← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 130

Sashe 127

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya rumtse ido ya bude yace "kiyi hakuri kinji ko ki kulamin da babies ki kuma kula da kanki kiyimin addua insha Allah soon zandawo normal kinji ko sorry"

Tai ta kuka abunta har seda akazo tafiya dashi yasa akakawo yaranshi yabisu da kissss ,yana hawaye faseelat na kuka akatafi dashi zuwa airport,

Har suka daga faseelat na kuka da akazo yi mata alluran relief akaimata data bacci ta sheme kan bed taita baccin,

Labaran BBC hausa na dare harda su faseelat a headlines,

Aichatu tace"wasu yan fashi sun kaiwa Governor Katsina hari bayan da suka shiga gidan daddyn amira sukai gaba da 100millions dollars, ankashe daya daga cikin su kuma ana cigaba da binciken gano sauran mahaifin amira de tuni yabiya company kudin bayan governor yabashi rabin kudin "aka nuno tattaunawarsu fahad da Governor,

"To kuma zakuji abun alherin daya samu ahalin domin bayan fashin da akamusu mamar amira ta haifi yara biyar batare da cs ba kuma yaran duk suna cikin koshin lpy ,

Ga kadan daga cikin rahoton ,se aka nuno babies jere biyar sunata bacci abinsu ,da kuma faseelat dabata iya magana ba ,

Aichatu tana murmushi tace" me girma Governor yayiwa yaran kyauta tareda mahifiyarsu muna yi musu murna muna fatan Allah yarayasu yasa su biyo yayarsu amira ahalin yanzu ni aichatu nake cewa mukwana lpy daga London"

Mutane se santin yaran akeyi ba bata lokaci suma suka watsu a media ,abunda yajawo hankalin masu kudi da dama,da yake karuwa ce se Allah yaraya ake ana musu kyakkyawar addua wasu kuma nata jin dama nasu,

Cikin dare su fahad suka isa tun kafin suje ansan da zuwansu karfe 4 na asuba akashiga dashi theater room, Umma nata salla tana addua ,

Seda suka kwashe 3hrs sannan suka fito gari tangarr garr kuma aikin yayi successful anmishi musanyar wasu kasusuwa yanzu yana bukatar time ne ciwon ya warke aga yadda aikin yayi ,

Yadda umma taga sunata murna likitocin shiyasa tadanji dama amma addua kawai takeyi ,

Tunda dare sabeer yafara receiving calls daga friend na fahad wadanda sukai business da normal friend sunata Neman yadda zasu temaka yabada account number din fahad ,

Nan kuwa kudi suka fara antayawa cikin 0 account nashi,

Wasu kudaden kuma sunata shigowa ta hannun governor yana ajiye mishi da niyyar bashi in ya dawo,

Tunda fahad ya farko yasa aka kiramai faseelat video call tana saman bed tana feeding yara ,

Kamar me lpy yace"maman babies how r u"

Ta turo baki tace "not fine"

Yayi murmushi ya fiddo ido yace"meya sameku?"

Tace "kana tambaya ta ya muke bayan kasan duk bamu lpy cos baka lpy"

Yayi murmushi yace "dont mind nakusa warkewa soon zan dawo"

Faseelat tai murmushi tace "to ya kafan "

Ya haskata yace "gatanan dasauki "

Tai narai narai da ido tace "Allah yabaka lpy abbu nankusa zaka warke "

Yayi murmushi jin sabon suna yace"I pray so ummuna"

*Kar a camfani 🤣ko ace yar karya wlh ana haihuwar yan biyar akwai wata diyar katibi tananan online inaganin sunan awasu novels mun zauna daita awani group wlh haihuwar farko ta haifi biyar kuma haifuwa ba cs ba sede daga baya nata biyu sun mutu bansaniba yanzu ko saura nawa amma na faseelat zasu rayu har tsufa💃🏻*
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

9⃣3⃣

I don't know anason writeup da nakeyi nide kawai ina rubutawa ne nasan wasu zasu amfana bansan andamu dashi ba,yusrah tace lecture🤣

yusra ga lecture ta yau 👇🏼

*Allah subhanahu wa taala yace"kace ba abinda ze same mu face abinda Allah ya rubuta mana shine ubangijinmu (me bamu kariya)kuma ga Allah ku dogara muminai*

*daga baban abbas abdullahi dan Abbas,Allah yakara masu yarda yace,watarana ina bayan Manzon Allah (S.A.W)se yace min:-ya kai yaro zan sanarda kai wasu kalmomi ,ka kiyaye Allah zai kiyaye ka,ka kiyaye Allah zaka sameshi agabanka,idan zakai roko ka roki Allah, idan zaka nemi temako ka nema awurin Allah,kuma kasani da mutane zasu taru don su amfaneka da wani abu bazasu amfaneka da komi ba se abinda Allah ya rubuta maka,kuma da zasu taru don su cuce ka da wani abu ba zasu cuceka da komai ba se abinda Allah ya rubata akanka, an dauke alkalumma,kuma takardu sun bushe*
(Hadisin me kyaune ingantacce)

Another hadith
👇🏼

Shima tirmizi ya ruwaito

*ka kiyaye Allah zaka sameshi agabanka, ka tuna da Allah lokacin da kake cikin yalwa, ze tuna da kai lokacin tsanani,kuma kasani duk abinda ya kuskure maka dama baze sameka ba,kuma abinda ya sameka dama baze kuskure maka ba ,kuma kasani cewa nasara tana tareda hakuri,kuma farin ciki yana tareda bakinciki,kuma tsanani yana tare da sauki*

Suka cigaba da fira abunsu su Ummi da Umma naganin abu,

Bayan sunyi bankwana suka bi wayoyin da kiss,

itade Ummi tasaba gani, Umma tana ta kallonshi tace "son tana tare da umminta fa inni bakajin kunya ta surikar ka fa?"

Yayi murmushi yace"umma menayi ?gaisawa kawai mukayi fa"

Tace"gaskiya kam"

Yayi dariya yace"Umma inasonta sosai ne"

Ta harareshi tace"shine agabanmu bazaa boye ba"

Yayi murmushi yace"I'm sorry,ina boyewan ahaka Umma da zan fito da shi fili maybe bazaki kara zama akusa ba idan muna waya"

Umma tace "aise na rika tashi nabarmaku wurin kuma ai nasan time da kakusa kashe kanka saboda ita"

Yayi yar dariya yace "its love "

Umma tai dariya tace"to Allah yakara maku son junan, yanzu de Allah yatemaka mana ka warke da wuri tun kafin kafara haukan son ganin matarka,zan rika ma tofi kanasha da zuma kasan tana temakawa wurin saurin warke ciwo danma bazasu yarda ba da idan ciwon yafara warkewa se in rika shafama dandanan ze warke ya ciko "

Yace"bazasu yarda ba ko Umma ,amma lpy lau sena rikasha nagode sosai "

Tace"me zakaci ?tun jiya bakaci komi ba "

Yayi shiru sannan ya dago yace "anything"

Tace"kanada hakuri kakara akai kaji?"

Ya daga mata kai kurum yayi shiru,

tahada mai tea da pan cake tarika bashi abaki,

Faseelat tana ta shan kulawa wurin doctors da yanuwa da mutanen arziki wasu manya sunata tattaki ganin kyawawan yaran suna masu alheri,

Tuni akaba yanuwan baba tsoho gawarsa da na yan sandan da suka mutu akai musu sutura aka kaisu gidansu ,

Governor yaje musu taaziyya yabawa iyalansu temako,

Shiko gawar lion tana matuary ana kara bincike akai,

Me asibitin Saboda jindadin yadda aka haska asibitinshi yabawa yaran gida karami me kyau ,

Tunda abun yafaru rashin lpyar mommy yakaru kullum magani takesha amma batajin saukin ranta,

Kullum sesun yi waya da fahad kuma tana zuwa duba faseelat da yaranta,

Kwanan su ukku aka sallame su ,suka koma gida ,

Nan kuma akafara zaman barka faseelat natashan gyara gashi Ummi ta dage wurin yi mata hadin ruwan nono kuma ana gamawa yaran da milk,

Umma sukayi waya da daddy ya tura lantana gidansu dan tarika temaka musu,ranan kuma ya aika da kayan babies akwati 12 sena faseelat akwati ukku yazama sha biyar da katon rago na kauri da kudi 1million, ya kuma riga da ya siyi shanu manya guda biyar na suna,

Faseelat kam kallon kayan tai tayi mutane sunata Allah yaraya,

Wanshekare daddy yawuce can turkey din,

Haka aketa taro mazan gidansu suyita daukar yaran kowa yanason yaran ,ita kuma tana cigaba da samun kulawa ciki da waje kullum sukanyi waya da fahad so hudu so biyar,

Matan sabeer suna zuwa danma fatouma kullum intaje kwance take itako radiya batasani bama cikinta har yakai 3month amma batasan dashi ba shima besani ba,

Ran daren suna sabeer ya aiko da raguna biyar da akwatuna shidda dukkansu dai daya,

Faseelat abun yazo mata a bazata akwatuna cike dam da expensive kaya ta kira fahad tafada mishi yaji dadi ya kira sabeer yana fara masa godiya ya kashe wayar fahad yayi murmushi kawai,

Ran suna tun asuba akai radin suna a masallaci ya omer ya kwaso uwayen goro da biscuit kowa ya samu da yawa,

Tun gari be karasa washewa ba shanu suka iso kofar gida su biyar ringis😂 dan Allah ku temaka ma shalele da daya🤣

gari na wayewa akafara yankasu suda ragunan ,

Acan cikin gida ko mejego tasha gayu itada yaranta,matan kaya iri daya pink colors maza iri daya wanduna golden riga black and white,itako oga taci dankareren lace maroon color da golden color kwalliya jiki dinkin riga da sket ya hau sosai tun kan ataru ta dauki pics ta turamai ta kira shi suka gaisa yanata santin kwalliyarsu,bayan sungama wayar ya bude pics din yanata kallo yana hamdala ga Allah,

Yan Niger sun cika gida dangin Abba dasu anty salma dangin miji da dangin daddy da na late daddy dana Umma ,

Aka shigo da bankararrun shanu da raguna ,

Ummi tai kason su bayan ta nemi shawarar baaba uwar diya da ammah,akabawa su dangin late daddy sa dangin daddy sa,dangin mommy rago,dangin Umma sa,su Ummi sa sora daya na me jego,raguna hudu daya anbarwa yanuwan ta daya na dangin Abba akabarwa Ummi daya tayi rabowa makwabta dasauransu dayan aka tambayi faseelat tace akai gidan marayu suci suyiwa babies addua🤣
(Rabonnan fa da son kai su mommy duk yawansu daya😂)

Nan fa gida yafara harmutsewa da kamshi can 12 suka sauya wanka faseelat tai shigar atamfa orange color da white taji kudi itama da different sarka dafkekiya ta zinari,tanata murmusawa abinta,

Kafin laasar sunyi shiga ukku ana laasar tabuga sabon wanka katuwar shadda dark purple taji uban aiki da white sarka tanata walainiya ba jimawa sega me pics akafara masu hotunan tarihi,

To andeyi taro an watse lpy bawani kida bawani tashin hankali,

Bayan 3 days sabeer yatafi Turkey dubo amininshi shida radiya ,

Sunje sun samu ana wanke masa kafar suka jira likitocin na fitowa ya shiga idanun fahad jawur saboda ciwo hakan behana yana ganin sabeer ba ya fara murmushi

yace "wannan surprise din fa?"

Sabeer yayi dogon murmushi yace "nasone kaganni a sama nasan zakafi murna"

Fahad yace"I'm very happy ka zauna "

Sabeer dake bakin gadon yace "firstly de ya jikin naka?"
Yana kallon kafar da hannun,
Chapter 127 · 0% Book details