede ina rokon da kuyi hakuri kubarmishi ita karku rabasu, don ita haske ce arayuwar dana, tana duk wani kokari na gyara mishi rayuwarshi badan ita ba da yanzu bama tare dashi, ina rokon da kuyi hakuri akan abinda yafaru kubarmishi ita Dan Allah "tahade hannayenta biyu,

umma ta bawa ummi tausayi tace " da nasa araina dole ya saketa saboda wannan abunda yayi kuma ba yaune yafara dukanta ba, amma na hakura saboda ke kuma zanyi iya kokarina naganin takoma dakinta, sede bazan bashi ita hakanan ba se yagane kuskurenshi "

Umma tace "nagode sosai ummi kuma naji dadin hakan don ko dauketan da kukayi yau kadai ma ya razana shi na tabbata wannan zesa yagane kuskurenshi nagode da kika min wannan alfarmar "

ummi tace "bakomi "

su faseelat najin abinda suke fada sede ita abun be mata dadi ba ashe dauketa sukayi, yanzu se yaushe zata ganshi? jin datayi umma tace yana ta kuka yasa taji tausayin shi ta riga tasan fahad na sonta sosai wannan dukan da yamata Har cikinta yafita kokadan besa ta rage digon son da takema shi ba,

Faseelat tace "umma dan Allah kikiraminshi inason ganinshi "

umma tace "kiyi hakuri kinji ,kibarshi yakara gane kuranshi, hakan zesa kobaya cikin hankalinshi baze iya dukanki ba, kuma ze kara sanin darajarki "

faseelat tai shiru,

ganin har 11:30 yasa umma tacewa ummi zasu tafi ta fiddo kudi boundles na 1k ta aje musu,

Ta shafi fuskar faseelat tace "kiyi hakuri kinji yata gobe inanan zuwa me kkso nazo miki dashi? "

faseelat ta girgizakai,

umma tace "kifada min me kkson ci ni da kaina zan girka miki "

Faseelat ta yamutsa fuska ahankali tace "komai inaso "

umma tai murmushi tace "to ki kwantar da hankalinki kiyi bacci "

taiwa ummmi bankwana ummi nata godiya suka fita daga dakin,

ummi ta kalli faseelat tace "shasha ashe duk sunsan kin mutu sonshi,mutum ya nakada maki duka amma kinata nemanshi har uwarshi taji haushi amma ke ko ajikinki marar zuciya"

faseelat ta juyar da fuskarta ummi tace "Allah yakawomaki sauki"

khalil ko abinci kala kala aka kawomishi wanda sede ya tsakura yabarsu saboda bejin dadin komi hankalinshi kuma yakoma ga hjya yasan iyanzu tana cikin tashin hankali, musa yazo sukai ta fira sama sama se 9 sannan ya shiga gida,

suma su hjy sunanan har 10 ganin ba yau zaa sallamesu ba yasa mamar jamila tace wa su hjya sutafi gida, hjya tace ita zaabari akai akai tatafi taki dole suka hakura suka tafi sukabarta rungume da lil khalil ,

da khalil da fahad da hjya da jamila, duk bawanda ya rumtsa,

Baccin asuba ne ya dauke fahad sede bewani dade ba yafarka ,

karfe 7 aka sallami su hjy suka dawo gida,

Karfe takwas fahad ya fita daga gida wanka kadai yayi ya sauya kaya ya nufi gidan su faseelat sede ya makara don har sunbar gidan yana kulle kamar jiya, ya bata fuska yanajin kamar yayi kuka ya cize lips ya juya ya tafi gidan umma,

umma na kitchen don sotake karfe tara tabar gidan,

ya shiga yayi kwance kan kujera don gabadaya bejin dadin jikinshi,

umma tagama komi ta fito da niyyar hawa sama tai wanka ta ganshi kwance hannunshi saman kai,
Chapter 86 · 0% Book details